← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 82

Sashe 54

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

......Kurɓarta kusan uku ta fara jin yunƙurin amai. Ita dama zazzaɓinta kenan. Bata son abinci, dan ko an takurata taci zata iya amansa. Da sauri ya amshe mug ɗin tare da riƙota. A bazata, matuƙar bazata ta jita a jikinsa hannunsa saman bayanta yana shafa mata kamar yanda akanma yara idan ana son lallashinsu. Wani irin yuuu ta sake ji saboda tasowar aman da shaƙar ƙamshin turarensa. Jikinta taja da sauri tana toshe bakinta da hannu, kafin ma yay wani yinƙuri ta dire ƙasa. Ƙofar da ta gani a falon kawai ta nufa da gudu fatanta kawai ace bayi ne a wajen. Takoyi sa'ar hakan, dan kuwa ƙaramin toilet ne dake tsaf-tsaf yana ƙamshi alamar ana kula da shi yanda ya kamata. Bama wani aman kirki tayi ba saboda babu komai a cikin nata sai shayin nan da ɗan malt.. da Gwaggo Safina ta matsa mata tasha sanda suka iso. Yanda take yunƙurin aman ya haddasa mata rashin ƙwarin jiki. Daga duƙen da take ta dinga jin kamar juwa zata kwasheta, baya tai da nufin jingina da bango taji an riƙota. Bata da zaɓin daya wuce kwantar da kanta a ƙirjinsa tana sauke numfashi guda-guda.
A hankali cikin nuna damuwa da yanayin nata ya furta, “Sannu! Kin gama”.
Kanta ta ɗan ɗaga masa tana lumshe idanunta. Sosai jikinta ya sake ɗaukar zafi. Taimaka mata yay ta wanke bakinta, a bazata kawai taji ya ɗauketa gaba ɗayanta. Idanunta ta waro sosai, sai kuma ta maidasu da sauri ta rumtse sakamakon haɗa ido da sukai da shi. Bata sake gigin buɗe idonta ba sai da taji ya direta akan wani lallausan abu, ga sanyi da wani irin ƙamshi mai shegen daɗi na ratsata. Kaɗan ta buɗe idon tana dunƙule jikinta waje guda. Gado ne babba da yaji shimfiɗu na alfarma, sai dai rashin yawaitar hasken ɗakin yasa bata iya tantance sauran abinda ke cikinsa ba. Dan shi kansa ba wani ganinsa take sosai ba da ƙyau. Jin ya yafa mata ƙaton blanket ɗin gadon mai shegen laushi ta sauke ajiyar zuciyar da har sai da yaji sautin hakan. Baice komai ba yaje ya kashe ac ɗin gaba ɗaya. Wani ƙaramin freight dake a ɗakin ya nufa. Madara ya ɗako mara sanyi sosai da ruwa ya dawo bakin gadon ya ajiye, sai kuma ya sake fita a ɗakin babu jimawa sai gashi ya dawo da tarkacen maganin da doctor ya bada da allura da zai mata da kansa dan ya iya. Zama yay a bakin gadon saitin cikinta har tana iya jin kamar ya jingina da jikinta kaɗan, dan haka ta sake ɗan takurewa waje guda a cikin bargon. Allurar ya haɗa sannan ya yaye bargon batare da yayi magana ba ya ɗaga farar rigar ƙasan ta fulanin dake sama kaɗan, ya kuma zama zanin shima. Wani irin dukan uku-uku zuciyarta keyi amma ta dake da son tabbatar da abinda zai yi. Jin shigar allura jikinta yasata rumtse ido sosai, dan akwai ɗan zafi kaɗan. Shi da kansa ya murza mata wajen dan haka ta kasa buɗe idanunta har ya ɗagota ya zaunar. Madarar nan ya saka mata a baki cikin lallashi ya ce, “Daure kisha kaɗan sai kisha maganin”. Sam bata so, amma girmansa da yanda ya cika mata ido ya hanata iya masa musu. Haka ta daure ta ɗan sha kusan kwata ɗin robar sannan ta kauda kanta. Baice mata komaiba ya ajiye ya bata maganin. Tana gama sha kanta a ƙasa muryarta na rawa ta ce, “Bara na koma can kar su Gwaggo suga na daɗe”.
Idanu ya ɗan zuba mata kamar bazaice komai ba, har sai da ta tsargu ta ɗago ta kallesa. Maidawa tai da sauri cikin dabircewa. Ɗauke nasa shima yay tare da miƙewa ya kauda kayan maganin daga gaban gadon sannan ya dawo inda take. Batare da yayi magana ba ya kamata ya kwantar a hankali, blanket ɗin yaja ya rufa mata zuwa ƙirji, sai kuma ya ɗan zuba ma fuskarta datai takwaf-takwaf kamar zatayi kuka ido. Kamar mai raɗa ya furta, “Miyasa baki son nan ɗin?”.
Kamar mai jira da rawar murya tai saurin faɗin, “Su Gwaggo duk suna nan fa. Kuma ance musu kawai zanga doctor ne na koma kaga babu daɗi suji shiru ko?”.
Yanda ta ƙare maganar cikin sigar tambaya ya sashi sakin ɗan murmushi, sai kuma ya saki bargon dake cikin hannunsa har yanzu ya ɗan shafo black beauty face ɗinta mai santsi da laushi. Rumtse idanunta tai da sauri tsigar jikinta na wani irin tashi. Hannunsa na akan fuskar batare da ya janye ba ya ɗan ƙara duƙowa kanta sosai har tana iya jin saukar numfashinsa a fuskar tata. “Su Gwaggo bazasu taɓa jin rashin daɗi ba sai dai ma suji farin cikin kwananki a nan tare da mijinki, in dai nine ki kwantar da hankalinki zan baki isashen lokaci na hutawa, sai dai ba hakan na nufin bazan iya canja shawara ba okay”. Ya ƙare maganar da ɗan bubbuga kumatunta kaɗan ya miƙe daga ranƙwafar da yay a kanta.
Da kallo ta bisa zuciyarta na wani kalar tsitstsinkewa, sam tama kasa fahimtar kalamansa na ƙarshe balle gane ina suka dosa. Bayi ya shiga, babu jimawa sosai sai gashi ya fito. Ya shimfiɗa sallaya tare da daidaita tsaiwarsa ya kabbara salla. Ajiyar zuciya ta ɗan saki kaɗan tana gyara kwanciyarta, a haka barcin dake rinjayar idanunta yaci galaba a kanta. Can cikin barci sama-sama taji hawowarsa gadon, bargon ya gyara ya shiga, tana ɗan jiyosa sama-sama yana addu'ar barci, harya kammala ya shafa mata itama sannan ya kwanta a gefe yabar ƴar tazara a tsakaninsu. Daga haka bata sake jin motsinsa ba barci mai nauyi yay sake sureta.....

_____________★
Chapter 54 · 0% Book details