Sashe 73
Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
........Rayuwa taima ango Abaan daɗi fiye da yanda yay hasashe. Hakama amarya Khadijah dake samun kulawa a garesa da ahalinsa. Idan kaje gidan dolene rayuwar cikinsa ta burgeka musamman yanda kowa ke girmama ɗan uwansa. Tsakanin ango da amarya kam ai ba'a cewa komai. Dan soyayya ce mai tsafta da tarin birgewa, tuni Abaan ya kaɓar da ƴar sauran kunyar Khadijah musamman idan an shiga daga ciki. Yanda soyayyarta tai tasiri garesa haka itama tashi tuni ta mata shigar sauri saboda nagartattun halayensa. Bayan sun dawo Kano ya bar ƙasar. Ya barta da damuwar rashinsa kusa da kaɗaici, sauƙinta ma ta koma zuwa wata babbar islamiyya anan kusa da su. Sashenta kawai masu aiki ke gyarawa, nasa kuwa ita da kanta take wannan aikin batare da jin gajiyawa ko ƙosawa ba kullum duk da baya nan. Takan shiga sashen Mamy susha hirarsu, dan Noor ma tana zuwa aiki. Satinsa biyu ya dawo aka cigaba daga inda aka tsaya. Ita ke tsaye kan hidimar mijinta da safe. Hakama idan lokacin ɗora abincin rana yayi tayi musu da kanta dan in har Abaan na Abuja zuwa ake a amsar masa abincin rana daga gida akai masa office. Dan haka nan ma ta riƙe ragamar girkin rana. Bana safe da rana kawai ba, na daren ma ita ke shirya musu abincin mara nauyi, sannan ta koma sashensu tarbar mijinta duk da in har ya shigo gidan ƙa'idarsa ce sai yazo ya fara gaishe da mahaifiyarsa sannan, hakama idan zai fita sai yazo ya mata bankwana. Idan sun kamala ƴan hidimominsu kamar taimaka masa yay wanka da sauransu zai wuce massalaci har sai anyi isha'i ya dawo. Sukan nufi sashen Mamy ita da shi suyi dinner acan. Daga haka ai zaman hira. Goma nayi Mamy ke korosu, wani lokacin ma tara da rabi tace suje sashensu su ƙarasa hirar acan tagode. Noor kan dinga musu dariya dan su sunfi son ayi hirar anan. Saboda Mamy mace ce data san kanta. Dolene ma idan ka zauna da ita komanta ya dinga birgeka. A koda yaushe cikin gyara Khadijah take batare da Khadijahn ta farga ba. Dan ita dai sai dai kawai a bata abu ace ta shanye ko ta ci. Ita kuma saboda biyayya bazata taɓa tambayar Mamyn minene wannan ba balle ta musa sha kota zargi wani abu. Halayen Khadijahn na sake saka ƙaunarta a zuciyar mijinta da mahaifiyarsa harma da ƙanwarsa ɗaya tilo data zame mata ƙawa a yanzu duk da ta girmeta.
A wannan hali kwanci tashi Khadijah da Abaan suka cika wata goma da aure. Akan samu sassaucin yawan faɗa ko rigima ta ma'auratan zamani, ba komai yasa hakan ba sai kasancewar su su duka biyun masu haƙuri ne. Sannan Abaan ya girmi Khadijah nesa ba kusa ba, takanyi abu da yawa yay masa kallon ƙuruciyace kawai ya share. Wanda kuma ya zama dole yay magana a kansa sai ya zaunar da ita cikin nasiha ya ankarar da ita kaza ba dai-dai bane kazane dai-dai. Hakan da yake na ƙara saka girmansa da kimarsa a wajen Khadijahn, dan takanyi ƙoƙarin ganin ta kiyaye duk abinda zai ɓata masa rai. Takanyi waya da iyayenta a wayarsa, dan ita har yanzu bata da waya, bai siya mataba ba kuma ta taɓa masa magana ko nuna ta damu da son a sai mata ba duk da tana buƙatar hakan. Ko magana yake son yi da ita idan yana office sai dai ya kira wayar Mamy yace ta bata dan yasan da rana suna a tare idan bataje islamiyya ba. Idan kuma zatai waya da ko su Zuhrah ne tashin take amsa kota Mamy ko Noor. Bata taɓa nuna damuwar hakan ba garesa ko waninsa ko taji a ranta ana raina mata wayo. Sai dai ma takan ɗan ji kunyar cewa su ara mata tai wayarne wasu lokutan, koda tana da buƙata sai kawai ta haƙura.
Abinda Khadijah bata sani ba Abaan na gwadata ne kawai, dan Mamy tasha masa faɗan ya saya mata waya sai yace tayi haƙuri zai saya akwai abinda yake yi ne. Mamy tasan halinsa, dan haka ta saka masa ido kawai akan hakan. Dan daga baya itama sai ta fahimci dalilinsa akan ƙin sayen wayar. Ana cikin haka yay tafiya waje ya barta bata jin daɗin jikinta, takuma ƙi yarda suje asibiti, to anan ne fa shima abin ya fara cin ransa. Dan da rana dai yakan kira su Mamy su bata. Da dare kam yana son waya da matar tasa ko zaiji raguwar kewarta da lafiyarta babu dama. Da farko ya fara saka Noor ta bata tata, sai kuma nata saurayin yayta kira, wani lokacin kuma sanda shi zai kira saurayin Noor ya riga ya kira sai hakan ya ƙona masa rai. Ai fa babu arziƙi kwanansa goma sha biyu sai gashi ya dawo. Sam babu wanda yama san da dawowar tasa, dan ita Khadijah ma ranar jikinta ya takura mata ko sashen Mamy bataje hira ba, tadai je ta gaisheta ta dawo sashenta ta kwanta.
Cikin barci sama-sama take jin ƙamshin turarensa na hawar mata kai. Idanunta da sukai matuƙar nauyin barci ta buɗe a hankali. Lumshewa ta sake yi, sai kuma ta sake buɗewa domin tabbatar da shi ɗinne ko mafarkin data saba take yi. Shi ɗinne dai ba mafarkin take ba. Tashi tai da sauri, sai dai mi, ƙamshin turarensa na bugarta a guje ta nufi toilet sai amai. Hankalinsa ya tashi, ya taimaka mata ta gyara jikinta suka fito yana mata faɗan ya akai take barin ƙofa buɗe sauro na shigowa, dan shi zatonsa malleria ce, tunda yaga sanda aka kawota haka taita amai tana zazzaɓi. Ita dai batace da shi komai ba, sai faman toshe hanci ma takeyi.
Karon farko Mamy tazo sashensu tunda Khadijah tazo gidan, itace ta fahimci halin da Khadijahn ke ciki, tai mata tambayar ƙamshin miye bata so. Da ƙyar ta sanar musu turaren jikin Hamma. Idanu sosai ya waro waje, mi Noor zatayi inba dariya ba. Har sai da ya harareta sannan ya miƙe fuuu ya fita shi yaji haushi. Ita kanta Mamy sai da tai murmushi. Koda ya fitan ma Khadijah ta kasa sukuni, dan tace har lokacin tana jin ƙamshin. Dole aka haɗa turaren wuta da yawa Noor ta saka ako ina. Sai da aka ɗauki lokaci ga ac sannan tace ta daina ji, lokacin kuma Mamy ta kira Abaan da tunda ya tafi sashensa bai dawo ba tace yay kiran doctor.