← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 82

Sashe 48

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

      _🥱🥱Gaskiya zanci ganda irin mai yajin nan da romo da ake cema ragadada sanda muna yara😩. (🚴🚴🚴Kai jama'a Bily da son girma, irin mu mun girma ɗin nan yanzu fa ko🤣 wai sanda muna yara🤣)._

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Ashirin da bakwai_

__________________

*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥

*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_

*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*

*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*

*TSUTSAR NAMA Billynabdul*

*GUDUN K'ADDARA Huguma*

*AMEENATU Mamuhghee*

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

_______________

.......Jin kamar mutum a gefenta da azababben ƙamshin daya gama ɗaure motar ya sata juyawa gefenta kamar a ɗan razane. Wani irin bugawa ƙirjinta yay da ƙarfi har tana ƴar zabura. Sai kuma duk ta daburce cikin lalube take son kama handle ɗin ƙofar amma tama kasa sai dibi-dibi take. Yanda take yi ɗin harga ALLAH ya bashi dariya, dan sai yi take kamar makauniya na laluben hanya. A hankali ya saki wani ɗan gajeren murmushi batare da ya daina abinda yake a laptop ɗin saman cinyarsa ba ya furta, “Awwal muje”.
Murmushi shima Awwal ya saki cikin ƙunshe dariya. Harga ALLAH yana a cikin matukar farin ciki da yanda al'amarin nan ya kasance haka. Dan jin komai yake ma kamar wani mafarki ko almara gaskiya. To amma ikon ALLAH yafi gaban komai ai. Fara tafiyar motar ya saka Khadijah jin kamar ta fasa kuka. Idanunta cike da ƙwalla ta sake kallonsa a karo na biyu. “Dan ALLAH ku sauke ni zan koma ciki nayi mantuwa”.
Kusan mintuna biyu kamar bazaice komai ba, ga Awwal kuma baida alamar tsayawa. Itako jikinta sai wani tsuma yake zuciyarta na duka kamar zata fito waje.
“Wannan shine gaisuwa?”. Ya furta cikin sassanayar muryarsa mai cike da kamala da dattako batare da ya ɗauke idanunsa a laptop ɗin ba. Gaba ɗaya sai kunya ta lulluɓe Khadijah. Cikin sanyin jiki da jin bata ƙyautaba ta sake ƙasa da kanta. Ai koba komai basu cancanci haka a gareta ba kodan alkairin da suka taɓa mata a rayuwa, dan tun ganin Awwal shima yayan nasa ta ganesa. “Ina yinin ku”. Ta faɗa muryata na ɗan rawar jin kunya. Murmushi ya sake saki mai sanyi hankalinsa dai na ga aikinsa. Shiru bai amsa mata ba har tsawon wasu sakanni, kafin ya rufe laptop ɗin ya ɗago yana mai juyowa gareta. “Mi kika manta acan ɗin?” ya faɗa maimakon amsa mata gaisuwa.
A hankali ta ce, “Abu ne!”
Shima a hankalin ya furta, “Bashi da suna?”.
Shiru ta gagara amsawa. Sai ya zubama yatsun hannunta da taketa faman cuɗawa ido, yanda ƙunshin yama hannun nata ƙyau a take yaji wani iri a ransa. Idanunsa ya kauda da sauri yana jan numfashi. Laptop ɗinsa ya sake buɗewa a can ƙasan maƙoshi yana furta, “Ki faɗi ko miye kika manta ɗin, in har ana saida shi za'a saya miki shi”.
Yanzu kam jitai kamar ta tsilga a motar ma kawai ta hutama. Jikinta har wani yamm-yamm yake saboda yanda sautin muryarsa ke wani ratsa mata zuciya. Ga ƙamshin turarensa yay masifar addabarta kamar yanda shima nata ke matuƙar masa daɗi da sakashi a wani yanayi. Jin tai shiru ya sashi ɗan ɗagowa ya kalleta, sosai ta takure jikinta a jikin murfin. Kamar ance ta juyo itama karaf suka haɗa ido. Da sauri ta sake maida kanta. Murmushi kawai ya saki ya ɗauke nasa kan shima. Daga haka babu wanda ya sake cewa komai sai shi da kan amsa waya lokaci-lokaci yana ta aiki a laptop har suka iso ƙofar gidan su Khadijah. Kafin ma Awwal ya gama kashe motar harta buɗe ta fita ita, “Nagode sosai, ALLAH ya saka da alkairi” ta faɗa dai-dai lokacin da take ƙoƙarin rufe motar. Shi dai kallonta kawai yake dan ya fahimci burinta kawai tabar wajen ne, kafin kace mi ko harta faɗa gida cikin sassarfa da harɗewar ƙafafu. Kansa ya ɗan girgiza da sakin guntun murmushi kawai ya maida kansa ga laptop ɗin yana faɗin, “Awwal muje”.
Cikin girmamawa Awwal dake ta jin daɗi kamar ya taka rawa ya ce, “To Yaya”.
Wata ajiyar zuciya mai ƙarfi Khadijah dake jikin ƙofar soron tana leƙensu ta saki tana mai dafe ƙirjinta. Tama rasa wane kalar tunani zatayi akan al'amarin. Kenan mutumin nan daya taimaketa a randa ta baro Adamawa nada alaƙa da mazajen su Zuhrah. UBANGIJI kenan mai hikima. Ita tamayi zaton bazata sake ganinsu ba a rayuwarta har abada. Ashe akwai alaƙa a tsakani duk da dai bamai ƙarfi bace ba... Fara isowar motocin da suka kwaso ƴan dinner ya sata barin soron ta ƙarasa shiga cikin gidan itama...

Tunda ƴan dinner suka dawo aketa labarin abinda ya faru a hall ɗin yau akan Khadijah da ogan anguna Abaan da kuma matashin saurayi mai suna Yassar. Kowa da yanda yake fassara al'amarin da kuma fatan da yake yi akai. Ita dai Khadijah ko kanzil batace ma kowa ba, ta kuma ji daɗin yanda babu wanda ma yasan ogan angunan ne ya kawota har gida. Bayan sun wuce gidan makwafciyarsu da zasu kwana Ni'ima ke cemata itafa sai taga kamar mutumin nan shine suka kawota ɗin nan dan Awwal bai ɓace mata ba. Shiru Khadijah tai mata taƙi ta tanka, dole Ni'imar ta ƙyaleta itama dai dan tasan halin auntyn nasu in bataso asan abu ba.....

_______________★
Chapter 48 · 0% Book details