Sashe 9
Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Maganar Khadijah tamkar a wasa ko ƙuruciya bayan kamar wata biyu aka nemeta aka rasa ita da Dafeeq. Hankalin kowa ya tashi, tako ina aka shiga nemansu amma babu labarinsu. Da ga ƙarshe aka samu saƙon wasiƙa daga garesu suna bama iyayensu haƙuri akan sunje suyi aure, amma in sha ALLAHU watarana zasu dawo garesu.. A take Baba ya yanke jiki ya faɗi, ranar sai a asibiti ya kwana. Yayinda iyayen Dafeeq keta tujara wai Khadijah ta janye musu hankalin yaro da asiri, ya daina jin maganar kowa sai tata da tasu Baba. Maganganu marasa daɗi dan har gida sukazo suka cima Umma mutunci da Baba dake kwance yana fama da kansa...
Duk da wannan labari duk ya shiga kunnen Dafeeq da Khadijah basu koma gida ba, sai ma tattarawa sukai suka ƙara gaba. Sunyi aure kamar yanda suka shiryama kansu da taimakon hakimin yankin da sukaje. Dan sun haɗa masa ƙarya da gaskiya ne shi kuma ya amince. Sai dai bayan auren nasu ya basu shawarar komawa gida. Sun yarda da hakan, amma sun nema alfarmar a ɗaga musu ƙafa sai bayan lafawar abubuwa sosai. Wannan dalilin ne yasa ya barsu, tare da basu gida matsakaici, ya kuma zuba musu kaya a ciki masu ƙyau tare da nemawa Dafeeq aikinyi a wani Company. Aikin ba wani aiki bane babba can, dan na sharane acewarsa ya fara kafin a samu mafita, yadai samu abinda zai riƙe matarsa.
Ansha amarci na nunama tsara tsakanin Khadijah da Dafeeq. Dan Son juna suke tamkar zasu cinye kansu. Kowa ƙoƙarin ƙyautatama ɗan uwansa yake. Sun manta da gida da iyayyensu gaba ɗaya. Sam Khadijah bata tuna jarabawarta da ta baro a lokacin da ake gab da farawa duk da tsananin son da takema karatu a baya. Idonta ya rufe gaba ɗaya babu wanda take tunawa da gani sai Dafeeq. A haka sukaci watanni huɗu, sai ga ciki. Sosai Dafeeq ya nuna farin cikinsa da samuwar wannan ciki, ya shiga tattalinta kamar ƙwai, sai dai bayan kamar sati biyar sai kuma tayi ɓari. Tasha kuka sosai dan ta mugun ƙwallafa rai a cikin nan, haka shima Dafeeq ya shiga damuwa, daga baya dai suka lallashi kansu suka cigaba da rayuwarsu ta faranta ran juna. Ba'a ƙulla wata biyu ba sai ga wani cikin dai, nan ma sunta murna, sai dai shima bai kai labari ba ya zube. Nan ma kuka suka dingayi rurus har sai da matar hakimi ta dinga musu nasiha sannan suka haƙura. Bayan shi Khadijah ta sake samun ciki sau biyu yana zubewa, zuwa lokacin kuma sun ƙulla shekara kusan biyu da barin gida. Tun daga ciki na huɗu daya ɓare bata sake samun ciki ba, tun suna damuwa har suka dangana, a yanzu haka kuma shekara ta uku suke. Khadijah nada shekara goma sha tara, Dafeeq nada Ashirin da uku cikin da huɗu. Basu da wata matsala sai ɗan faɗan masoya irin na yau da gobe, basa jimawa kuma suke shiryawa saboda ita Khadijah nada sauƙin kai, koda Dafeeq ya ɗauki zafi da ita takan nuna masa itace a ƙasansa ta bashi haƙuri tana kuka da roƙonsa da magiya. Har yanzu Dafeeq na aiki a companyn nan, da ga shi har ita basa zancen komawarsu makaranta, shiko bayan shara a kamfani baya sana'ar komai, dubu sha takwas ɗin da ake biyansa duk wata acewarsa ai ya ishesu rayuwa. Khadijah bata taɓa damuwa da haka ba, dan tana son mijinta, shi kaɗai ta sani a sabon garinsu, sai gidan baba hakimi da takan ɗan je lokaci-lokaci ta gaishesu. Shima kuma bayan ita da gidan baba hakimin babu wanda tasan ya sani sai abokan aikinsa na Company, amma abin mamaki yau sai gashi da key na gida da mota yana faman farin ciki da iƙirarin wai nashi ne. A ina ya samu? Waye ya bashi? A dalilin mi aka bashi?. Waɗan nan tambayoyin take zumuɗi da burin yazo ya amsa mata ko zata samu nutsuwa a zuciyarta itakam....
(To Khadijah muma dai zamu so san jin ina Dafeeq ya samo key na gida da mota haka. Amma bari mu leƙo JJ na amarya Alimah mu dawo dai🚴🚴🚴).
★★★.....
Cikin ƙarfin hali JJ yay wanka ya shirya a ƙananun kaya marasa nauyi. Duk tunaninsa su Baba na falo ne basu wuce ba, dan haka ya fito cike da ƙwarin gwiwa. Amma sai ya samu falon wayam. Zuru yay yana kallon kujerun, sai kuma ya shiga laluben aljihunsa cikin tsumar jiki alamar neman waya. Babu komai, da alama ya barsu a ɗaki ne ko. Ya ayyana a zuciyarsa yana komawa da baya zuwa ɗakin. Babu wayoyin nasa duka biyu anan ma, dan haka abin ya bashi mamaki kuma. Fitowa yay da ɗan hanzari, sai hakan yay dai-dai da fitowar Alimah da ga nata bedroom ɗin. Suna haɗa ido tai azamar rissinar da kanta cikin jin kunya, sai kuma ta fara magana ƙasa-ƙasa da badan yana kusa da ita ba ba lallai yaji ba ma.
“Ai ban san ka fito ba. Ga abinci to dan ka samu kasha magani kamar yanda Yaya ya faɗa”.
“Sun tafi ne?”.
Ya faɗa kamar cikin rawar murya. Kanta ta jinjina masa batare data ɗago ba ta ce, “Eh, ai kana shiga ciki suka wuce su kuma. Shine ma Yaya Mujee yace daka fito kaci abinci kasha maganinka”.
Cikin kullewar kai da rashin makamar riƙewa ya jinjina mata kai kawai. Ga wani irin matsanancin tsoro na ratsa masa zuciya. Amma dai ya dake a zahiri dan yana son tabbatar da abinda ya faru a daren jiya. Murya a sanyaye ya ce, “To muje ki bani”.
Babu musu tai gaba ya biyota a baya har zuwa tsakkiyar falon. A ƙasan carpet ya zauna kamar yanda yaga tayi itama a gaban kwanikan abincin. Ya zuba mata idanu yana kallon yanda take zuba abinci, sai ƙafafunta da yake kallo suma lokaci-lokaci. Zuwa can kamar wanda aka zaburar ya ce, “Alimah na tambayeki dan ALLAH?”.
Duk da tayi mamakin jin ya kira sunanta kai tsaye sai ta jinjina masa kanta batare data bar abinda take ba ko ta ɗago. Shima bai damu da rashin ɗagowar tata ba ya cigaba da faɗin, “Daga bayan dawowata raka abokaina jiya zuwa sanda kika kira aka kaini asibiti miya faru?”.
Cikin ɗan jin kamar mamakinsa ta ɗago ta kallesa. Sai kuma ta sake maida kanta da sauri ƙasa. Kamar bazatace komai ba sai kuma ta nisa a hankali. “Bayan ka dawo ka sake samuna a falo, shine kace muje ciki muyi salla, ka ajiyeni saman gado kace na jiraka anan kayi alwala, shine ka shiga bayi ni kuma barci ya ɗaukeni. Da'alama dai banyi nisa ba na farka a dalilin jin ihu da nayi, na tashi a firgice sai naji motsinka a bayi, baifi mintina biyu ba tsakani ka fito, shine kace na koma falo na jiraka kana zuwa. Ban jima a falon ba ka fito ka sake samuna, shine ka sake cewa na tashi muje sallar. Kaine ka kaini har ƙofar bayi dan nayi alwala, bayan na kammala na fito na sameka a ƙasa ka faɗi, na nufeka ina ƙwalama kira ka tashi ka maran, sai kuma ka sake sumewa, ni kuma kawai na fara haɓo. Nata kuka ina zuba maka ruwa baka farka ba shine nai kiran Rabi'ah lokacin kusan ƙarfe huɗu na dare, shine sai ita kuma ta gayama Yaya Mujee yazo muka tafi asibiti da asuba.”
Tunda ta fara maganar jikin JJ ke rawa. Dan gaba ɗaya muryarta ta koma ta wadda bazai taɓa mantawa ba a rayuwarsa. Duk da kuwa bai kamata ace itace kaɗai zata zauna masa a zuciya fiye da sauran na baya kafin ita ɗin da bayanta ba. Jin shiru yasa Alimah ɗagowa a hankali. “Yayana wlhy ni fa duk a tsorace nake”.
Wani irin yankawa ƙirjinsa yay na tsantsar firgita. Tuni ya zabura yay tsalle gefe cikin kaɗuwa. “Anoosh!” ya faɗa cikin rawar baki jikinsa na ƙara ɗaukar rawa..
“Anoosh kuma?”.
Cewar Alimah tana masa kallon tsoro. Zaraf ya miƙe har yana taka plate data zuba masa abinci. Baibi takansa ba ya kwasa da gudu zuwa ƙofa, sai dai yana isa ruff ta rufe kanta da kanta. Baya yaja da wani irin rawar jiki yana zaro idanunsa gaba ɗaya waje. Sai kuma ya waiga bayansa da sauri. Alimah na tsaye tana kallonsa, da sauri ya juyo gabansa, nan kuma Anoosh tsaye jikin ƙofa itama tana kallonsa. Rigifff ya zube ƙasa kamar wani tsohon amalen raƙumi daya gama morar duniya......✍️
(😂 Uncle JJ namu🚴).
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na shida_
📲 *UMMUL~ADNAN DATA SERVICE*📲
We offer you the most affordable and cheapest data🥰
*MTN*
📲500mb ➖ 170
📲1gb➖340
📲2gb➖640
📲3gb➖940
📲4gb➖1250
📲5gb➖1550
📲10gb➖4000
Check balance=*131*4# or *460*260#
*GLO* *CORPORATE GIFTING*
📶500mb➖150
📶1gb➖270
📶2gb➖540
📶3gb➖790
📶5gb➖1300
Check balance=*127*0#
*AIRTEL*
🆒500mb➖150
🆒1gb➖270
🆒2gb➖530
🆒3gb➖800
🆒5gb➖1270
🆒10gb➖2510
Check balance=*140#
*9MOBILE*
☑️500mb➖140
☑️1gb➖240
☑️2gb➖480
☑️3gb➖660
Check balance = *228#
All network valid for 30days👌
*PAYMENT*
Through this acct
7032785536 ZAINAB SARKI AHMED
OPAY
CABLE SUBSCRIPTION ARE ALSO AVAILABLE
Phone no 07032785536
____________