← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 61

Sashe 30

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zata furta rashin yarda alhalin tana kwance a inda na barta ita bataje nema min abinda zanci ba an ban kuma tace wai tana zargin abincin bayan a gaban idona aka sayoshi ina kallo ko karban ledan take away din batayi ba. Haka gidan ya koma family house don saida suka share kusan kwana uku a tare damu kafin su koma part din da aka gyara masu din da zama suka barmu da aikin gyaran waje. Saida hakan ya dan sani zazzabi kwana biyu don komai dagani sai mum keyi daga su har iyayyensu suna zaune suna kallo ko hira kafa mike abinsu. Munyi barka komawansu wajensu din don yanzu ko hayaniya da koke koke yai muna sauki ko haka kawai zakiga danbe ya kicime a tsakaninsu zakice su din diyan yarene ba hausawa ba wallahi. Don dabi,unsu sam baiyi kama dana dan bahaushe ba gasu a tsatsaye koga iyyayansu wanan yasa na kara nisa dasu din don ko hjy mum da taga zasu shige min yanzune zata kirani ta sakani wani aikin da zai dauke min hankali. Don yaro ya zagi uwarshi ko kuma yace yayi fushi yana kaiwa uwa duka itako tana dariya adole ga yaro su iyayyen basu dauki hakan komai a wajensu ba. Gasu dai tsab a ido amma kan gaskiya halin ba kyau ko kadan suna da saurin fita ran mutane don wanan halin nasu naba kwabo a garesu . Ranan da suka koma din wuni mukayu muna gyaran part din mu wani abin kn saidai hjy mum din tayi hakkuri dashi don sun halaka mata kaya ko yaro ya dauki abu zai barnata uwa bata iya tsawata mashi sai idan yayi barnan kaji ana fadin kai dan nema kawai zan dukeka/ki fa. Da yake weekend ne mun gama na dan kwanta don in huta sai barci gashi kuma nayi wanka a lokacin sai kawai kasala ya sauka min shine na buge da barci nayi sa,a kuma hjy mum bata tayar dani ba a lokacin kodan tasan na debi gajiyane ta barni oho ? Karfe biyar na tashi a gagauce ina duban lokaci a dan zabure na mike ganin lokacin danayi na nufi bandaki na dauro alwala sallah na tayar ranan ba zancen zuwa islamiya awajena. Falo na fito na leka mum bata ciki hakan yasa na nufi kitchen nan ban ganta ba sai na tuno ranan itace zatayi girkin daddy watakila tana part dinshi kuma tana gyara ga girki dai ta dora amma bata nan cikin part din namu. Tsayawa nayi saidana tuka tuwon tare da hada miya lokacin tashigo a gajiye tana fadin yar albarka kingani na gama wanan na dan shiga wai in rage aiki bakiga uban aikin dana sama ba kuma a can din. Taja tsuki tana bude kulan dana kwashe abinci zuwa lokacin ledan yayi sutum sutum ciki ya dauki zafi ga tuwon na kwasheshi yan madaidaita daidai cin mutum daya. Mama ke kan kin huta mijinki baya shan wahalan abinci da gyaran gida komai da akeson ya mace ta iya kingama iyasa Allah ya baki miji dan albarka irin ki sai na turo mata baki hakan nakanyi a duk lokacin da tayi min zance irin hakan. Niga nawa watauna na tsani aure ayanzu tun akan abinda ya samu anty Nafisa yadda naga suna soyayya da mijinta amma a karshe suka kuma rabu rabuwa mai muni a tsakaninsu. Hakan yasa a yanzu nake jin na tsani zancen aure ban ma taba kawowa kaina wani zancen aure ba can balle har naji ina son yinsa din a kaina. Mun karasa kafin magariba don haka a nan baya na dauro alwala nashige ciki ban kuma sake fitowa ba don nasan ranan kwana ni kadai zanyi a part din tunda Mum kila part din daddy zata kwana. Kwance nake falon ina kallo sai wayana dake gefe ya dauki kara na dan dago ina dubawa Anty Nafisace don wani lokaci takan kirani hakan tace inzo in karbi wani abu a part dinsu. Nasan kuma ranan bamu hadu ba ko donshi zata iya kirana a lokacib tayi min korafin hakan tace na manta da ita ko naki zuwa inga lafiyanta. Na mika hannu nayi receiving ina fadin Ayya anty Nafisa wallahi yanzun nake zancen ki a raina yau aik,,,,, muryanta naji cikin wani yanayi hadi sauke numfashi guda guda tana fadin da kyar. Sister kina inane kizo yanzu don Allah ki sameni a dakina sai naji ta kashe mikewa nayi tsaye da sauri na dauki wayan na nufi hanyan kofa sai kuma na tuna babu kowa a part din mu a lokacin. Hakan yasa na tsaya na jawo kofan mum dake bude nasaka key na jawo kofan na nufi hanyan part dinsu sauri nake jikina na rawa ina dan hada hanya don sauri. Ina tafe inawa kaina tambayoyi barkatai na meya sameta naji muryanta a hakane ina mutanen part din nasu suka tafi kuma da wana tambayan har na isa part din nasu nayi sa,a babu kowa a falon hakan ya ban daman shigewa dakinta kai tsaye. Ina tura kofan na hangota kasa tayi gurfane ta dafa gado ta dukar da kanta kasa da gani tana a cikin wani hali mai muni a lokacin hakan yasa na karasa da sauri dakin ina fadin Anty meya faru meya sameki kuma ? Ta samu ta dago kai da kyat ta kalloni yanayinta gaba daya ya sauyawa sanin da nayi mata son lokaci guda naga hallittan ta ya canza min ga gani hakanlina ya kara tashi da gagawa na karasa gab da ita ina kiran sunanta. Dafata nayi ina maimaita tambaya anty meyake damun ki hakane sai naji ta dan sauke ajiyan zuciya a wahalce t dago kai wani uban zufa naga tayi tana kuma cije baki. Ta dan kai zaune tana fadin Sister kira min Mum idan tana nan don Allah ko kuma ki kiramin Dada dai don nasan yanzu mum tana wajen daddy. Da sauri na juya don in kira mum din har da Dada don ina ganin wanan ba zancen kiran mum bane ita kadai na murda kofan in bude naji ta saka wani salati me karfi a wahalce murya na rawa tana son tashi ta dafa gado ta kasa sai murde murde takeyi a wajen ita kadai. Hakan yasa da sauri na dawo gareta kuma ina faman yi mata sannu hannu ta miko min tana min alaman inzo in taimaka mata niko a lokacin nagama rudewa ko nace bari na kira Dada dai tazo. Yadda ta ciji kasa ta yunkura ta mike ta dafa gado haka harafin bakinta ya fito da karfi tana fadin sister ki kamani don Allah zan mutune kila da sauri na rike ta ina fadin baki mutuwa anty bari na kira su mum suzo. Wani nauyi naji tayi min a hannuna wanda hakan yasa nakai zaune bakin gadon ta dora kanta a kan cinyata gami dayi min rikon da kamar karti goma naji sun rikeni a lokacin. Saida na dan sake dan kara kafin naji tayi wani irin nishi da karfi saiga da ya fito daga jikinta yana callara ihu irin na jarirai wani irin tsoro ya kamani lokaci guda don ko ance nasake fitsari bani mussu. Ganin ashe haiwace yasa na dan dake ina fadin sannu anty ina kokarin cireta a jikina ta sake wani irin ajiyan zuciya tana amsa min tare da fadin yi sauri sister ki kira wani yazo ya yanke cibi don Allah. Na fito a gigice ina kwasan gudu zuwa wajen Dada banko kula da mum na wajen ba tazo tambayan ko nashigo wajensu don taje part dinta ta samu a rufe yake ta dauka nazo nan din. Ke lafiya ga uwarki tazo neman ki kina ina hakane mum ta tambaya ta tare zancen Dada din nace mum anty Nafisace ta haihu yanzu. Haihuwa a ina nace ina haki tana dakinta salati suka saka suka kwasa zuwa dakin nata dukan su suna rige rige Dada na fadin dazun fa da uwarta zata fita shine tace ita bata zuwa ina mata sheri. Kusan tare mukai part din dasu saidai a falo na tsaya don sai lokacin naji tsoro kuma ya kamani Dada ce ta fito muka zauna a falon nan muka barsu tare da mum din a cikin dakin. Dan tsayin wani lokaci saiga mum din ta fito da abinda aka haifa din nade a cikin wani zanin anty din don a lokacin ba zance ga kalan abinda ta haifa ba don ban tsaya duban kome ta haifo ba saboda firgicewa. Dada ta mikawa da sai fadin take ikon Allah na yarda haihuwa habone don baifi awa ba da muke zaune da yarinyar nan a waje har inawa uwata fadan kwasa su fita haka su barta ita kadai ga ciki tace min ba dadewa zasuyi ba ai a can din. ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/14, 11:11] Aishatu Aliyu Musa : DUBA MIN BAYA FOKON ,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Wayan da ya Addel ya kara sai mun ya zama abin hassada ga yan uwana a wanan gidan duk da ba wani dogon shiri muke a tsakanin mu ba wanan bai hanasu sakawa takona ido ba don basu san da wayan ba da farko sai daga bayan nan suka kula da wayan da nake riko din wanda ya Addel ya sayo min din saidai basu san a ina na sameta ba har yanzu. Don ince a dalilin wayan nan harkal ta da halimatu yayi rauni a yanzu a cewanta ita da uwarta wai asiri iyayyena ke min na farin jini a gidan nake da sa,an mutanen gidan wanda ba haka bane kuma. Rashin kiuyana da girmama mutane yake jawo min alheri ga kowa a gidan koda mutum bai niyar yimin hakan ba zai mun duba ga irin halina ya kyaleni wanda a lokacin
Chapter 30 · 0% Book details