← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 82

Sashe 16

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

.......Ƙarfe ɗaya da mintuna goma sha shida duk wanda ke a massalacin ya shaida ɗaurin auren Dafeeq Abubakar Ja'e da amaryarsa Kainaat Usman akan sadaki naira dubu ɗari biyar. Kasancewar massalacin a anguwar su Kainaat yake gane wanene angon nata ya haddasa ƙananun maganganu a bakunan mutane. Kainaat sananniyace a anguwar tun tana budurwa, duk da mahifinta talakane ta tashi irin yaran nan marasa jin magana da son ƙarya. Za'a iya rasa masarar tuwo a gidansu Kainaat ka ganta da dressing na kusan dubu ɗari biyu a jiki. Gashi bata da mutunci ko kaɗan, dan ko gittawa tai ka gaya mata cuta sai ta dawo ta gaya maka mutuwa. Yanda Kainaat ke fantamawa a cikin dukiya yasa tuni kowa ke mata kallon ƴar iska. Sai dai kuma a baɗini sam ba haka bane. Dan duk rashin jin Kainaat bata aikata zina, amma fa ko kai waye a wayo in har ta ƙwallafa maka sai taci kuɗinka. Zatabi tako wace irin hanya taci saboda shegen wayonta. Kainaat ƙyaƙyƙyawa ce sosai, dan ta kasance buzuwa, sai dai anan Nigeria aka haifeta, dan nan ta tashi taga kanta da iyayenta nan kuma kaɗai ta sani ko Niger da aka san asalin buzaye suke basa zuwa. Ƙawayen Kainaat duk ƴaƴan masu kuɗine, ta kuma samosu ne a yazon bin joint-joint ɗinta. Dan duk inda tasan ƴaƴan manya suke nan ne wajen zuwanta. A wannan kutse-kutsen nata ta tattara ƴaƴan manya suka zama abokanta. Sometimes ma sune ke saya mata sutura, dan in har zasu shiga shopping to itamafa dole a mata. Tayi samari kala daban-daban kama daga kan alhazawan birni har zuwa matasan masu kuɗi dama yaransu, sai dai taci kuɗinsu ta gudu. Da taimakon Nadwa ta koma makaranta, dan ta kammala secondary ɗinta tuni. Nadwa mommy's girl ce. Dan babanta ya jima da rasuwa, kuma mai kuɗine sosai, ita kaɗai ya haifa dan haka ya barsu da tarin dukiya itada mahaifiyarta. Tunda taga Kainaat ALLAH ya ɗaura mata sonta, dan ita mutum ce mai son ƙyaƙyƙyawa. Tare suka fara karatu, daga baya Mommyn Nadwa ta turasu abroad. Da ƙyar baban Kainaat ya yarda, dan sai da Mommyn Nadwa ta lallaɓashi.
Su Kainaat na shekarar ƙarshe a school Abaan yazo yin wani course na wata shida. Tunda Kainaat ta ɗaura idonta a kansa ta haukace. Haka ta addabi Nadwa sai da ta binciko mata shi ɗin ɗan waye. Hankalin ta ya sake tashi jin bama ubansa ba, shi akaran kansa gayyane. Dan matashin mai kuɗine a harkar noman shinkafa da shigo data waje gida Nigeria, ya kuma fitar da ta Nigeria waje. Kai a taƙaice dai shine kankat a harkar shinkafa a Nigeria bama arewa kawai ba. Wannan shine irin mijin da Kainaat ta jima tana burin mallaka, matashi ga kuɗi ga ƙyawu. Uwa uba miskilanci. Dan kallon fuskar Abaan kawai ya isa tabbatar ma da mai hasashenshi shi ba kanwar lasa bane. Duk da jikin Kainaat ya ɗanyi sanyi kaɗan da jin shekarunsu ɗaya na haihuwa, amma da ga baya sai ta ware akan hakan ba komai bane. Kainaat ta fara ƙoƙarin shiga jikin Abaan sai dai ko kallo bata ishesa ba, hasalima an sanar mata shi fa mata basa gabansa sam. Mahaifiyarsa da ƙanwarsa ne kawai taurarinsa a duniya. Jin wannan batu yasa Kainaat shiga ta fita harta jawo hankalin P.A nashi kanta, da taimakonsa ta fara kusanta kanta da Abaan, sai dai nan ɗin ma babu nasara, ganin bazai kulata ba ta canja alƙibla zuwa kan ƙanwarsa da mahaifiyarsa bayan sun dawo gida Nigeria sun bar Abaan acan. Yanda Kainaat ke kwantarma Hajiya Maryam kai yasa ta fara jin sonta a zuciyarta, gata kullum cikin shigar kamala. Noor ce dai ma aka ɗan sha wahala da ita, dan da ƙyar ta fara kula Kainaat saboda faɗan da Hajiya Maryam ke mata. Da taimakon Mommyn Nadwa Kainaat ta sake samun shiga jikin Hajiya Maryam, danta alaƙantata da cewar ɗiyar ƴar uwarta ce. Duk da Hajiya Maryam ba damuwarta dole sai ɗanta yay auren ƙwarya tabi ƙwarya bane sai taji ta amince Abaan ɗinta ya mallaki Kainaat matsayin mata. Dan koba komai ƙyaƙyƙyawace kuma nutsatstsiyar yarinya. (Nace Humm).
Daga ƙarshe dai anyi auren Kainaat da Abaan badan yana sonta ba sai dan biyayya ga mahaifiyarsa. Yayinda komai akayisa a hannun Mommyn Nadwa matsayin itace uwa gareta iyayenta sun rasu. Mahaifiyarta tayi kuka sosai da irin wannan aure, dan tana son ƴarta, amma gashi a dalilin auren mai kuɗi ta kashesu ta ɗauki matar data santa da girmanta. Haka dai aka sha shagalin biki iyayen Kainaat basu da wani power a ciki. Amarya ta tare, sai dai babu kulawa daga miji, hasalima randa aka kaita yabar ƙasar, hakan ya ƙonama Kainaat rai sosai, taci kuka bana wasa ba, sai dai Mommyn Nadwa nata kwantar mata da hankali ta waya. Hakama Hajiya Maryam tasa Abaan ya dawo dole bayan tafiyarsa da kwanaki uku. Anan ɗin ma Abaan bai niyyar shiga sabgarta ba, amma babu wanda yasan yanda akayi kwanakinsa biyu da dawowa yakai kansa gareta har ma ya angwance a wannan dare. Samunta da budurcinta ne abu na farko daya kankaro mata mutuncinta a wajensa, duk da kuwa asiri na cinsa, dan kai kansa da yay gareta kam tabbas magani yaci a cikin abinci. A watan da Kainaat taje bata tsallake na ciki ya bayyana, kowa murna yake tsakanin Abaan da mahaifiyarsa da Ƙanwarsa. Tattalinta sukeyi kamar ƙwai, dan ko motsi tai sai ance mike damunta. Wannan al'amari yayma Kainaat daɗi, sai ta dinga langaɓe musu kuwa fiye da jin jiki na laulayi suko suna rawar jiki. A haka ALLAH yakai ciki watan haihuwa, ta ko haifo ɗanta namiji mai kama da ubansa sak. Farin cikin wannan family bama zai misaltu ba. Amma abin baƙin ciki mahaifiyarta da ƴan uwanta da mahaifinta sai zuwa sukai dubata a matsayin wai dangin babanta ne dake Niger, Mommyn Nadwa itace komai. Ranar ma mamanta sai da tai kukan baƙin ciki, yayinda ƴan uwanta sukai alkawarin bazasu sake raɓarta ba, dan yanda ta amshesu a wulaƙance ya ƙona musu zuciya sosai. Suna baro gidanta suka tattara kayansu dama gidan da suke gidan haya ne sukai tafiyarsu Niger. Wannan shine silar rabuwarta da iyayenta da ƴan uwanta, har yanzu bata kuma nemesu ba suma basu sake memanta ba.
Ranar suna an zubar da kudi na tashin hankali, yayinda yaro yaci sunan Kakansa wato mahaifin Abaan da ALLAH yayma rasuwa tuni. A wannan ranar ne Abaan yayma Kainaat ƙyautar companyn nan, tare da maƙudan kuɗi daga mahaifiyarsa, ƙanwarsa Noor ma ba'a barta a baya ba ta siya mata danƙareriyar mota duk da kuwa Kainaat ɗin nada har guda biyu na lefe da aka saka mata da wadda Abaan ya bata matsayin tukuycin kai masa budurci. Ansha shagali an kuma samu dukiya sosai daga abokan arziƙi, dan kwarai da gaske yaro yayi goshi, Kainaat na alfahari da haihuwarsa. An fara rainon yaro matsayin ɗan gata, sai dai kuma ashe bamai zama bane, dan watansa ɗaya da kwanaki a duniya ya rasu sakamakon mura da dama aka haifesa da shi, dan Abaan nama shirin suje suga likita ne a waje ashe babu rabo.
Kuka na tashin hankali Kainaat ta dingayi, dan kuwa dai taga samu taga rashi, harta fara alfaharin dukiya ta zama tata ta gida gaba ɗaya. Abaan da Mamah suka koma lallashinta ita da Noor, dan kuka suke sosai. Ansha fama Kainaat harda kwanciya asibiti kamar ba mutuwar ƙaramin yaro ba, da ƙyar ta dawo hankalinta.....

___________★
Chapter 16 · 0% Book details