Sashe 32
Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
JJ shine ya zama tamkar ɗan uwa na jini wajen jana'izar Hajiya Lailah, dan shine akan gaba, sannan shine ma ake ma gaisuwar. Shine ya kawo ƴan sanda akan shi bai yardaba sai a bincika a tabbatar da dalilin gobarar da alamu da yawa suka nuna akwai lauje cikin naɗi. Ba komai ya saka JJ yin hakan ba sai tsoron kar Anoosh ta rayu al'amari ya zama wani abu daban. Ƴan sanda sunyi bake-bake akan case ɗin, yayinda cikin ikon ALLAH suka samu wani ɗan alama da ya sakasu jin cewar lallai maganar JJ nada ƙamashin gaskiya, dan haka suka jajirce akan son binciko komai. A zahiri JJ na sake ingizasu da tsayawa tsayin daka akan binciken, a baɗini ko hankalinsa tashe yake da bin matakan toshe komai da zai bayyana gaskiya, tsabar son a yadda da shi ya kawo iyayen ƙaryar nan dai an ɗaura masa aure da Anoosh dan ya tabbatar musu da akowane hali take shi dai yana sonta. An jinjina ma wannan sadaukarwa tashi ƙwarai da gaske a anguwar, duk da ma auren an ɗaurashi ne kawai bayan idar da sallar magrib kamar yanda ya buƙata tare da waliyansa na ƙarya. Komai na Anoosh ya koma ƙarƙashin JJ batare da sanin kowa nashi ba, dan hatta ƴan san jin yanda akai idan sun so yin magana da shi baya yarda sai ma ya hau musu kuka akan shi su barshi yaji da abinda ya damesa. A haka Anoosh ta kwashe tsahon shekara kusan ɗaya kwance a asibiti. Tako ina al'umma na kawo taimako da gudunmawa, duk kuma abinda aka bada kai tsaye a asusun JJ yake tafiya. Duk da dai ana cire wasu ai hidimar asibitin. Tana da shekara ɗaya da wata uku likitoci suka bada shawarar fita da ita ƙasar waje yimata wani ai. Ɗari bisa ɗari JJ ya yarda da batun, har ma an fara shirye-shiryen hakan, sai dai kwanaki uku dayin maganar ALLAH yay mata rasuwa. Ta rasu idanunta ƙyam akan JJ tana hawaye.
Yanke jiki JJ yay ya faɗi a wajen, sai da doctor ya tsaya kansa ya farfaɗo. Yanda yake wani irin kukan tashin hankali dole ka tausaya masa, dan harga ALLAH da gaske kukan yake yi. An kai Anoosh makwancinta na gaskiya JJ na a wani hali, bai kuma samu kansa ba sai a washe gari. Kamar yanda ya zama komai a yayin rasuwar Hajiya Lailah a ta Anoosh ma dai shi akema gaisuwar har akai addu'ar uku. Bayan ƙura ta lafa ya ɗan cigaba da zuwa anguwar har bayan wasu watanni, dan haka gidan su Anoosh ya cigaba da kasancewa a ƙarƙashin kulawar ƴan sanda da dattijan anguwar. JJ ma dake zuwa jefi-jefi ya rage zuwa. Watanta bakwai da rasuwa ya haɗu da Alimah. Ƙyaƙyƙyawar yarinya mai kama da larabawan Sudan. Dan Alimah ba fara bace, sannan bata kasance baƙa wulik ba. Mace ce har mace a tsaye da sura ga ƙyawun fuska da ko mace ta kalleta sai ta sake kallo.
Alimah dai ƙawa ce ga Rabi'ah ƙanwarsa. Department ɗin su ɗaya a F.C.E. A wata ranar babbar salla tajema Rabi'ah yawo gida sukaci karo da JJ a ƙofar gida. Cikin masifa ya ɗago a zatonsa a cikin ƙannensa ne. Amma sai yaci karo da halittar data nema gigita rayuwarsa. Dan kuwa dai sumar tsaye yayi har Alimah ta gama magiyar bashi haƙuri baima san tanai ba sai da Rabi'ah ta taɓashi ya dawo hayyacinsa. Bai iya cewa komai ba, face gyaɗa kai tamkar wani dole. Bayan shigewarsu gida sai shima ya fasa fitar ya koma ciki. Zama yay a falo tare da su, dukkan wani motsin Alimah akan idonsa ne. Tun ma bata farga ba har dai ta tsargu. Al'amari kamar wasa dai sai ga magana ta zama babba, dan lokacin da Alimah da ƙanwarta suka tashi tafiya sai JJ ya dage akan zai kaisu gida. Badan taso hakan ba ta amince aka tafi harda Rabi'ah suka maidasu gida. Wannan shine sanadin da JJ yasan gidan su Alimah. Bayan sun dawo gida kuma ya titsiye Rabi'ah da tambaya akan Alimah. Itako ta sanar masa komai. Tun daga lokacin JJ ya koma kai Rabi'ah makaranta da kansa, yakan je kuma ya ɗakkota duk dan Alimah, sai dai duk yanda yaso Alimah ta kulashi hakan ya gagara, iyakarta da shi gaisuwa matsayin yayan ƙawarta Rabi'ah.
Irinsu JJ idan ALLAH ya tashi kamasu ba'a magana, dan kuwa dai da gaske neman zaucewa yake akan Alimah, yayinda itako ta cigaba da jansa a ƙasa. Bawai wulaƙanci take masa ba ko zaginsa, kawai dai bata shiga sabgarsa ne bayan gaisuwa. Taƙi kuma bashi fuskar tunkararta koda da magana ne. Haka ya cigaba da haƙuri da jurewa dan so yakema Alimah na gaskiya, soyayya ta aure. Har faɗama abokansa su MB yake shikam ya samu matar aure. Hakama gidansu kowa yasan yana son Alimah. Dan danan JJ aka fara gini, sannan ya rage abubuwa da yawa musamman akan harkar mata. Da farko iyayensa sunyi mamakin inda ya samu kuɗin gini haka, dan filin kansa ba wannan suka sani nashi ba. Amma sai ya musu bayani akan kasuwanci ya shiga shi da wani uban gidansa aka samu yay albarka, hasalima ubangidan nasa ne ya bashi filin. Sanin wanda yake kira da uban gidan nashi yasaka su yarda, duk da kuwa ya kamata a matsayinsu na iyaye su bincika uban gidan nasa tunda bawai ya wani jima da kawoshi garesu ba ne. Amma tunda kudi na shigowa yana ɗaukar wasu daga cikin ɗawainiyarsu sai babu wanda ya sake masa magana akan hakan.
Ya cigaba da ginin gidansa da yaƙin campaign ɗin soyayyar Alimah, wadda da ƙyar da ƙyar ya samu ta fara kulashi. Ya fara rawar jikin kashe mata kuɗi mahaifinta ya taka masa birki, tare da shimfiɗa masa dokoki na neman ƴarsa in har da gaske yake. Babu musu JJ yabi kowace doka, dan hatta hira bayayi da Alimah sai a falon mahaifinta tare da ƙannenta biyu. Sannan akwai cctv camara a falon da mahaifin nasu ke ganin duk wani motsinsu da ga bedroom ɗinsa. Sannan a sati sau biyu yake zuwa kawai hira, dokace bazai tsareta a hanya ko makaranta ba ko dan ya ganta a gidansu. Ako ina suka haɗu gaisuwace kawai, hira dole sai yazo gidansu. Da yake da aure JJ keson Alimah duk ya amshi waɗan nan dokoki da hannu biyu kuma yana kiyaye wa har iyaye suka shiga cikin lamarinsu. Ahakan ma dokar bata sauya ba, dan duk da mahaifinsu ba wani mai kuɗi bane akwai dai rufin asiri tsaye yake akan ƴaƴansa. Shekara ɗaya aka saka bikin, akwana a tashi ta cika aka shiga shagalin biki. A gidan su Alimah ɗaurin aure kawai sukayi babu wata bidi'a a ciki, sai dai bayan an kaita gidan su JJ ne suka ɗora da nasu bikin a yanda suke so. Shine akai dinner da dare bayan an kaita gidansu, washe gari aka kaita ɗakinta....
★______________★