← Book details Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 61

Sashe 35

Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Banda wani aiki don haka mum tace in shirya in bisu naje don hankalina ya kwanta a can muka samu su maito dasu halima da Asiya don banko sanda fitansu bani. Ina shiga Anty ke fadin ehh sister badon ke dake da kula ba da yaron nan ya mutu muna zaune ana faman surutu a daki ba wanda ya kula da hakan gareshi. Mum tace haba bai mutuwa ai sai idan kwanansa sun kare wahala dai akewa gudu amma kowa ya mutu dama iya abinda ya debo ke nan a rayuwanshi. Mun jima a nan take min hira cewa dan iskan uban nasa dazun daddy ya buga mai waya yana sanar mashi gamu asibiti sai cewa yayi Allah ya sauwaka kawai. Mum ta kara kada baki garemu tace to me zaice Nafisa dole dama ai addu,an samun lafiya zai masa tace ki bari kawai hjy mum habib dan iskane na gaske dama ya fadi ya barmin cikin duk abinda na haifa inje inji dashi tunda nace ban yarda a zubar da cikin ba. Kinga dan nan dayaki anty idan Allah ya bamu raida lafiya wata rana shine mai tallaban rayuwansa saukin abin agaremu bakece baki kaunar yaron ba ai kuma yan family din mu kowa yana kaunarsa kauna mai tsanani. Yarone fa amma ki duba daga dakin nan har waje duk yan uwane suka taru akan dan nan insha Allahu sai yaji kunyar wanan abin dayayi wata rana. Kwatsam ya hafiz ya fado dakin kallo daya nayi masa na dukar da kai ina tuna irin yanayin da naganesa a ciki a dakinsa sai naji girmansa da kimarsa da nake gani yazube min ga ido. Gashi tsab zakice mutumin kirkine a fili ashe a boye mutumin banzane irin na bugawa a jarida din nan muryan anty nafisa ce yakatse min tunane a lokacin take fadin wai baki gaidashi ba sister. Firgigit nayi tare da fafin wa hafiz mana ta fada nace ai nagai dashi daya shigo na kara fadin ina wuni tsuki yaja yaci gaba da magana da yar uwarshi ya fita zance na. Mummy ce ta fado dakin da kawayenta kallon yadda muka hade kai da anty muna magana kus kus kus ga iya zaune a saman tabarma bata ko jin me muke fadi tashigo. Kallo mu ta sakeyi tana fadin to rakwato aisai ki fita ga bakina nan sunzo duba yaro kar kuma a kaimu haba mummmy please ki dainawa yarinyar nan haka a gaban mutane mana sai a dauka haka halintane ai yar ta fada ciko bacin rai. Ban san ya sukayi ba don na bi driver nakoma gida sai washegari na sake lekasu asibitin koshi da nace ba zanje ba don mummy saboda nagane dai ta tsaneni a zuciyar ta. Banje da niyar zama ba muna zaune saiga ya Addel da budurwansa sun shigo wanan gulma ya zaunar dani muna kallon ikon Allah yadda ake soyayya nami sai a barshi kawai akan soyayya don idonsu kan rufene a lokacin. Donko abinda ya Addel keyi ba zakice shine ba ko don iyamu yarane a wajen lokaci saiko yan tsofin dake zaune daga waje ga yarinyar da alama ba kunya gareta ba. Don ko garemu katsinawa wanan rashin ta idone mutum yazo gun dangin miji tun baishigo ba yana wanan kaudin haka ba nuna alkunya ga kowa sai nuna sani da iya tun a nan ta sure min a zuciyana. Shiko yana faman washe baki yana jin dadi nace kaiya anyi ba,ayi ba kenan mutum kamar ya Addil Allah ya hada da wanan kalar macen kuma ? Yar gayuce ta fada amma hade da rashin kunya ko gayun nasune yake jawo masu rashin kunya oho saidai mazan dake son su basu ganin hakan. Basu jima suka tafi ina gefe daya lafe ina kallon ikon Allah saida suka tafine kowa ke fadan albarkacin bakinsa kan yarinyar nasa nikan ina tsoro ban furta komai ba nabarwa cikina mamaki. Aiko labari har kunnen iyayyen mu yakai nan hjy malka aka samu abin fadi don tun mum bata gane ba har ta gano ta tsureni tana tambayana amsa daya na bayar shine kila bayan fitowana sukazo. Wanan kalman ya rabani da kowa lafiya ana gobe suna aka sallamo su Anty suka dawo gida har lokacin uban yaron bai tako yazo yaga dan nasaba. Ko hakan yasa anty Nafisa yin sanyi ba kilama don gaskiya abin yana damunta sosai don tun tana boyewa har ta fitar muna da damuwanta fili nida iya da muke dakin wanda ba komai ya dameta sai rashin radawa jaririn suna da uban bai aiko ba. Nan ta gane lalai furcinshi akansu da gaske yake har dan ya yafe mata ke nan yake nufi wanan nasan yasa hankalinta tashi adaren sunan. Don ba itaba har mummy lokacin jikinta yayi sanyi da zancen don ta rage yawan rigiman da takeyi da farkon haihuwan sun koma shiru shiru yanzu. Ashe bamu sani ba daddy yaci masu mutunci daga uwar har yar nata don yakira shi habib din kan zancen sunan ya so gayawa daddu din zancen banza akan anty nafisa din shine shi kuma ya sauke haushin hakan akansu da yadawo gida. Bayan ya fitane nashigo nan ne take muna korafi nida iyan mai kula dasu shigowan ya Addil gidan yasa muka danji sanyi inda yace suna kan za,ayisa don ba za,abar yaro ba suna ba ai hakan saiya zamo abin kunya ga family tunda yana da ubansa. Ga daddy yayi rantsuwan cewa bai yankawa yaron rago da kudinsa duk nan takewa yaya din complain yace yaro kan yana da gatansa ai don bai fado a gidan banza ba . Shi dai da ya mayar da kansa dan iska yaje duniyace ai zata bashi darasi komai dadewa bayan ya gama lalashinta yake tambayanta sunan da take so ta sanyi dariyan yake kafin tace ga uwarsa nan zeey ka tambayeta sunan da sukeso. Farat nace yaya kasa mashi mohammad don Allah mu dinga kiransa da Amir baiyi magaba ba bayan dan kalloni da yayi sai washegarin suna kowa na zaman darr sai gashi ya shigo yana fadin suna da Mohammed rago biyu manya aka yanka. Sai akwatina set da aka shigo dasu wai inji uban da wanda komai na baby da uwa ansaka aciki daya kai wajen Dada ta kawo ko mum bata san yayi wana hidimar ba don ya hana yar uwarshi kukan zuci mai yawa. Albarka yasha shi wurin kowa wanda bakin mummy ya mutu mutus da ganin kayan idan ba dan gida ba yadda kowa ke fadi idan yashigo yaga kayan zasu tambaya wanan kayan sunane ace masu ehh. Zakiji sunce gaskiya yayi kokari haka akai suna kowa na farin ciki da yamma akai walima anci ansha an raba abubuwa kamar ko wani suna aka watse. Da daren kuma wanan budurwan nasa ta zowa jariri da nata gudun mawan shake da leda don ko Pampers har hudu nagani a cikin kayan. Ranan kuma bata tafi ba saida tabi su mum ta gaidasu taba kowa turmi daya daya har Dada wai na fitan suna wanda kowa yasan aiki ya Addil ne hakan. Sani mum bata so yasa hjy mummy kama zancen kamar da gaske wai danta yayi dace da mace ta gari gaskiya wanda kowa yasan bana Allah takeyi ba hakan da takeyi dayan biyune. Ko dai don rufawa yarta asirine da yayi ko kuma akwai abinda take kokarin kullawa gareshi nan gaba don danin halin mummy din da kowa yayi. Mun dora abubuwan shagalin sunan da akayi wanda har ita maijegon ta dora hakan yasa shi uban dan gani a status dinta har yabi bayan kwana kamar ukku da suna saiga yan gidansu sunzo. Da nasu kayan suna wanda ba wani abin azo agani ciki kuma wai sunan da Sani sunan kakansa Dada ko ta hausu tace su dauki kayansu su tafi yaro ya rigada yaci sunanshi dama mohammadu daga iyayyensa masu kaunarshi. Mum ce tasaka baki har suka danji sanyi aka karbi kayan da sukazo dashi din daga bangarensu suka tafi tsomai tsomai dasu da kunyan da dan uwansu yaja masu. Haihuwan nan na anty Nafisa yasa innan mu zuwa gidan akai akai wanda zuwanta kusan uku duban maijego da danta bayan suna kuma suka dauke kafafun su don gudun magana. Ganin angama shagalin buki lafiya yasa na mayar da hankalina kan karatu na da yanzu saura kiris mu kare gaba daya mu fada wani matakin a yadda nakewa kaina fata nan gaba. Don ganin yadda su Mairo suka maimaita shekara yasa ko ysushe ina addua Allah ya taimakeni inketare nawa ba tare da tabgardan komai ba ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/15, 08:01] Maman K: DUBA MIN BAYA FOKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Tayi jidalinta ta fice don ya Addel dayayiwa mum signal da ido akan ta kyaleta don Allah kada ta biyewa shirmenta na banza su zama daya wanan yasa mum din kyaleta badonshi ba ita ta iya biye mata sosai. Ga mum irin masu soka magana dayace ya tsaya wa mutum a rai kalma daya biyu zuwa ukku zata fada da zaisa mommy jininin wata da watani agidan. Batan fitan ta kaina suka juyo ranan mum tayi min kaca kaca saida ya Addil ya kwaceni ya nunawa mum aiba laifina bane tunda bazan iya cewa bazanje ba don ita din ba sa,ata bace amma da akai hakan yafi ai. Ranan ban koma gun maijegon ganinsu ba gashi tana ta aike da bugo waya nazo amma fir naki na shareta har takaiga bugowa mum waya tana nemana. Hakan yasa dole da dare na dan shiga na lekasu ban jima ba kuma na sulale tana bayi na fito nadawo part din mu hakan yasa da saffe ina kitchen sai gata ta shigo da kanta tana fadin ina mum ? Hjy mum nazo naji dalilin dayasa
Chapter 35 · 0% Book details