Sashe 48
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
za,ayi masa Dad ka fita zancen kawai muga tsiya shidin banza zai tsaya yana juya mutane haka. Dakata hakana naji zancen kowan ku ai magana ta gaskiya a yanzu banda halin yin hakan bandai sanarwa gaba ba idan rai ya kaimu lafiya. Ko gaban ba za ai masa ba daddy ai ba shi kadai ka haifa ba su sauran yan uwasa fa idan akace sai abinda yake so za,ai masa kada ya zauna mana. Da dai kin bari mun roki Dad din ayi masa yadda yakeso din zaifi sai a gaba da babinsa ba shike nan ba ya Addil ya fada cikin ladabi . Aliyu nasan meyasa kakeson hakan to ba zanyi ba yaje yayi duk abinda yayi niyar yi kada ya fasa idan ban canza masa gidan ba koba shike nan ba donshine ma na kiraku ku manyansu kuji . Dad din ya shiga masu dogon sharhi akan rayuwan dan nasa yace ya kuma sani ko zancen giidan nan da hadin bakin uwarsa ya furta hakan cewa sai a canza masu wani don bai zama kusa da dan uwasa a waje daya. Nan dai suka tashi a hakan bayan sun fito sun dan jima a waje suna zancen kafin ya Addil din ya tafi wajen matarsa data kirasa don tana gidan iyayyenta a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/28, 06:27] Maman K: DUBA MIN BAYA FOKON,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO. Duk wanan badakalan da akeyi iyayyena basuce uffan ba duk ko da zagi da cin mutuncin da mummy keyi kamar a gabansu take fadinsa don komai sunaji amma sun taushe zuciyarsu saboda zumunci. Akwai sauran imanin zumuci a lokacin dan uwa na iya bugun gaba da dan uwashi ako wani lokaci ya yanke hukunci akansa ba tare daka daga kai kace don me akayi hakan ba. Duk dadai har duniya ta nade akwai masu imanin gaskiya da biyayya bisa ga tsarin musulunci don sai ince duk yawancin al,adun malam bahaushe kadan ne yake tsarin al,ada duk koyine da addini bahaushe yake abinsa. In banda yanzu da boko ya sauya wasu suke ganin tsarin na farko ba tsari bane akwai tauyewa acikinsa yasa karfin zumunci da bahaushe yake girmamawa ya rage a zukatan mutanen yanzu sosai bisa ga mutanen baya da suka kwanta dama. Allah ubangiji ya jikansu da rahama ya gafarta masu albarkan kalman shahadan da suka rike a bakunansu Allahuma amin. A kwana a tashi hasaran rayuwa inji malam bahaushe buki dai ya karato kowani bangare sai shiri akeyi inda hjy mum gwaggona uwar dakina itama ba,a barta a baya ba wajen shirya yarta da zata kai aure watau ni ke nan. Don ko wani tsimi wani gunba wani hayakin jiki dana tsuguno da siracin irin na shuwa duk nashashi a wajen hjy mum don sai dare yayi kafa ya dauke zata tasani agaba da wa yanan abubuwan tun ina sha ina amai har ya fara zama min aciki saidai idan nasha zuciyana ya dinga tashi inyi ta barci. Sai yanzu nake tuna abubuwan nan don tun ina karama muke shiga daji debo wasu ganyewa matan gidan mu na kauye wani lokacin muke hada masu kafin yan sari suzo daga birni suna saya. Wanda sai na mahaifiyata ya kare kafin saura su samu shigar da nasu don ita tasam hadi don hakanema nima na koyi hadin ina taimaka mata wajen hada abubuwa. Sai yanzu tunanen hadin yake dawo min arai naga ai nima nasan dame dame ake hadawa ya zama gumba ko hayaki ko gari da sai sauran haki irin na yar mai ganye . Tabbas sudin ne don na tuna da dandanonsu hakan yasa na fara tuhumar wasu daga ciki sun fito hannun mahaifiyata ke nan. Saboda nasu hadin na El,sutura daban ne dana saura ba irin hadin neman kudi bane kawai hadine na sahihi da masana tasirin ganye a jikin dan adam suke hadawa mata don amfaninsu. Hadine mai inganci dake saukarwa mace da ni,ima da gyaran jiki ki koma abin sha,awa agun kowa duk wanda yasan asalin yar mai ganye yasan yadda maganinsu yake da kyau da tasiri agun manya da yara don ita yar mai ganyen asali bata tsaya iya gyaran mace ba kadai har yara da masu lalura tana taimakawa da magani cikin yardan ubangiji kuma a dace harma da maza wani lokacin suna dace idan sun samu yar asalin yar maiganyen na ainihi. EL,SUTURA TANA SOKOTO YANZU HAKA ZAUNE GA DUK MAI BUKATAN MAGANIN TA NA AINIHI HAR GOBE AKWASHI KU GARZAYO KUSHA MAMAKI DA IKON ALLAH . Saura kwana hudu bukine anty Nafisa ta turasasa min binta zuwa wajen gyaran jiki inda ta kaini wani shagon gyara na mata suka fara gyara min jiki tun daga kaina zuwa tafin kafana basu barshi a baya ba . Don bayan dilka ga kitso ga kumshi ga kuma turaren jiki bayan wanda hjy mum ke banka min din itama ta dora nata akai don hakane duk inda nazo na tsaya zan bar wajen da kamshi. Duk da ba fita nakeyi ba ina dakina ko dakin mum in kafa ya dauke kuma a falonmu . Saidai hakan bai hana halimatu yawo da sunana wajen classmates din mu da sunan raba chewegun din buki tana tallana cewa auren hadi za,amin ai. Mijin baisona amma ni sai rawan kai nakeyi dan naga dan maikudine tun yanzu na dara dagawa mutane kai shine ita tace bari tazo ta kawo masu IV don kar,a manta juna. Wanan dalilin yasa Anty Nafisa daukana kowa bai sani ba gidan takaini wajen gyaran jiki don ta fahinci irin makircin da sukeyi suna son bambanta sha,anin da wani manufa. Sai gashi suna ganin gyaran da akai min sai kuma ya koma tsone masu ido ni ina ta kaina su kuma suna hassada dani bansan dalilin wanan abin ba nasu akaina koda yake ba abin mamaki bane don mummyce uwarsu fa. Hakama kawayen da halimatu ta gayato sai sunzo zasuga aiba gaskiya ta fadaba don yadda suke samuna cikin rashin dadin rai a lokacin zasu fita suna gulma nan dai Allah zai wankeni akan zargin su gane gaskiya a take. Nida kaina na fadawa wayanda muke courses tare yanzu gaskiyan abindake faru dani sun kuma tausaya min jin zanyi aure da fara karatun mu ta hanyansu suka kara walwalewa kawayen namu gaskiyan al,amarin sabanin abinda halimatu ta fada masu kaina. Ban taba ganin mahaifina ya shigo wurin hjy mum ba harsu kebe su dade suna magana sai a yau da ya saura kwana biyu daurin aurena da yaya Hafiz ba alamansa nasan wanan maganan kodai wani daya shafi rayuwanane ya kawo baba wajen hjy mum din har suka dade irin haka suna tataunawa a falonta dashi. Daddy ko ance kallo daya zakai mai kagane hankalinsa ba a kwance yake ba don ance ya fada sosai don tashin hankalin abinda dansa keson yimasa na bashi kunya ga yan uwa da mutanen arzikinsa ga kowa sunan hafiz ya sani a cikin yayansa don haka sunajin auren Hafiz ne ai zakiji mutum yace insha Allahu muna nan zuwa damu za a daura auren. Wanan ganin da nayiwa baba da mum ya kara daga min hankali sosai da har na kasa fitowa washegari ina kwance a daki sai da mum ta leko tana fadin wai ke lafiya kin shige daki tun safe baki leko ba. Zaune nakena mike kafa saman gado dake nuna alaman lafyata kalau illa da dumuwa kawai ke damun zuciyana lokacin na dan dago da zuman kallonta saiga hawaye ta ko ina idona sunyi hulu hulu saboda kuka da naci. Kai haba mama yanzu kuma don Allah damuwa ko kukan nan meye kikeyi hakane don kawai ki tonawa kanki damu asiri mama. Ya kamata ace kinsawa zuciyanki dangana game da zancen nan don kin gani a zahiri tun ainda aka fito har kawo yau din nan babu alaman canji ko gezau ga Alh gareku. Aiya kamata ki dauki hakan a matsayin kaddara ki yarda ki amince da hakan kaddarakice mama yin biyaya zaisa kiga Allah ya sakawa rayuwanki ba zaki taba tabewa aduniyan nan ba insha Allahu. A hankali na iya dago kai na kalli mum din ina fadin mum badon wanan nake kuka ba ni ko waye daddy zai ban ya bani amma ba ya hafiz mashayi dangiya da,,,, Haba mama kul na sake jin wanan kalamin a bakinki kin taba jin inda hannunka ya rube ka yanke kayar wanan dalilin na cikin nacin auren ku da Alh keyi don yasan irin tarbiyanki yana fatan ta dalilinki hafiz ya shiryu nan gaba. Mum ta ya ni zan iya shiryashi bayan Allah daya haliceshi yakewa sabo ga kuma daddy da mummy aisu ya kamata ace sun gyara abinsu bani ba ni har wani hikima nake dashi da zan gyarasa. Addinin ki da tarbiyanki mama dasu zakiyi amfani ki gyara dan uwanki dashi ke dai kawai banda garaje kinsan halin hafiz sai kin bisa a sannu. Ba kuma ance da zuwanki ki fara masa zancen shaye shayenshi ba a,a cikin hikima da basira da saka wa,azi da kuma addua idan da rabo sai kiga kinyi babban jahadi kin kwatoshi daga wanan mumunan dabi,an. Ki tashi maza ki wanka ki gyara jikinki kamar kowa don gida ya fara cika da baki ko tun yanzu don yan katsina na nan sun fara isowa kuma suna tambayan ina kike ki kuma adana duk wani abinda kikeso cikin wardrobe dinki ki kulle ki miko min key din na rike a hannuna tana kaiwa nan ta juya ta fita daga dakin. Jin hakan dole natashi nashiga bayi nayi wanka na fito na samu wani yadin material da akaiwa dogon riga na saka a jikina. Mum ce ta kwala min kira daga dakinta na amsa nashiga take fadin in dauki abinci inci itama shi takeci a lokacin ban