← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 82

Sashe 33

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

          Hayaniyar mutane a kanta da zafin hantsin rana daya fara fitowa suka farkar da ita. A hankali take ƙoƙarin buɗe idanunta da sukai mata matuƙar nauyi, bata iya gane komai sai cakai-cakai ɗin mutanen da kowa ke faɗar albarkacin bakinsa game da ita. Wasu na ganin accident ne, wasu na ganin ɓarayine sukai mata haka suka yardata a bakin titin. Sai dai an kasa samun ko mutum ɗaya da zai taimaka mata. Hasalima kowa tsoron taɓata yake yi. Dai-dai tana ƙoƙarin sake buɗe idanunta a karo na biyu wata mota baƙa wulik mai ƙyawun gaske ta iso wajen. Kasancewar a hankali motar ke tafiya harta ɗan gotasu sai kuma aka gangara gefen titi ta gabansu kaɗan. Wasu hankalinsu akan motar yake, yayinda wasu ke cigaba da surutansu akan Khadijah.
        Da sauri drivern motar ya fito domin cika umarnin ogansa da yace yaje ya duba mike faruwa a wajen, ya nufo taron mutanen da ƴar sassarfa yana faɗin, “Bayin ALLAH lafiya kuwa? Mike faruwa kuka taru anan haka?”.
        “Wlhy wata yarinyace aka samu kwance anan kamar ma ta mutu duk raunuka a jikinta. Sai dai bamu san miya sameta ba ko dalilin yasar da ita anan ɗin. Gadai tanan da alama ta farfaɗo ma”. Wani magidancin dattijo ya bashi amsa cike da kulawa. Mamakine ya kamashi har ya bayyana a saman fuskarsa. Amma sai baice komai ba ya juya ya koma motar. Saitin sit ɗin baya ya tsaya tare da ɗan rissinawa yanda zai iya gani wanda ke ciki. Glass ɗin aka sauke a hankali, wani ƙyaƙyƙyawan kamilin matashin mutum ya bayyana. Cikin dattako da tausasa lafazi ya furta “Mike faruwa ne Awwal?”.
        “Wata yarinya ce Yaya aka yasar a wajen, sai dai suma basu san accident tai ba ko jefar da ita akayi, amma dai tana cikin wani hali kuma duk suna jin tsoron taimaka mata”.
     Shiru yay yana kallon Awwal ɗin cikin yanayin mamaki da ɗan ɓacin rai, sai kuma ya girgiza kansa batare da yace komai ba ya buɗe motar ya fito. Da sauri Awwal ya matsa ya bashi hanya. Tun fitowarsa motar ƙamshin turarensa ya baɗe wajen, hakan yasa mafi yawan mutanen waigowa suna kallonsa, sai kuma wasu suka shiga rawar jikin gaishesa duk da kuwa basu san wanene ba, sai dai kuma a duk inda mai kuɗi yake a cikin al'ummar mu ta yanzu zakaga an ɗaukesa ne da muhimmanci koda ba'asan wanene ba ko inda ya fito. Hannu kawai ya ɗaga musu cikin gyaɗa kai da faɗin, “Barka”. Sai kuma ya ɗan bisu da kallo da sake faɗin, “To mizai hana da wannan zagayetan da kukai ku ɗauketa ku kaita asibiti bayin ALLAH”.
      Ai kamar wanda yay shela a kunnuwansu, a take suka shiga darewa. Yayinda wasu ma suke ƙoƙarin barin wajen suna ƙunƙuni alamar dai su bazasu taimaketa ba kenan. Mamakine yake neman halakashi a tsaye, sai dai kuma bai gama haɗa mamakin nasa ba idanunsa suka sauka akan yarinyar dake kwance a wani yanayi mai ban tashin hankali da al'ajabi. Duk da shi ba ɗan sanda bane a kallo ɗaya da yayma Khadijah ya fahimci ba accident taiba dukane wannan. Bai ma san lokacin daya ƙarasa gareta da sauri ba yana baton sunan UBANGIJI.. Har ya kai hannu zai taɓata sai kuma ya dakata, sake ɗagowa yay yabi mutanen dake wajen da ido, babu abinda yake buƙatar gani, wato ƴar uwarta mace, hakan ya sashi ɗaukarta cak batare da ya kalleta ba zuwa motarsu dan gaba ɗaya mutanen wajen ma haushi suke bashi. Da sauri Awwal ya buɗe masa gaban motar alamar ya sakata anan. Amma sai ya girgiza masa kai da masa nuni da sit ɗin baya. Babu yanda Awwal ya iya sai cika umarni, a bayan ya kwantar da ita, shi kuma ya koma gaba ya zauna, yana ƙoƙarin rufewa Awwal ya miƙa masa takardar data faɗo daga jikin Khadijah. “Yaya daga jikinta ta faɗo.”
Takardar ya ɗan zubama ido kamar bazai amsa ba, sai kuma ya amsa batare da yace komai ba ya ajiye gaban motar. Zagayawa Awwal yay mazaunin driver, yana ƙoƙarin ma motar key ya ce, “Zamuje asibiti ne Yaya?”.
Kai ya gyaɗa masa alamar eh.
Jin sun fara tafiya Khadijah dake jinsu ta kai hannunta da ƙyar saman fuskarta ta share hawayenta. Cikin muryarta dake fita da ƙyar ta ce, “Dan ALLAH na roƙeku kada ku kaini asibitin garin nan ku wuce dani Kano. Idan ma mutuwa zanyi na mutu gaban iyayena ko zasu yafemin kar naje ga UBANGIJINA yana mai fushi da ni”.
        Da mamaki Awwal da yasan ba lallai Yayan nasa ya tanka ba ya ɗan dubeta ta mirror da faɗin, “Haba ƴar uwa wane Kano za'a wuce da ke a wannan halin, babu abinda kike buƙata ai sama da kulawar likita a yanzu”.
    Kuka ta sake fashe musu da shi tana cigaba da magiya. Har sun ɗauki hanyar asibiti idanunsa akan wayarsa tamkar baima san mike faruwa a motarba a hankali ya furta, “Muje airport ɗin”.
Sosai Awwal yay mamakin jin abinda Yayan nasa ya faɗa, dan shi dai yasan sun riga sun sayi ticket ɗinsu guda biyu tun a jiya da dare. Sai dai bai iya cewa komai ba sai amsawa da “to” cikin girmamawa. Daga haka ya ɗauki hanyar airport ɗin. Suna isowa airport ɗin yay kiran wani Attahir. Cikin mintuna kaɗan sai gashi ya isa. Fita yay yana bama Awwal umarnin zama a motar ya jirashi, shi kuma suka nufi wata hanya shida Attahir ɗin bayan ya leƙo yaga Khadijah da barcin wahala ya figa....

★Koda gari ya waye Dafeeq yayi zaton Khadijah na gidan bata wuceba. Dan shi a tashi wautar bazata iya barinsa ta tafi ba kodan wasu dalilai. Ƙwaƙwƙwara a cikinsu shine bazata iya tunkarar iyayenta ba saboda tsoro. Sannan tana masa matsanancin son da bazata iya taɓa rabuwa da shi ba. Ko sakin da yay mata guda biyu yayine dan gargaɗi, zai kuma maidata amma sai ya wajiga rayuwarta ta yanda ko kallon banza bazata sake marmarin sake kwatanta yimasa ba. Sai ta koma masa tamkar baiwa ta yanda kozai maidata ƙasa dan takawa bazata sake koda tari ba. So yake ta koma jin tsoronsa fiye da yanda takeyi a baya.
Baibi takan Kainaat ba sai ma hidimarsa yake hankali kwance kamar baida wata damuwa. Nan ko can ƙasan ransa addu'a yake ALLAH yasa Khadijah tazo ta bashi haƙuri da wuri. Anci Sa'a kamar yanda ya share Kainaat ɗin itama ta tattarashi ta watsar a wannan yinin ita a dole fushi take da shi. Hasalima yini tai a ɗaki kwance. Sai kusan uku na rana aka kawo mata order na abinci da tayi sannan ta sakko ƙasa. Sun fito kusan tare da Dafeeq da ke kwance shima a ɗakin, sai dai rashin jin motsin Khadijah ya damai ya ce bara dai ya fito ya duba. Sake tamke fuska yay lokacin da suka haɗa ido da Hajiyar tasa. Itama sai ta ɗauke nata kan batare da tace komai ba ta haura sama abinta cike da takun izza da taƙama. Ƙwafa yay da cije lips ɗinsa, yayinda yake ayyana abubuwa a ransa kawai. Sai da yaji shigarta ɗaki da rufe ƙofa sannan ya nufi ɗakin da Khadijah take da sassarfa. Sosai gabansa ya faɗi ganin ɗakin wayam, amma sai ya ƙarfafa kansa ya nufi toilet. Nanma babu kowa, babu ma alamar anyi amfani da ruwa dan ko'ina a bushe yake. Ji yay zuciyarsa na motsi a cikin ƙirji, dan haka ya fito har ƙafafunsa na harɗewa. Ƙofofin ɗakunan ƙasan ya shiga buɗewa, sai dai ko'ina babu ita babu alamarta. Shine har kitchen, nan ma wayam, ya sake komawa sama ya dudduba, nan ma dai shiru. Da sauri ya sakko ƙasa zuwa wajen maigadi........✍️

_Huummm Dafeeq. JJ 😡😡_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na goma sha tara_

_____________

METAFORCE online business ne Wanda malamai suntabbatar da halascinta masana suntabbatar da ingancinsa ba iri kasuwancin da'ake gudunmma mutane da kudin subane shi wannan an centralized ne ko Wanda ya kirkira bazai iya kulleshiba saboda Yana kan block chained.
METAFORCE zakashiga da kudi kadan ka dauki da yawa ummu khalilwacce take zaune akasar Nigeria sananniyace akan harkar METAFORCE ta kawomana hanyar sauki dansamun cigaba.
Zakasamu kudi Mai tarinyawa dawayar hannunka insha Allah
Yana da matakai 1....12
Level 1 anafarawa da 5$
Level 2 anadarawa da 10$
Level 3 anafarawa da 20$
Hakadai har zuwa level 12
Alkhairan metaforce
Kingama register za'abaki TR coins na adadin level din da kika bude
Samun reffaral bonus
Ga garabasar spillover
Da dollars suke biya zaka iya cirewa kamaida kudinka account nantake
Babu faduwa Babu asara aciki
Kishiga kasuwanci Mai tarin alkhairi zaka kwashi kudaden musamman kana gayyato al'umma.
Metaforce alkhairine ga duniya insha Allah

Phone number 07038708382/09069163665

_________________
Chapter 33 · 0% Book details