Sashe 24
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/3, 07:47] Aishatu Aliyu Musa : DUBA MIN BAYA FOKON,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Tabbas ba a nunawa shege hanyar neman uba saidai ki sani hjy malka duk wanan dukiyan dake gareni yanzu zan kara fada a gaban iyalina kuji sanadiyar kakan yarinyar nan na sameshi. Ni Alh musa ba butulu bane ko kaza mai ci ta goge bakinta nafi gaban wanan yau har a samu daya daga cikin iyalina yace zai gorantawa iyalan Garba wani abu a cikin gidan nan wallahi karyane daddy ke fadin hakan a gaban iyalinsa. Da akai komai a gaban idanunsa ashe yace hjy kece shedana a madadin yan uwana dana kafaku sheda a ranan kada wani yace zai matsawa yaran nan dana dauko a gidan nan da suna riko in samu lada. Sai gashi yau hjy malka tayi kokarin take wanan dokan da sunan gida na diyansuns don haka babu dan shan miyan da zaizo gidan nan ya takurawa rayuwansu da sunan zaman riko. Yau yar garbace ta zamo yar riko a cikin gidana ko kuma yar saudatu kanwata ce diyar dan uwana isa ta zamo yar riko a gidan nan ya juyo yana tambayan hjy malka din da tun farkon zancen take mamaki yadda yasan wanan zance. Da ace yaran sun dawo gidane da sai tace a bakin mu yaji hakan don mu kadaine a wajen saiko yayanta da driver to ko driver ne ya fadawa Alh din ? Ta tambayi kanta wanan zancen cikin mamaki kafin tace amma ai Alh kamata yayi ka tambya har in ma wanine ya tsegunta maka zancen kaji meya faru har na furta hakan garesu. A,ahaa gareta dai don ita dayan ta kasance mai baki biyu wajen ki take donke ke rikonta yanzu gidan nan ita dayan kuma da kikabi da zagine har da gori ban fahintaba ni. Shiru tayi kafin ta dago cikin karfin hali tana fadin aida munafunkin daya fada ma anyi sai ya fada maka ita metace dani har na fada mata hakan. Kin dai fada ke nan marka aiko yaran nan basuci hakan gareku ba gidan nan nina dauka koba Alh kuke aure ba suna da daman zuwa wajen ko wacenku su zauna a karkshinta. Balle kuma nan din daya zamo gidan wan mahaifansu kuma yan uwanku har wanan kalamin ya fito a fatan bakinki yanzu sai yarkice zata kwaba maki karshe. Lalai tabbas munafukin nan yakai tunda komai ya kwashe ya fadawa Alh duk yadda akayi Sani driver keda wanan munafuncin ta fada a ranta. Banyi magana bane don naga takai ga samun yadda takeso zubar mutuncinta don ko yarinyar ta bata ansa a bakinta ai yadda zata iya kwatan kanta gareta . Kallon mijin nasu tayi yace agabana komai ya faru malka da wani zai fada min ba zan yarda ba zance yai maki kazadin da kike fada kullun an maki agidan nan ne amma sai gashi idon ki ya rufe har kuka tafi baku san ma ina tsaye a wajen ba nida bakona a lokacin. Kai ta dukar kasa lalai in ba ta mata ba motarshi tana wajen a lokacin ashe yana ciki ke nan ake nufi lokacin lalai ta tafka babban kuskure nayin hakan a ranan data bari tabi shawaran yarta Asiya zaifi mata sauki amma ina zafin zuciya ya hanata yin hakan alokacin. Muryan dadine ke fadin don haka kan taka min doka zan dauki kwakwaran matakin da nace zan dauka akan ko waye yace zai takurawa yaran nan tun farko. Kafin daddy yakai karshe har hjy mommy tace dashi don Allah Alh kayi hakkuri kusukure aka samu ba za,a karan hakan ba insha Allahu bacin raine don Sadiya sata take mum sosai yasa naso in horata ga hakan. Duk suka kallota tace kwarai kuma saida na tabbatar da hakan gareta nagane itace take daukar min kudi da wasu abubuwa yasa na dauki mataki. Itama yar uwan shine tambayan da nake mata taso ta kawo min rashin kunyane harka jimu da ita idan ba haka ba aini ba ruwana da sha,aninsu. Kuma ita din ta saka kanta cikin harkan kishin mu bata kallon kowa da kima a gidan nan lokacin hjy Kuburah tayi magana tace bako Mama ba don ba mecewa tayi mai rashin kunya don ba halinta bane. Idan batayi yau tayi min ko karya nayi mata kuma ta fada a dan hasale don hjy mum tayi magana a lokacin abinda bata kauna ke nan taji don tana ganin batayi matsayin da zata saka baki a rigimanta ita da mijinsu ba ai. Saida Dada ta saka baki ganin yadda hjy malka ta kwanta yasa daddy ya hakura bayan ya kara jadada masu akan kafin suka watse har lokacin hjy malka bata yarda cewa daddy ne yaga abinda ya faru da idanunsa ba. Koda muka dawo ina cika saiga hjy mum tafito min da zancen nima nayi mamakin jin zancen a bakinta takuma fada min matakin da daddy ya dauka akai wanan yasa naji dan sasauci a zuciyana. Sai gashi kuma a yammacin anty Nafisa ta dawo gida ba dadi ita da miji har abu yakai ga sakin daba gyara a tsakaninsu ga kuma karamin ciki a jikinta duk uban kudin da aka kashe da wanan bukin da baifi wata uku ko hudu ba a yanzu ya tashi ga banza tunda auren ba gyara kuma . Mun dawo daga islamiya muka tsinci wanan bakin labarin a bakin Dada daketa yankan fada a dakinta don nashiga ingaida ita tunda tun safe ban shiga ba mun gaisa. Nan take fada muna abinda ya faru cewa ashe shi din dan duniyane wai baison haihuwa matarsa ma ta gida haihuwa biyu yasa ta dakata da haihuwan. Saboda baison mace mai haihuwa yasa ya nemi anty Nafisa din don yaga kanta a waye yake zatayi na,am da bukatashi sai gashi takiyin planning din daya bata tayi ciki ya baiya daga kaita gidanshi. Wanan ya kawo masu fitina ba dadi yace ba zai zauna da ita ba tunda tun farko ya fada mata shirinsa taki daukan mataki don haka ko a zubar da cikin tayi planning ko kuma su rabu tace ba zata zubar da ciki ba tunda ta samu. Sunsha rigima kuma uwarta ta sani amma bata fadawa kowa ba saidai tana tausan yar nata dako yaushe cikin bugo mata waya take tana kuka idan sunyi rikici dashi din ta bata hakkuri wai kada aji ai masu dariya saboda bakin kishi. A karshe dai sai takarda ya mika mata ta bar mai gidansa hakan ko akayi da tace saita haihu zata bar gidan amma ya dauko mata yan sanda da mota yasa aka kwaso mata kayanta kaf a lokacinne gida aka sanda zancen. Anan kuma bayan dan sandan ya korawa daddy komai yace baison har cikin ya yafe gidansu su rike idan ta haihu nan daddy yace a fada masa bai isa ba ko dan gidan uban waye shi a garin. Da kyar dai dan sanda dayake na Allahne shi yabawa daddy shawara akan a kyaleshi idan an kwana biyu ko bayan ta haihu a makashi kotu ko kuma da daddy zasu iya hakkuri wata rana dole zai waiwayi abinda aka haifa masa shida kansa gidan. Dada tace wanan ya dan kwatar da hasumin da daddy din keyi don bata san abinda ya tuno ba da kalamin dan sanda har ya hakkura lokaci guda. Dada din kuma ta daukemu zuwa dakin Nafisa din wace muka samu kwance duk ta rame ta lalace ba zakice Nafisa bace da akai bukinta lokacin tana baka sha,awa. Muna shiga dakin muna sallama Dada na fadin Allah sarki kibar kukan nan hakana yar nan tunda ya riga daya cuceki dan banza wanan yasa ake kyautata zurfin bincike akan mutum kafin ayi aure. Haba Dada ki barta taji da abinda ya sameta koda anyi bincike din tunda Allah ya kaddara hakan saiya faru tsakaninsu ba makawa sai hakan ya faru din. Tayi hakkuri tabarwa Allah komai ta dinga istigifar ga ubangiji shi zai duba mata lamarin insha Allahu na fada daga inda nake tsaye bayan Dada din mun kura mata idanu muna kallonta cikin tausayi. Allah ya saka maki da mafificin alherinsa anty ya kuma saukeki lafiya ya baki mai albarka amin na fada ina shirin barin dakin yayinda halimatu itama ta amsa da amin daga bayana har mun juya naji tace Sister nasan dani takeyi don haka take kirana tun zuwan mu gidan har lokacin bukinta din dashi take kirana a gaban kowa. Najuyo tace idan kinje ki dawo don Allah na amsa da to nafice nikan ina zuwa part din mu na manta da zancen ta don na samu mum tana fama da ciwon kai ko girki bata iyayi ba a ranan gashi kuma ya Addel yana gari yazo . Hakan yasa na kwabe hijjab dina zuwa kitchen na dora ruwan zafi naji muryanshi a bayana yasa na juyo ina gaidashi yace ruwan zafi nake son in kaiwa Mum tasha magani tace kina nan. Ruwan dana saka din na debo mashi a cup na hada dana surkawa na gora na mika mai ya karba har ya juya sai kuma ya tsaya yana fadin idan abinci zaki girka ki bari dare yayi zan fita inyo maku take away na amsa da to. Bayan fitarshi na kashe wutan gas din na gyaro kitchen din na fito na koma wajen mum a falo na sameta zaune da alaman har tasha maganin a lokacin. Kara gaida ita nayi kafin na kai zaune a gefenta zan fada mata abinda yace saita rigani ta dan dago tana fadin yayanku yace kibar girkin dare yayi ko ? Nace ehh shine nazo in fada maki tace nima nayi tunanen hakan yaushe zaki gama dare bai maki ba yanzu shida da rabi har ya gwauta ai. Nabi ta