← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 61

Sashe 17

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kai gefe don na zuciya dashi iya makura don abinda yaiwa tsohuwar bana kai sake bane kokarin kai min mari yayi yaji an rike hannun nasa ta baya ya juyo a fusace yana fadin. Ka sakar min hannu nayi maganin wanan karamar yar iskan haba dai meyasa kake hakane wai da wanan karamar yarinyar zaka tsaya kuma fada haka. Sai yayiwa dan uwan wani irin kallo kafin ya kuta ya fice yabar dakin Dada tace mahaukaci sai turu kuce min ashe kara haukacewa yayi acan turai din yanzu. Suka kwashe da dariya suna zolayan Dada din tunda ya bar dakin ban kara cewa uffan ba suma basu dadeba suka bar dakin kamar jira nake su fita na saka kuka sosai lokaci guda. Hankalin Dada ya tashi tana fadin dama nasan za a aika hakan wanan yaron kan baisan arziki ba a rayuwansa daga maganan fatan baki gashi yanzu ya saka yar mutane kuka. Duk lalashin da Dada tayi min hakan baisa nayi shiru ba saida ta fita can sai gasu tare da hjy mum sunshigo tana fadin kingata nan badon Allah ya gyara ba da dukanta zaiyine kome oho. Ki taso muje part dina ta fada cikin bani umurni banki ba nabi bayanya zuwa part din ta dakin da muka sauka nayi niyar shiga amma naji tace nazo dakinta sai nabi bayanta muka shiga tare da ita. Zama mukayi bakin gadon dagani har ta dan kura min ido na wani lokaci kafin ta soma magana ki bar kukan nan hakana mai sunan hjy nasan ba karamin abu bane yasakaki wanan kukan haka amma kinyi hakkuri don Allah. Nasan an zaluncekine yasa kike wanan kukan amma shima ya kuru da bai kai ga taba jikin ba yau da ranshi yafi naki baci a gidan nan kuwa ta fada a cikin sanyin murya. Ni gida nake son komawa mummy na fada ina sake barkewa da sabon kuka lokaci guda ta girgiza kai tace akan Hafiz zakice zaki koma gida yau. Saida buki yazo gab zakice ke gida zaki tome akayi ke nan idan kin koma gida yanzu sai kace wace ba gidan ubanta tazo ba. Nasan Hafiz baya da kunya ko sagarcine ke damunsa ohh komu mata yaushe kika tsaya shiga tsabgan mu balleshi namiji don Allah kiyi hakkuri ki daina wanan kukan haka. Koda yake nasan bayin kansa bane iyayyensane dai basu yarda da hakan don sonsa ya rufe masu idanu basu ganin laifinsa su. Da kyat ta samu na tsagaita kukana bankoma part din da Dada din take ba don nasan idan naje can zamu iya haduwa dashi wurin ni kuma ba zanso wata halaka kota gaisuwa ya kara hadani dashi ba kuma. Nan nake zama wurin gwaggona inkin debe zuwa gaisuwan safe da nakeyiwa Dada din bayanshi yanzun na daina zuwa mata hira ga baki daya. Wanda yasa Dadan ta fara korafin hakan har yakai tana biyoni part din hjy mum mu dan zauna idan tazo zakiji tace na biyo wanan matsorociyance data zama ta gudu yanzu gidan nan tana tsoron miskilin yayanta har ranan da har aka wuni ban samu lekasu ba yakai ta biyoni da yamma har part din hjy mum din. Nan baba na kano ya dawo kasuwa akace tana wajen hjy kubura ya biyota nan din yana fadin Dada naje daki akace min ai kina nan Dada tace gani nan na biyo matsoraciyan nan Abulle ne kasan miskilin nan ya tsorata ta da shiga wajen mu tunda ya daga hannu zai mareta ranan ta daina zuwa inda nake. Baba yana kaiwa zaune yakr fadin mari kuma Dada wa ke nan wai Hafiz wazai mara din wai tace gata nan don kawai tace mashi ya daina tsoratani shine nan ya dago hannu da niyar zai mareta saida mai sunan malam ya tareshi ya fita yana zuciyan banza don an hana ya mareta. Aiko daya gane kurensa daya dora hannu akan jikin yarinyar nan don zan gwada mai daya suke da ita a gidan nan ita din ba bare bace a cikin gidan nan don itama mai galihuce kamar kowa a cikinsu. Daga inda hjy mum ke zaune suna hira da Dada ta jefo baki tana fadin gara dai a tsawata mashi din don kasan halin Hafiz idan ya tashi zuciyarshi na banza bajin zancen kowa yake a gidan ba shi. Idan ya isa ya taba ta ai gani hjy mum bata dadara ba sai cewa da tayi dashi gara dai din a tsawata mashi kansu don kada yazo ya takurawa yar mutane ko yanzu din ma a takure take wajen nan ai tunda ta daina fita ko ina sai nan part din kagako ba,ayi ba ai. Bari zan gashi in masa kashedi akansu tace dadai yafi gaskiya ya jiyo wajena yana fadin haba uwata akanshi saiki daina fita ko ina ai nan gidan kune kema kamar ko wani da kike a gidan nan ai. Hawaye na dinga saukewa ya tsaya ya dan lalasheni wajen kafin ya fita bansan ya sukayi ba da baba din halima daice ke fada min wai ya samu Dada yana fada ankai karashi wajen baba. To yanzu kuwa zai saka kafan wando dani a gidan nan ke nan idan ya ganeni sai ya makeni ko a inane naja tsuki ina fadin ya kasheni idan yaso an fada mashi kowa mahaukacine irinsa ? Washegarine kamun anty Nafisa don haka tun safe kowa yake busy a gidan duba ga yadda gidan ya kara cika sosai da mutane tako ina mutane sai zowa sukeyi na dauka part din hjy mum ba zai cika kamar na mai bukin ba sai gashi an kai ga bude sauran dakunan dake rufe a part din bakin katsina sun sauka ciki. Don ita bangaren mai bukin yan gayu ire iren matan abokan baban kano da matan yan uwasa dake birni aka sauke a cikin part din su kuma yan gida anan wajen . Don haka nike faman dawainiya dasu kome sukeso nice zasu kira su tambaya donko sun tambayi hjy mum zatace su nemoni don haka ko yaushe ina basy. Dole ina kallon kowa nashiri don fita zuwa wurin kamun amma ni hakan bai samu gareni ba don ko wanka banyi ba ina faman dauko min da miko min ga mutane ga mutane da ganin iyaka. Haka nayi ta daurewa ina komai sannu a hankali har yakai saura iyamu da hjy mum data tsaya shiryawa a lokacin sai wata da nake yawan yiwa dawainiya a dakin nata mu muka saura a part din don haka zamu rufe kafin mu dawo daga can din. Na dauka zan samu su halima a waje amma kodana rufe kofan nafito kamar yadda hjy mum ta umurceni dayi saina samu babu kowa a wajen sai inta da wanan kawar nata a wajen. Hayaniya gami da dariya danaji a bayana yasa na dan juya hjy mommyce tare da wasu abokanta suka fito suma a cikin shirinsu lokacin har hjy mum ta bude wani mota tashiga nan naga sunja sun tsaya cikin mamaki. Kizo mu tafi hjy mum ta fada hakan yasa da sauri na dago kafa na samesu na bude motan nashiga ta tayar muka bar wajen wai ashe ban sani ba nan rigima sukeyi akan motocin maigidan saisu da shakikanaune suka san hakan. Don abinda ya faru shine hjy mummy ta karbi mota daga hannun mijin datake ganin zatayi sha,anin bukin ta burge kowa a wajen har kishiyan nata tasha mamaki wajan . Sai gashi ta fito taga hjy mum ta shiga dayan motan nasa dayafi tsada a gidan ta wuce ta barta nan gashi kuma itace ta zabi wanan dake wajenta don haka yanzu me zatace dashi kuma ? Don bata taba zato ko tsamanin wayewan hjy mum yakai haka ba a ganinta don ita hjy mum komai nata a addinance takeyinsa bata faye irin rigingimun duniya din nan ba. Gashi kuma tana zaunene bata kaiga ganin irin shigarta ba inda itama hjy mum din sam bataso hjy mummy din taganta a yanzu ba sai idan anje wajen ni kaina da yanzu na zamo yar koren hjy mum din ta kyashewa shigata na buje da rigan less daya fito min da suran matashiyar budurwa mai tasowa a jikina. Wanda kalan light pink din less din yai matukar min kyau ga dinkin da ganinsa an kashe mai kudi sun min dauri dayake dan baiya kitson kaina hakan yasa hjy mommy jan guntun tsuki tana fadin. Haukar banza wai hankaka maida dan wani naka ke nan ita ala dole ala tsiya yar nan take kokarin mayarwa nata abinda ba zai yuyuba ke nan kuwa a gidan nan ta dauko muna wata yar ta jefa muna gida don kawai kyashi da hassada mafarin duk abinda akaiwa yayana tace sai anyiwa wanan yar ke nan ko ? Koda yake ma aikin banza idan mutum ya isa ya haifo ya macen mana mugani da ake min wai kallo adole itace mai yaya maza a gida yanzu ko ga yaya matan sun taso sun tsone idanu. Kai hjy malka banga abin damuwa bafa wajen wanan bagidajiyan mata daba kowa yasanta bama sai yan tsiraru in fitsari banzane kaza tayi mana duk inda kika shiga dai dole akalleki a barta wani hadewa zatayi gaki a wajen. Wanan ya karfafawa hjy mummy din gwiwa don dadata da na kut da kut dinta sukai mata saiga waya ana cewa suyi sauri an fara program din event din. Ba can mukaje ba saida muka biya wani gida muka dauki wasu mata biyu muka koma mu uku a bayan motan kafin muka doshi wajen. Karyan yan kano da son bidi,a wajen ya hadu da manyan da kananu kowa tana nuna halinta don bame bari a barshi baya wasu sunzo daga bangaren amarya wasu kuma daga bangaren ango haka wasu sunzone ta uwar amarya haka dai kowa da dalilin zuwanta wajen taron. Tun shigowan mune kallo ya koma gun hjy mum din da yaranta suka sayo mata tsaraban lafaya tun daga Dubai don kawai su fidda uwarsu kunya basuji tsadansa ko kudin da zasu kashe ba a wajen sayan . Haka nima a cikine bataji zafi ko kuashin dinka min ba don kawai yadda ta amince kuma ni din na zage ina fitar da ita nauyi da kunyan da bata zata ba a lokacin saboda kawai
Chapter 17 · 0% Book details