Sashe 19
Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tuni anguwar su JJ ta ɗauki ɗumi akan abinda ya faru daren jiya. Dan su baba da wanda suka bisu gulma da ƙyar suka sami kansu a safiyar yau. Masu baƙin surutu suka kasa haƙuri suka shiga bada labari. Kowa jinjina al'amarin yake da mamakin mi JJ ya aikata haka shi kuwa da zafi? Babu mai basu amsar nan sai JJ ɗin, shi kuma yana kwance babu lafiya. Dan mafi yawansu ana idar da sallar asuba mazan anguwa da sama suka shiga gaisheshi kamar yanda al'adar anguwar take. In dai baka da lafiya aka kuma sani to maza kan shiga dubaka bayan kowacce salla daga massalaci.
Duk wanda ya shiga yakan samu JJ na kuka da ihun jikinsa naci da wuta. A taimakesa a zuba masa ruwan sanyi kada ya ƙone. A zahiri kam babu wani abinda ke faruwa da shi. Hankalin ahalinsa gaba ɗaya ya ƙara tashi, a take yara da manya suka taru a kansa ana masa addu'a. Da ƙyar aka samu kansa kusan sha ɗaya na safe. Yay shiru sai wani irin mugun zufa da yake yi dan cikin duk bayan mintuna ashirin yakam jiƙe abinda aka shimfiɗa masa kamar wanda aka watsama ruwa, sai an ɗauke an canja da wani. Yayi wata irin muguwar rama ta tashin hankali jikinsa yayi baƙi sosai duk da kuwa JJ fari ne sol da shi. Tuni ƙyawun fuskar nan tashi ta gushe, baƙin sajen nan dake ɗaukar hankalin ƴammata kamar ma ya fara furfurar wahala. Baka iya hangen komai a tattare da JJ sai ƙwala-ƙwalan idanu da haƙora tamkar dillalin aljanu. Baba dake share hawaye cikin kasa daurewa ya ce, “Jazool mika jawoma kanka haka ne da zafi? Mika aikata ne da har muma yake neman shafarmu? Jibeka dan ALLAH cikin kwanaki uku kacal halittarka ta canja gaba ɗaya. Jazool ka faɗa mana mika aikatama bayin ALLAHn nan? Wacece Anoosha? Miye haɗinka da ita da ka shiga irin wannan bala'i a dalilinta ne?”.
Duk da azabar dake ratsa JJ da wahalar ciwo a firgice ya kalli Baba jin ya ambaci sunan Anoosh. Yaya Inusa ne ya karɓe da faɗin, “Ba kallonsa zakai ba Jazool, ka sanar mana wacece Anoosh? Kamar yanda baba ya buƙata. Minene haɗinka da ita? Dan bayin ALLAHn nan sun tabbatar mana da har sai ka sanar mana wacece Anoosh sannan zasu bada matarka. Dan ALLAH ka sanar mana ko muma ƴan uwanka zamu sami nutsuwar zukata da kwanciyar hankali. Jiba kaga Baba ko taka ƙafarsa baya iya yi saboda wahalar da mukasha tsakanin safiyar jiya zuwa yammaci. Jibi fuskar Mujetapha yanda ya kwaye kumatu saboda gudun ceton rai. Kalleni kaga raunuka biyu naji a tsakanin hannu da gefen cikina duk a dalilin gudun kuɓuta daga gidanka. Dolene akwai abinda ka aikata Jazool, in ba hakaba miyyasa saboda kai duk zamu shiga bala'in nan. Hatta su baba liman basu tsira ba suna gidajensu suna jiyyar kansu. Mazan anguwar da gidanka yake ɗai-ɗaine jiya basuyi fitsari a wando ba banda tashin hankalin da idanunmu ya gani. Jazool wacece Anoosh! Mika aikata mata ne!!”. Yaya Inusa ya faɗa cikin ƙaraji da kaushin murya jikinsa har yana rawa. Shima JJ ɗin rawa jikinsa ya farayi yana mai kallon duk wanda ke ɗakin. A ƙufule Yaya Mujee ya amshe da faɗin, “Garama ka faɗa Jazool, kai dolene ma saika faɗa mana mika aikata. Dan tace idan ma ka ɓoye wani abu tana anan tare damu dan akoda yaushe tana kusa da kai. Ya rage naka ka faɗa da arziƙi koka faɗa da wahala. Dan kaga dai yanda ka koma a cikin kwana uku kacal tamkar wani dilallin aljanu. Har muma ana neman sabauta mana rayuwa a dalilinka”.
Wasu irin hawayene masu zafi suka shiga ziraroma JJ a idanu. Tamkar wanda ake controlling murya na rawa ya ce, “Anoosh budurwata ce. Mun haɗu a ranar babbar salla ta shekarar 2020 da ƙarfe huɗu da rabi na yamma. Dan fitowarmu da ga salla kenan ni da su MB a anguwar su Gwaggonsa da mukaje gaidawa.......”✍️
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na goma sha biyu_
..........Tafe take cikin nutsuwarta tamkar wadda ke tsoron taka ƙasar. Hijjab ne a jikinta har ƙasa fari tas. Idanunta da siririn farin gilashi da kasancewarsa bai hana bayyanar ƙyawun idanunta da girmansu ba gamai kallo. Sam bata da alamar hayaniya akan fuska, sannan da ga ganinta kasan bata da yawan magana akwai kuma kunya da tarbiyya tattare da ita.
“Woow! Ya arrahaman kaga wata halitta!”. SJ ya faɗa. Da ga JJ har MB ɗagowa sukai suka kallesa. Dan su hankulansu nakan wayar JJ ne suna kallon hotunan da suka ɗauka a wajen idi. Maimakon magana ita ya nuna musu da yatsa, dan harta gotasu kaɗan. Su dukansu babu wanda zuciyarsa bata harba ba, sai dai kafin su farga har JJ ya zabura zumutt, tamkar ƙyaftawar ido sai gashi a gabanta.
“Assalamu alaikum ƙyaƙyƙyawa”. Ya faɗa cikin wani irin murya mai taushi da amo. Ko kallonsa batai ba, sai dai ta motsa jajayen ƙananun laɓɓanta da babu komai a kansu sai lips gloss alamar amsa masa sallamarsa batare da yaji sautin muryarta ba. Rabashi tai ta wuce, kafin ya zabura ta buɗe wani farin gate dake gab da su ta shige abinta. Kansa ya dafe cike da takaicin kansa da kansa. Yayinda MB da SJ ke faman masa dariyar ƙeta. Yana tsaye a wajen suka ƙaraso suna cigaba da dariyarsu. SJ ya ce, “Tuku-tuku mugun icce! daga ganin sarkin fawa sai miya tai zaƙi. Banda ma cin amanar abota nifa na fara ganin yarinyar nan amma ka zabura kamar wani kafilfilo kazo kamun yankan baya. To sai ka kama kanka ai dan wannan fa ba irin motocin titi bace ba”.
Harararsa JJ ya ɗan yi, batare da yace komai ba yaja guntun tsaki ya barsu wajen. Inda motarsu ke ajiye ya dawo, ya jingina cike da damuwa yana mai lumshe idanunsa. Sake biyosa su MB sukai nan ma suna dariya, har sai da ya ƙufula ya shige mota. Ganin zai tada suka shige suma, dan kaɗan daga aikinsa ya tafi ya barsu a wajen duk da kuwa motar tasu ce su uku, dan tare suka haɗa kuɗu suka saya dan kawai burge ƴammata.
A hankali JJ ke murza steering fuskar yarinyar na masa waiwayi a cikin idanu, ko sau ɗaya ya gagara saka baki a zancen su MB har sai da yaji SJ ya ce, “Ai inaga fa Gwaggo Ladi na mutunci da mutanen gidan, dan ina ƙyautata zaton ko abincin data bamu take faɗin daga maƙotan can natane masu farin gate to daga gidanne kuwa”.
ƙuwww!! Kake ji JJ ya taka birki. Har sai da sukai gaba su duka suka bigi jikin motar. MB dake baya ya dafe goshinsa yana murzawa a hasale ya ce, “JJ halan kana hauka ne nikam? Yanzu dan ALLAH saboda mace kake neman kashemu a ranar salla”. Shima dai SJ masifar ya balbalesa da shi, amma a mamakinsu ko'a jikin JJ, sai ma ƙoƙarin gangarawa gefen titi da yay saboda yanda ake masa horn ya tsarema mutane hanya.
“Wai lafiya kake kuwa?”. MJ ya sake tambaya a ƙufule. Kai JJ ya girgiza musu a karo na farko. Muryarsa na ɗan rawa ya ce, “Gidan Gwaggo zamu koma dan ALLAH”.
Kallon juna MB da SJ sukayi. Sai kuma suka kwashe da dariyar shaƙiyanci. JJ bai damu ba, da kuma kafiya-lafiyane masifa zai fara musu. Suna ji suna gani ya karya kan mota suka koma gidan Gwaggo Ladi. Shi ya fara fita a motar ya nufi gidan, dan ba baƙonsu bane ba kasancewar sun saba zuwa duk salla. Wani irin zuzuzu JJ yaji sakamakon yin tozali da yarinyar nan zaune a tsakar gidan Gwaggo tana cin abinci. Fuskarta ƙawace da wani irin murmushi da ya sake fiddo ƙyawunta.
“Jazool kunyi mantuwa ne?”.
Gwaggo data farga da shi ta faɗa. Cikin sauri yarinyar ta ɗago kanta, dan sam ita ba ƙofa take kallo ba. Idanu ta waro, sai kuma ta fisgi hijjab ɗinta dake saman jarkar ruwa a gefe ta shiga kiciniyar sakawa. A dai-dai nan su MB suka shigo suna dariya. Suma turus sukai da ganin yarinyar, sai kuma suka wayance tare da kamo hannun JJ da yay sumar tsaye baima amsama Gwaggo Ladi tambayarta ba. Shigewar yarinyar falon Gwaggo ya Bama SJ damar matsawa kusa da Gwaggo yana ƴar dariya. “Gwaggo ɗanki fa yay gamo, dan yarinyar nan fa ta dawo damu”.
Da mamaki Gwaggo Ladi ta dubi hanyar falonta, sai kuma ta juyo ta kalla Sj. “Wai Anoosh?!”.
“Wannan dai data shiga falonki yanzu. In dai sunanta kenan to ita”. Tsaff ya kwashe komai ya sanarma Gwaggo. Murmushi Gwaggo keyi tana kallon JJ. Sai kuma ta kamo hannunsa ta zaunar kusa da ita. “Kaga kwantar da hankalinka Jazool. In dai Anoosh ce da yardar ALLAH ka samu kuwa. Na kuma tayaka murna dan yarinya ce mai tarbiyya da hankali. Sai dai bebiya ce dan bata magana amma tana ji. Tana kuma iya baka amsar da zaka iya fahimta ta motsin laɓɓanta. Zanfi kowa farin ciki da wannan al'amarin kuwa”.
Ba JJ ba hatta su MB kallon Gwaggo suke jin wai Anoosh bebiya ce. Sai dai a cikinsu babu wanda yace komai. Gwaggo da bata lura da yanayin nasu ba ta ɗaga baki ta kira Anoosh dake cikin falo. Kusan mintinan biyu sai gata ta fito tana rabe-raɓe. Fuskar Gwaggo da murmushi ta nuna mata su JJ. “Anoosh waɗan nan ƴaƴana ne, sun zo min gaisuwar salla ne”.
Jin jina kai Anoosh da idanunta ke ƙasa cikin gilashi tayi, sai kuma ta motsa ƙyawawan lips ɗinta a hankali alamar gaisuwa a garesu. Gwaggo ce ta sanar dasu tana gaishesu, cikin rawar lips suka amsa su duka, JJ kam yama kasa sai kallonta da yake kamar idanunsa zasu zubo ƙasa......
____________★