Sashe 47
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da basira ko wanen ku ya hadashi da wanda yasan zai gyara rayuwansa amma ba kowa zai fahinci hakan ba sai nan gaba. Idan kun daure gaba dayan ku zakuji dadin auren nan naku jin meta fada yasa na dago kai na kalleta tace Yes iam telling you zakice na fada wata rana insha Allahu. Hannunta ta dauka ta dagwara a nawa tace ki jajirce sosai zeey ki zamo jaruma a gidanki zainab ki mayar da mijinki abin alfaharinki abin kuma so ga kowa daya gansa. Kuka sosai nake har ban iya gane mum na dakin ba saida naji tace kukan na meye haka don kawai kijawa kanki ciwo duk abinda Nafisa ta fada gaskiya ta fada maki. Don ba karya acijin zancenta nima abinda na hango Alh yayi ke nan kikaga ina faman baki hakkuri da kike dauka duk bamu son kine wanan shine gata da kaunan da zamu iya nuna maki ai mama. Itama mum dafani tayi acikin sanyin jiki tace mama kiyi hakkuri ki daina kukan nan don Allah ki yarda da hukuncin da Allah ya kaddara a gareki. Ki yawaita kiran Allah ya sasauta maki abinda kikeji a zuciyarki insha Allahu abin zaizo maki da sauki ta hanyar da baki tsamani ba da yardan ubangiji. Tana kaiwa nan ta juya ta fita zuciya ba dadi agareta ta barni da Anty Nafisa din dake fadin haba sis ki kwantar da hankalinki mana ki dauki shawaran da muke baki nasan kowaye hafiz idan kikabi sharan mu zakiyi maganinsa hafiz zai dawo a hannunkine wallahi. Haka kuma sai kin daure da mummy don rayuwan Hafiz gaba daya bisa tsarin mummy yake don hafiz ko wanka yayi saiya kira mummy wani lokaci yana tambayanta kayan da zai sauya saboda sagarta data koya mai wai so. Don haka ki dauri kibi shawaran nan namu insha Allahu zakice nace dake ni zan koma don in gyara wancan kayan nasu mairo dake part din mu don nasan mummy ba zata tabasu ba idan bani naje na kawar ba a yanzu don Allah ki natsu kamar yadda hjy mum ta fada maki. Daga haka kuma tafice daga dakin ta barni a wajen saida na dan dauki lokaci kafin in mike nashiga bandaki na fito don la,asar ya shigr ko ana batun magariba ba daman ayi nafila a lokacin yasa na wanko fuskana na fito abinci na sama mum ta kawo min har daki na zauna naci kadan don kada tace banci ba na kwashi kayan zuwa kitchen. A dakin kwananta ta jera akwatinan auren nawa da daddy ya gabatar masu a matsayin lefen mu wai ashe duk da fitinan mummy bayan Dad ya kirasu saida ta saka matar daddy enugu ta bude ko wani tagani ta kana tace a musaya a dauki wanda daddy yace shine nawa shi kuma ya fito yace bata isa ba kowa da sunansa yasaya mai ya kuma saka komai iri daya aciki don yasan kalan da kowan mu ke so ai. Nan kuma ta kwashi fushi ta hau bakinta daddy din yace idan son kai nayi kece dai naiwa son kai din don matar dankice na cikinki zata daura kayan don haka ake nayiwa son kai din ke nan . Wani kallo tayiwa daddy kafin tace matar danka dai amma ba dana ba in gaskiyane ita mama din abin kwaraice ka hadata da Nasir ko Addil mana amma ba jini naba. Tunda kasan ko a rarihi ba aure tsakanin zauren gidan mu da nasu ke nan ashe ba aure a tsakanina dake ko ? Tunda hakane tayi shiru ta juya ta bar wurin rai bace yace sakaran banza zan koya maki hankali a gidan nan tunda ke kulun yarinya kike zama baki girma kafin ki tauna zance. Dada da abin duniya ya dama a lokacin kallon hanyar da hjy malkan tabi tayi tana dadin wai ko anya kan marka daya kuwa kodai marka ta tabune ba,asani ba ? Lafiyanta kalau tsaban iskancine da rashin sanin ciwon kai data iya take nunawa wanda bai gama sanin halinta ba a yanzu wai ita marahankali. Bayan kamar kwana biyar ya Addil ya shigo garin sai washegarin asabar ya shigo gidan muna zaune falo don ranan ba zamuje karatu ba kowa na gida saboda dan tafiyan da mai course din yayi muka huta gida a ranan. Yana saye a cikin wani yadi fari daya kara masa kyau sai wata yar hulan maza dagani mai tsadane mai kalan dan ruwan toka akansa duk da akwai rama a jikinsa hakan bai hanashi yin kwarjini ba a idanuwan mutane. Part din Dada ya fara shiga dana daddy Enugu ya gaidasu suna tambayarshi matarshi Aisha duk da tare suka shigo kanon amma saiya saya yace tana lafiya kawai ba ambata tare suke ba don gudun korafi a wajensu. Ya gama dasu har part din mummy kafin yashigo nasu part din ya samemu zaune da mum din a falo muna kallo mum kuma na waya da mai kayan kamshi da tayi Oder a kawo mata wata yar maiduguri. Lah ya Addil ashe kazone na fada cikin yar fara,ata ina kokarin dagawa inda nake zaune yace amarya gaki duk kin rame mana ko duk rakin auren ne haka kika fada tun yanzu ? Fuska na dan bata tare da fadin haba dai ya Addil har dakai kuma kaine fa share hawayena kullun inawa ya Nasir gorin hakan don yaji haushi . Zance kuma a gaskiya karo na farko ke nan duk zamana gidan da wani kalman wasa ko zolaya ya taba shiga tsakanina da yaya din don baya magana balle inga fuskan tsayawa wani wasa dashi can yadda mukeyi da ya Nasi da sai mum ta koresa wani lokaci . Mun din ta gama wayan ta dago tana fadin ashe kun samu shigowa yace ehh aina fada maki zanzo kafin buki na ganku ya sauko saman kujeran ya tsuguna yana gaida ita a cikin ladabi ta karba masa ni dai hakan na ban sha,awa wallahi. Ruwa da abinsha na karaso masa dashi har na dire a gabansa yace nagode mum yarki ta rame da yawa wallahi ko tayi ciwone wai don raman nan yayi mata yawa gaskiya. Aiba ita daya ta rame ba har kai don haka ashe aure ramar da mutane yakeyi ke nan ba kiba ba kana zancen mama kai kaga yadda ka rame din kuwa ? Halan ko abinci bata baka balle wajen kwana kai ya kamata aiwa wanan tambayan a yanzu ba mama da har yanzu tana dakin uwarta bako . Meke sakaka wanan rama haka har ya ja maka dushewa hasken ka ya dushe sosai a yanzu mai sunan malam ta kirasa da sunan da akasarin yan family suke kirashi dashi din don sunan kakansa malam Ali da yaci . Dan shafo kai yayi zuwa fuska yana murmushi yace mum don daidai kin dade baki gani bane kike ganin na rame amma ai jikina nan da haskena kuwa. Allah yaya ka rame ka fada sosai kayi baki ka rage tsayina ya dago ya harareni nayi saurin nokewa a bayan mum yace kika karajin ana min magana kin sani ai zan fasa shegen bakin nan naki a wajan nan. Ba zaka dukar min diya ba son gaskiya ta fada ai duk mai kaunan kako zai fadama sauyawan nan da kayi Addil da alama dai auren nan abinda mukewa gudune ke faruwa da kai dai ke nan ? Dan murmushi yayi yana fadin mun kin fa san yanayin aikina yanzu ba kamar da bane mum aiki yai min yawa a yanzu ga kuma nauyin iyali akaina. Tareshi mum tayi da fadin au kace min kun samu karuwa ashe kunfi ku biyu yanzu gidan to Allah ya raba lafiya ya bamu mai albarka da sauri yace ba abinda nake nufi ke nan ba mum muna dai fatan Allah ya kawo ya fada yana dukarda kai kasa cikin ladabi . Shiru kowansu yayi kafin shi ya kawar da shirun da cewa Dad ya buga min waya yace saura sati uku yanzu daurin auren yaran nan da sauri na kallo mum din ina fatan tace yafi hakan ai sai naji tace insha Allahu ga yadda yasa lokacin ba saidai uwar yaran ai ta nemi da ya kara mata lokaci ta kara shiri ban sani ba ko zai yarda da hakan data bukata don Alh bahagon mutum ne idan ya tashi abinsa. Ko naka ba haka bane daga zuwa nema ya saka rana mikewa nayi tsam na barsu a wajen hankali tashe ya Addel din yace nasan ba zai canza wanan ranan daya saka ba ai. Don yanzu ma kiran da yai min akan hafiz ne wai yace baya son wanan gidan daya gina masu saidai a canza mashi wani mum fara zancen dashi a waya shine yace idan na samu lokaci inzo. Yanzu canza masa wani zaiyi ke nan yace to bamu kaiga magana ba shima bansan dalilinsa nakin wanan gidan ba ai gashi baya da nisa sosai da gida kuma ginan gidajen yayi kyaiu sosai wallahi. Sagartane irin nasa kawai da neman magana yana son ya bullo da duk wani hanya da rayuka zasu kaiga baci in bashi ba ina ba zama nan din zasuyi ba na dindindin meye nasa na tsaya zaben gida inba neman na yiba. Zanje na gani yanzu ai kafin daddy din ya fita muyi magana akai Allaj ya kyauta ta fada tana kawar da kai gefe cike da takaicin abubuwan dake faruwa a gidan cikin dan lokacin. Shin tunda ba Allah yace sai anyi hakan ba abari mana amma kan yaro daya har ciwo na batun kayar da Alh in anyi magana kuma suce saboda taga ba danta bane. Koda ya Addil din yaje wajen daddy ya sameshi yana shirin fita baiyi magana saida yasa aka kira anty Nafisa razo yake kara gaya masu matsalan da dan nasa ya kawo kuma yanzu. Anty Nafisa ce ta fara magana tana fadin wai meke damuwan hafiz ne haka wanan ai iskancine kawai yakewa mutane wanine zai zauna masa da matar ? No ba hakana bane ke Nafisa kinsanfa halin hafiz sarai idan da hali a canza masa kawai a wuce wurin hakan zaifi sauki kafin yakai karshe tace. Amma kana bani mamaki wallahi ta nasa za,abi koshi ya haifi mutane da zaice sai yadda yakeso