Sashe 54
Duba Min Baya Fakon Biri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kafin ta fahinci inda Alh ya dosa da ita. Bawai tana nufin ya zauna dani dole bane a,a suyi nasu irin takon suma su nunawa Alh din ai suna tare dashi da hakane zata fahinci me yake nufi da canzawabshi. Duk da dai bai sake mata magana ba akan dan nata amma tasan shirun shi a yanzuma din maganane bawai ya kyale zancen bane akan a tafi a haka hakan na nufin shima da nasa shirin akansu ke nan. Anty nafisa bata dadara ba saida ta dauki waya ta kirani bayan sjn gama waya da mummy tana fadin sis ashe kina shigowa school shine baki taba nemana ba sai yau dana ganku din nan ? Ina zuwa anty iyakaya department din mune kada nayi wani laifi kuma ace ina yawo donshine ban zuwa ko ina idan nashigo amma kiyi hakkuri don Allah na fada a karshe. A,a aiba komai nafahince ki amma ki sani dake da hafiz din dukkan ku kanne nane don kinzo waje na bashi zaisa a jefiki da wani zargi ba sai dai idan dama kina da wani manufa akaina. Na danyi murmushi na sake fadin anty kiyi hakkuri ba haka bane na fada maki gaskiya kawai don ki fahinceni bayaga school a yanzu babu inda nake zuwa kuma. Gidan na bude nashiga ina sauke ajiyan zuciya tare da zama ina bin ko ina na gidan da kallo kafin in sauke ajiyan zuciya ina lumshe idona na fada bayan kujera na fara tunane. Wayana dake aje gefena dana aje yake dan haske alaman kira yana shigo min a lokacin na dauka ina kallo number kasar wajece Canada na gani a rubuce. Na sake maimaita sunan garin har kiran ya tsunke ban daga ba don ina tsoro banda kowa dake kasan waje da zai kirani nayi tunane a zuciyana lokaci guda. Saiga kiran ya kara shigowa again nayi karfin hali na dauka na kara a kunnena ba tare da nayi magana ba sai naji muryanshi yana fadin. Keda wullakanci ana kiran waya kina share mutane me kike daukan kankine wai ko kin dauka kina da wani matsayin da za,a kirakine wai ? Muryanshine ba tare da sallama ba yatareni da fadin hakan daga daukan wayana kafin ya koma fadin ke ina kika fita kikaje ba tare da sanina ba ? Wai waye hakane don Allah kamar ba musulmi ba daga daukan waya sai bakar magana kamar mara hankali to wrong number naja tsuki na kashe waya kai tsaye. Ina jin yana fadin kika kuskura kika kashe min waya wallahi dip na kashe wayan ga baki daya ina jan tsuki nace wawa dab giya kawai kafin in koma fadin. Lalai mum tayi gaskiya da takece min na kula da Anty Nafisa don yanzu a matsayin yar miji take a gurina watau dan ganin nan da tayi min har ta buga masa waya kai lalai mutum abin tsorone duniya. Wasu zafafan hawayene suka zo min lokaci guda suna sintiri a fuskana har sai yaushe wanan zai fahinci iyayyenmune na tambayi kaina ina runtse idanuwana a cikin takaici. Wanan kila ya kora tsiyar nasane yake son ya karanto min hauka daga kawai fita zuwa school inba abin dan giya ba zaka kirani kana zagina. Na dade zaune a wajen kafin na mike zuwa dakina na sauya kayan jikina zuwa na shan iskan gida banso yin girki ba amma dole nayi saboda maigadina tun lokacin da yace min shi bakone daga kauye yazo neman abinci kano ya samu gadi nake tausayinsa. Dadina guda shine Allah baiyini da yawan magana ba don haka ban fadawa kowa abinda ya faru ba balle a ban shawaran na dakata da karatuna dana kwallafawa rai. Don hakane washegari na shirya na nufi school duk da zancen ya tsaya min a raina ni kadai nake hade abina tunda banda abokin shawara a lokacin. Ina nan zaune da yake ina fashin sallah naji sallama a gefena na dago ina amsawa watace tsaye a gefena take fadin ko zan iya zama ni bakuwace a department din nan bansan kowa ba asalima dai ni ba yar gari bace transfer akai muna muka dawo kano daga Lagos. Zaki iya zama mana na fada ina kawar da kaina gefe daya takai zaune tana bissimillah sai hakan ya burgeni amma ban dago na kara kallonta ba duk da kamshinta dake shiga hancina a wajen. Itama din karatunta takeyi hankali kwance har lecturan da zai dauke mu ya shigo ajin muka mayar da hankalin mu ga abinda yake koya muna din. Ya dade kafin ya fita lokacin ta juyo ta kalleni tana fadin gaskiya ban fahinceshi sosai ba da zan samu karin bayani zanso ni dai banyi magana ba sai kokarin bin abinda ya koya muna nakeyi. Tana kokarin jana da hira duk da basar da ita din da nayi a lokacin bai hana taci gaba da magana ba dani sai amsa da nake bata a takaice take fadin in taso muje wajen motarta mu karya don lokacin break yayi. Sai lokacin na dan dago ina fadin nagode ban tare da yunwa saida na karya na fito ke dai yar uwa naga kamar baki natsu dani ba niko kaf ajin nan dake hankalina ya kwanta. Nagode na fada tace kinsan komai gamon jinine na hango natsuwa a tare dakene sunana hauwa Garba daga Niger state muke aiki ya kawo mu garin nan duk da mijina uwarshi yar garin nan ne ita. Sai lokacin nayi dan murmushi a fuskana ina dagowa nace surname din mu daya dake ashe nima zainab Garba katsina nake bearing a takarduna. Tace shike nan mun zama sisters dake ashe shine mafarin sakewana da wanan bakuwar da yanzu take dan sakani magana koda ban son ba kuwa. Don irin mutanen nan ne masu son asani nan halinmu yasha bamban da ita amma ba laifi tana da son naci ga karatu ga yadda na fahinta idan an koyar bata gane ba zatayi ta nacin da sai ta gane kome ake nufi wanda nima ina kara fahinta ga hakan. ZAINAB IDRIS MAKAWA [3/1, 07:51] +234 706 511 1949: *_GUDUN ADDARA_* *H U G U M A* PAGE 13 Waya ta sameshi yana yi. Dogon wando ne fari qal a jikinsa da singlet fara itama,sai ya ajjiye wayar yana duban tanja data tsaya nesa da falon "Mainasara bibi ce take kira" "d'accord" ya amsa can qasa da muryarsa me sanyi. Ko daya baiyi niyyan shiga sassan bibi din ba,ya sanyama ransa ma sai tayi cigiyarsa kafin ta sake ganinsa,saboda yana ganin cewa suna da tagomashi wajen lalacewar ginin da ya fara yiwa rayuwar sultana. Saidai kuma bibi din ta wuce ta kirashi yaqi zuwa,don haka ya sauke qafafunshi dake saman table qasa yana ajjiye wayarsa saman kujerar ya wuce zuwa bedroom dinsa. Kaftan abaya budaddiya ya zura navy blue,kalar data fidda sigar kyawunsa matuqa,haskensa ya fito sosai,ainihin zallar hasken cikakken ba'abzine. Kamar yadda yake dabi'arsa hannayensa zube a aljihun kaftan abaya din yana qissima abubuwa da dama cikin ranshi. Iskar bayan azahar tana kadawa kadan kadan me cakude da sanyi maras tasiri. Ire iren wannan yanayin suna masa dadi sosai kasancewarsa mutum ras son zafi ko kadan. Hatta da sutura ba kowacce yake sanyawa ba saboda baison abinda zai takura jikinsa. Da nutsatstiyar sallamarsa ya shiga parlor din bibi. Ta amsa masa tana karantar nazarinsa sanda yake basarwa ba tare daya kalli fuskarta ba,daya daga cikin alamun fushinsa kenan. "Samu waje ka zauna" bibi ta bashi umarni kai tsaye,ita dinma yau fuskarta ba'a sake take kamar yadda ta saba ba. Kaman bazai zauna din ba sai kuma ya matsa sofa din gefanta ya zauna a kai bayan dukka wadanda ke zirga zirga a falon sun kau,don basu waje. "Aliyyu" bibi ta kirashi da sunansa na asali kai tsaye. Sexy eyes dinsa ya daga ya kalli Bibi sannan ya motsa bakinsa "Kada kace komai maina,mamaki kurum yanzu kake bani" ta fadi tana qare masa kallo tamkar tanason hange meye abinda ya canza a tattare dashi da ya sauya launin mu'amalarsa da sultanan tashi "Gaba daya ka canza maina,kamar ba kai ba,ka tashi daga mainan sultana ka koma aliyyu haidar,ka tashi daga fr ren sulty ka koma wani abu na daban,kana neman zamewa yarinya kamar wani dodo,kamar ba kaine ka raineta da hannunka ba?,kamar ba kaine kaci kashi da fitsarinta ba?,kamar ba kaine kake hana idanunka bacci saboda sultana na kuka ko tana rigima ko bata da lafiya ba,dukka ina wannan kulawar?,tsakaninka da ita yanzu sai kyara sai hantara sai tsangwama,sama da tsangwamar da kakewa kowa cikin gidan nan" bibi ta qarashe fada tana sauke maganganun nata hade da fitar sirrin numfashi,da alama daga qasan zuciyarta maganganun suke fita "Me yasa bibi?" Ya jefa mata tambayar,idanunta kadan ta qanqance tana dubansa alamun neman ba'asin tambayar da yayi matan "Me yasa bibi zaku barta ta sangarce bayan kowa cikin gidan nan tarbiyya bai daya ake musu,waye tafi cikin yaran gidan nan bibi?,sai abinda sultana ke so?,sai abinda ya kwanta mata a rai yayi kuma dai dai da raayinta?,bibi wannan ba soyayya bace sam ba qauna bace,ita din diya macace,gidan wani zataje,baki tsoron ta tashi a haka taje masa da dabi'ar da bazai iya ba a dawo muku gida da ita?,wala'alla ni din bana kusa da ku,kune zaku fini jin ciwon hakan,kuma kafin ni na gani ku zaku fara gani kune zaku fara karbar sakamakon" "Auzubillah......haidar me kake cewa haka?" Bibi ta fada fuskarta na nuna girman da zancan yayi mata. Ba komai saman fuskarsa kaman ma baisan me dame ya cewa bibin ba ya dage dukka girarshi biyu "Oui(yes)" "Dukka maza ne zasu iya daukan halin banzanta?" "Subhanallahi,da gaske ka sauya maina,ka canza,na tabbatar fr ren sultana bazai taba fadin haka a kanta ba......to bari kaji,kai din yaro ne da har yanzu bai wuce shekara ashirin da biyar zuwa da shida ba,a dukka matakan tarbiyya banjin kasan wani abu me yawa,bata haka ake yiwa yaro tarbiyya ba,tsanani da matsi basa kintsa yaro ko kadan,ka sanyawa sultana zafi da yawa,kana amfani da irin zafinka na halitta,ita diya mace kwata kwata bata buqatar zafafawar namiji,bare kuma yaran mata da yanzun suke tasawa tarbiyyarsu nada matuqar sulbi da santsi,don Allah maina.....banajin dadin canzawarka kwata kwata,ka koma fr re din sultanansa na baya". Idanunsa ya lumshe sannan kuma ya budesu, muryarsa a