← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 82

Sashe 82

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na arba'in da huɗu_

*_NACE KIN MALLAKI NAKI👋??._*

*_NAKI NAKE NUFI KIN MALLAKA KUWA👋🏻👋??_*

*_TIKITIN SHIGA JIRGIN TAWAGAR ZAFAFAN LITTATAFAN NAN NA ZAFAFA BIYAR NAKE MAGANA SISTER KIN MALLAKA👋👋👋🤔??_*

*_KIN SAN KUWA A WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA DABBANCE. IDAN NACE DABAN INA NUFIN DABAN A CIKIN DABAN_*

*_A 2024 ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN NAKU SUN SAKE ZUWA MUKU DA WASU SABON SALO NA MUSAMMAN DA ƘAYATARWA AKAN FARASHI KAI SAUƘI DA RAHUSA. DAN HAKA INA GAYA MIKI ƳAR UWA KADA KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE_*

_Littatafan sune kamar haka 👇🏻_.

*_KWANKWASON JIMINA....._*
_(NA MSS XOXO)_

*_GUDUN ƘADDARA_*
_( NA SAFIYYA HUGUMA)_

*_TSUSTAR NAMA....._*
_(NA BILYN ABDULL)_

*_AMEENATU_*
_(NA MAMU GEE)_

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥

_______________

.........Sosai Khadijah tasha kuka da ganin irin wulaƙantacciyar rayuwar da su Dafeeq suke a ciki shi da Kainaat. Kasa haƙuri tai tun a daren ta kira Alhaji Abaan ta zayyane masa komai. Shima dai al'amarin ya matuƙar girgizashi. Dan haka washe gari da suka zo ɗaurin aure bayan an kammala da yamma ya ɗauki Khadijah da autansa da autan su Khadijah sukaje har asibiti yaga su Dafeeq. Kuka sosai Kainaat ta dingayi da ganin Abaan. Ya sake zama babban mutum duk da shekaru sun fara nuna kansu. Amma dayake akwai kuɗi da hutu da jin daɗi yana nan a ɗan gayunsa ga aji da rashin son hayaniyar nan tashi. Babban abin sha'awa yanda yake tattalin Khadijah sa da ƴaƴansa biyu dake tare da su. Dan Muhammad da Fharooq suna makaranta su. Kasa iya cewa komai Abaan yay sai rungume Khadijah da Mimi dake kuka yay a jikinsa yana lallashinsu. Dan bayan komawarsu gida sai da Mimi tai yanda tai Aunty Jamila ta bata labarin tushen komai da basu taɓa sani ba. Anan ta fahimci tushen rikicin da aka sha a lokacin shirya aurema Yazeed ita sanda suke a shekarun ƙuruciya. Wanda da ƙyar suka sha a dalilin marigayi Baba Hakimi. A take Alhaji Abaan yasa aka canjama su Dafeeq asibiti zuwa Abuja kamar yanda Khadijah ta roƙa. Dan kafin ma su gama shagalin biki su an wuce dasu. An kuma fara basu taimakon da duk ya dace kodan matsayin Khadijah na babbar likita a asibitin na Abuja. Lokacin da suka kammala biki suka dawo Abuja Dr Khadijah ta cigaba da treatment ɗinsu su duka tare da taimakon likitoci. Yayinda Alhaji Abaan ya zuba maƙudan kuɗaɗe da ake basu cikakkiyar kulawa ta musamman. Kafin kace mi abubuwa sun fara daidaita a kansu. Dan kuwa an sakama Kainaat ƙafafun roba duka biyu. Yayinda jikin Dafeeq ya fara murmurewa. Kafin cikar shekara guda sun ɗan dawo hayyacinsu musamman da yake akwai lafiyayyun abinci ga kulawar lafiyarsu. Sai dai Dafeeq bai iya tafiya sai a wheelchair. Gara ita Kainaat ɗin takan ɗan miƙe akan sanduna. Sai dai itama tafiyar tata bata wani nisan zango. A kullum cikin kuka suke da nadamar rayuwarsu musamman ma Kainaat data rasa iyaye da dangi baki ɗaya. Dan tun da ta baro Niger babu wanda ya sake waiwayenta a ƴan uwan nata. Ga rashin ƴaƴa. Ƴar ɗaya tilo ta musu nisan da ko labarinta ma basu da ƙarfin ikon ji sai kukan zuci. Ko ƴan aiki da Khadijah ta ɗiba musu suke tare da su a ɗan gidan da suka basu dan bayan sun sami lafiya Kano aka sake maidosu haka zakaga suna musu wulaƙanci da daka musu tsawa. Yanda masu aiki ke tsoron iyayen gidansu su ga waɗannan ba haka bane. Iyayen gidan ne ke tsoron ƴan aikin. Dan basu musu komai sai hantara da wulaƙanci. Suna zama dasu ne kawai dan amsar kuɗaɗen albashinsu. Su kuma sun gagara iya gayama su Khadijah gaskiya dan kar suga sun cika ƙorafi. Saboda komai a rayuwa su Khadijah sun musu bai kamata su damesu ba kuma.
      Lokaci-lokaci idan su Khadijah sun shiga Kano sukan leƙa su duba su. Musamman ma Khadijah dake yawan shigowa saboda harkar aikinta na likitanci data samu ɗaukaka daban-daban saboda ƙwazonta. A yanzu haka akowane ƙarshen sati biyu akwai jihar da take zuwa bisitin matsayinta na gawurtacciyar likita da ake ji da ita a Nigeria ma baki ɗaya ba Abuja kawai ba. Ga mijinta daya kasance shahararren ɗan kasuwa lamba ɗaya musamman a fanin shinkafa. Dan zuwa yanzu bama a Africa kawai ba, a duniya kamfanin Alhaji Abaan yana cikin wanda ake matuƙar ji da alfahari dasu a harkar shinkafa. Kuɗi dai kam Alhmdllh akwaisu. Ga ɗaukaka ga suna ga taimako duk ALLAH ya basu. Dan Khadijah ta kafa wata ƙungiyar wayar da kan mata musamman ƙananun yara da iyaye akan harkar soyayyar ƙuruciyar nan da dayawa take kashe rayuwar yaranmu da nakasar zukatan iyaye. Tare da ƙarfafa iyaye akan tsayawa akan ƙafafunsu wajen ganin sun tallafawa ilimin yaransu musamman mata. Dan ɗiya mace tana matuƙar buƙatar ilimi kodan sanin yanda zata tafiyar da rayuwar aurenta ma da tarbiyyar yaranta. Domin kuwa wannan ƙarancin ilimin ya taka rawar gani akan mahaifiyar Khadijah a lokacin da soyayyar Dafeeq ke ɗibarta. Maybe da tanada ilimi data kasance mai tsayawa da bin matakan jan ra'ayin ɗiyarta. Hakama iyayen Kainaat. Maybe da sunada ilimi da basu yarda ƴarsu ta zubar da su ba a idon duniya ta ɗauki wasu iyayen barikin. Duk da dai idan mukai dubi da wani faninin kuma Kainaat nada ilimin ai, amma bai hana ƴarsu Banan ta bijire musu ba itama harta maimaita abinda Kainaat ta aikatama nata iyaye. Hakan na nufin koda ilimin sai an haɗa da ƙyawawan halaye da tsayawa wajen biyayya ma iyaye. Dan iyaye basu kasance abin wasa ba a wajen kowanne irin ɗa komai lalacewarsu da baƙaƙen halayensu. Dan kuwa dai Banan taga hakan, dan duk da baƙin halin iyayenta Kainaat da Dafeeq hakan bai hanata itama ɗan ɗana kuɗarta ba. Tunda da ga ƙarshe ta ɓige da ƙasƙantacciyar rayuwar prison. Ta kuma ratayama kanta alhakin rai. Inda ta koma ba dukiyar babu iyayen babu nasarar rayuwar. Hakama a fannin Khadijah sai da ta girbi abinda ta shuka duk da kuwa ita nata iyayyen ma ta roƙa gafararsu kuma sun yafe mata kafin subar duniya. Amma duk da haka sai da UBANGIJI ya ɗanɗana mata irin wannan zafin data ɗanɗanama iyayenta domin taji ta tabbatar da iyaye ba abin wasa bane ba. Hakama bijire musu babbar musiba ce kuma illa ga rayuwa. Sai dai ALLAH ya taimaketa kasancewa mijinta mutumin kirki mai tsarkin zuciya yasa komai ya daidaita cikin sauƙi suka cimma burinsu na aurar da ƴarsu cikin salama ga wanda taso kuma yake sonta a kuma lokacin da sukai fata. Haka dama rayuwa take cike da ƙalubale kala-kala da kuma nasarori. A wasu lokutan gaggawarmu ke hanamu zuwa ga nasarorinmu. Wani lokacin kuma son zukatanmu ke yanke mana igiyoyin nasararunmu. Mun manta cewar UBANGIJI ya ƙaddarara dukkanin ƙaddaririn namu tunkafin haihuwarmu. Babu kuma mahaluki ko alkalamin da takardar da suka isa canjawa daga abinda zuciya ke so zuwa ga abinda ke a rubuce a taskar ALLAH. Dan haka mu kasance masu tsoron UBANGIJI a duk inda muke a kuma duk yanda muke. Mu kasance masu jin soyayyar MANZON ALLAH a zukatansu akowane hali dan ita a garemu wajib ne. Mu kuma kasance masu biyayya da hakuri da iyayenmu koda abinda suke so mu bai mana ba mu so shi in sha ALLAHU zamu ribatun a wata rana koda ƙasa ta lulluɓe idanunsu. Sannan namu ƴaƴan muma zasu kasance masu biyayya a garemu.
       Ya rabbi ka shiryemu ka shiryamana yaranmu. Ka tsaremu katsare mana zukatanmu.  Ka saka gaskiya a harshenmu, ka saka gaskiya a zukatanmu, ka saka gaskiya a ayyukanmu da gaɓɓanmu. Ya rabbi ka hanemu saɓa maka da ganganci ko akan rashin sanin ka tsaremu daga aikata ZINA. ka shiryi masu aikatawa idan masu shiryuwa ne. Idan ba masu sjiryuwa bane ya rabbi ka nisantamu da su ka nisantasu da ƴaƴayenmu. Ya rabbi ka shiryi masu irin halayyar JJ idan masu shiryuwane. Idan ba masu shiryuwa bane ya rabbi mun kawo ƙarar su gareka ka fimu sanin yanda zakai mana da su.. Ya rabbi ka gafarta mana baki ɗaya. Ka ɗaukaka ayyukanmu da rahamarka.🙏😭✍️.

*_ALHAMDULLAHI!!_*

    Ya rabbi Nagode maka daka bani ikon kammala wannan ɗan littafi nawa. Kuskuren da nayi a ciki rabbi ka yafe mini ni da masu karantawa.🙏

Duk wanda na ɓatamawa a yayin rubuta wannan labari ya yafe Mani. Nima na yafema kowa.🙏

Ina sake tallata muku littatafan ZAFAFA BIYAR dake shirin zuwa muku da wani sabon salo na musamman masoya. Dan tafiyar wannan shekarar fa tanada banbanci da saura matuƙar banbanci. Soyayya ce za'a shata kwarya-ƙwarya😋 babu algus. A fanin ilimin ma mun tanada muku romo mai yawa. Hakama faɗakarwar munzo da sabon tanadi. Kai cakwakiyar ma fa da zamantakewar rayuwa duk ba'a barmu a baya ba. Kudai kawai ku kasance da zafafan biyar ɗin nan naku domin samun nishaɗi fiye da yanda aka saba.😁👍👌

Masha ALLAH sai mun haɗu a ZAFAFA BIYAR dan suna nan shirye tsaff da zafinsu. Kuma gab suke da zuwa gareku in sha ALLAHU suma😁🙏

Bilyn Abdull ce🤙.

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
Chapter 82 · 0% Book details