Sashe 8
Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Zuwa bayan la'asar aka sallamesu. Kamar yanda Doctor ya bada shawara gidansa aka wuce da shi. Sun sami mutane uku da suma suka dawo da Alimah babu jimawa dan tunda abin ya faru bayan an kaisu asibiti doctor ya tabbatar da ita bata buƙatar a kwantar da ita can gidansu JJ aka wuce da ita. Ƙannensa ne guda biyu sai sep mom nasu. Tana zaune a falo Alimah a kusa da ita tana mata nasiha, yayinda Rabi'ah da Sadiya ke tsaftace gidan duk da bawani datti yayi ba. A kusan tare JJ da Alimah suka kalli juna, tai saurin rissinar da nata kan cikin yanayin jin kunya da tsoro, shiko ya kasa yin hakan dan har sai da yayansa ya kamasa ya zaunar. Bayan Alimah ta gaida Abba da yayansa shi ta gaida da masa yaya jiki kamar yanda taji Umma ta faɗa cikin jajantawa. Itama da kai kawai ya amsa mata kamar yanda ya amsawa Umma. A haka su Rabi'ah ma suka fito suna masa sannu da yaya jiki. Suma amsa musu yay da kai.
Nasiha mai ratsa jiki Abba yay musu su duka, itama Umma ta ɗaura da nata. Sun sallami Alimah ta koma cikin bedroom wajen su Sadiya, suka sake rufuwa akan JJ a matsayinsa na miji babba da ya fita shekaru. Shi dai saurarensu kawai yake dan baima san yaya zai fassara al'amarin ba. Zuciyarsa gaba ɗaya a rufe take ruff, babu wani abu a jikinsa dake aiki a sashen tunani irin na masu hankali. Abinda kawai ya sani yana jinsu yana kuma ganinsu da idanunsa. Rabi'ah Umma ta ƙwalama kira, ta fito aɗan gaggauce tana amsa mata.
“Ki faɗama Alimah ta haɗa masa ruwan wanka ko? Dan ya kamata ya ɗan watsa ruwa ko jikinsa zai saki.” da to Rabi'ah ta amsa tana juyawa ciki, kusan mintuna shidda tsakani ta dawo ta sanar da an haɗa. Da taimakon yayansa JJ ya miƙe, yay masa rakkiya har bakin ƙofar sannan ya dawo. Daga haka suka miƙe su duka bayan an sake umartar su Sadiya akan su fito. Sosai Alimah ke hawaye dan bata son su wuce ita dai. Su dukansu sun fahimci tsorone a ranta, dan haka Umma ta sake lallashinta da tabbatar mata in sha ALLAH gobe su Rabi'ahn zasu dawo su yini mata. Kanta a ƙasa ta amsa da ta gode. Har tsakar gida tai musu rakkiya, suka wuce ransu fal tausayinta musamman ma Ummah da Abba da Yaya Mujee. Jiki a saɓule ta koma ciki, sai taji gaba ɗaya ma gidan ya fita mata a rai. Bata bi takan JJ ba ta wuce ɗakinta tana hawaye......✍️
_Ina fatan yau dai Yaya JJ zaisha amarcinsa da amarya Alimah 🥱🥱😆🚴_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na biyar_
https://chat.whatsapp.com/ImF9JpXmBISJCvMBGkTKLc
___________
📲 *UMMUL~ADNAN DATA SERVICE*📲
We offer you the most affordable and cheapest data🥰
*MTN*
📲500mb ➖ 170
📲1gb➖340
📲2gb➖640
📲3gb➖940
📲4gb➖1250
📲5gb➖1550
📲10gb➖4000
Check balance=*131*4# or *460*260#
*GLO* *CORPORATE GIFTING*
📶500mb➖150
📶1gb➖270
📶2gb➖540
📶3gb➖790
📶5gb➖1300
Check balance=*127*0#
*AIRTEL*
🆒500mb➖150
🆒1gb➖270
🆒2gb➖530
🆒3gb➖800
🆒5gb➖1270
🆒10gb➖2510
Check balance=*140#
*9MOBILE*
☑️500mb➖140
☑️1gb➖240
☑️2gb➖480
☑️3gb➖660
Check balance = *228#
All network valid for 30days👌
*PAYMENT*
Through this acct
7032785536 ZAINAB SARKI AHMED
OPAY
CABLE SUBSCRIPTION ARE ALSO AVAILABLE
Phone no 07032785536
________
.......A sanadin wannan abu daya faru mahaifin Khadijah yazo har makarantar tasu, yanda yayma malaman tas akan abinda ya faru na rashin ɗa'a da akaima yarinyarsa amma basu ɗauki mataki ba yasa aka hukunta Dafeeq. Dan shima har sai da mahaifinsa yazo makarantar. Abinda ya bama kowa mamaki shine kai tsaye ya amsa laifinsa, ya kuma bama Khadijah haƙuri. Abune da bai taɓa faruwa ba, dan ko mi zai aikata duk irin hukuncin da za'ayi masa bai taɓa bama koda malamai haƙuri ba saboda shegen girman kansa da rashin ji. An sallamesu komai ya wuce. Tun daga ranar kuma idan suka haɗu sai ta hararesa ta murguɗa masa baki. Shiko baucewa da ita komai sai dai ya ɗauke kansa ko yay dariya kawai. Sabon salon nasa na bama abokansa mamaki, dan akwai randa akai taren masu latti ƙiri-ƙiri ya hana a daki Khadijah. Abun nasu kamar wasa a wani hutu sai ga Dafeeq a gidansu. Da farko nunawa yay baba yazo gaidawa, a dawowa ta biyu kuma ya ƙulle da ƙaninta. Tun yana zuwa ya tsaya iya ƙofar gida har takai baba ya bashi damar dinga shiga cikin gidan ya gaida Umma. Ko kallonsa Khadijah batayi da farko, amma kafin hutun nan ya ƙare sai gashi ta fara sassautawa har tana gaishesa. Sannu a hankali al'amarin nasu ya fara sauyawa har yana koya mata karatu ita da sauran ƙannenta, da farko iyayen Khadijah basu ɗauki al'amarin komai ba, dan daga Dafeeq har Khadijah yarane. Kasancewar Dafeeq ya ɗan samu matsala a harkar karatunsa a baya ya bama Khadijah kusan shekara huɗu, dan ita bazata wuce 16years ba, shiko zai iya kaiwa 20 gashi kuma da tsayi. A haka Dafeeq ya kammala makaranta su Khadijah suka shiga ss3 suma. Yawan zuwan Dafeeq da yanayin da suke kasancewa da Khadijah yasa Umma ta fara fahimtar akwai magana a kansu, dan haka ta faɗama Baba. Yayi matuƙar mamaki da jin batun dan yasan dai su ɗin yarane, dan haka ya zaunar da Khadijah ya mata nasiha da sake tabbatar mata da burinsa akan tayi karatu mai zurfi kuma yasan itama shine babban burinta. Shima Dafeeq ɗin baba ya sameshi da nasiha akan ya dage ya cigaba da karatunsa su ajiye maganar wata soyayya gefe idan ma yana son Khadijah ne ya bari sai nan gaba yanzu su yara ne, amma idan sun kai girma yayi alƙawarin zai aura masa ita. Kamar Dafeeq da Khadijah sunji wannan nasiha fa, sai kuma gashi bayan watanni kamar biyu aka kawoma Baba shaguɓen yafa saka ido akan Khadijah kada yaron nan dake zuwa gidansa ya lalata masu ita. Hankalin Baba ya tashi, sai dai baima Khadijah magana ba ya fara bibiyar al'amarinta batare data sani ba. Ilai kuwa sai ga Baba ya gano inda Khadijah da Dafeeq ke ɓuya yin hira wai. Ranar ya zaneta duka irin wanda bai taɓa kwatanta mata ba, ya kuma takama Dafeeq burki da zuwa gidansa gaba ɗaya.
Al'amari kamar ya lafa sai kuma wasa da karatun Khadijah ya ɓullo, dan takai sam bata maida hankali har suna shirin fara jarabawar ssce. Tun Umma na lallashinta da mata nasiha a ɗaki su kaɗai har tadai faɗama Baba. Shi rasama abin faɗa yayi a wannan gaɓar, dan haka ya kira Khadijah ya tambayeta mi take buƙatane? Babu kunya babu tsoro kamar ba Khadijahrsa ba tace ita aure take so. Kuma Dafeeq take so. Kallonta kawai baba ya tsaya yi, sai da yaja wasu mintuna kafin ya sauke ajiyar zuciya da fuskantarta. Cikin lallashi da nuna kulawa yace to yaji zai mata auren, amma ta maida hankali akan jarabawarta da suke shirin farawa. Bayan ta kammala secondary ya mata alƙawarin tana fara jami'a koda wata biyu ne zai mata auren. Amma fa ta sani bada Dafeeq ba. Dan Dafeeq dai a yanzu haka yaƙi karatu, baya kuma sana'ar komai sai yawo da abokai, sannan iyayensa sunce ba aure zasuyi masa ba yanzu. Kuka ta fashe masa dashi tare da rantsewar itafa shi ɗin take so. Kuma idan ba'a aura mata shi ba zata bishi su gudu kamar yanda ya buƙata suyi aurensu acan wani waje. Cike da takaici da gatse Baba yace ga hanya nan ta tafi to. Daga haka ya buga babbar rigarsa ya fice a gidan ransa a ɓace.