Sashe 25
Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Komai nada mafari, wannan rana itace mafari tsakanin Anoosh da JJ. Dan kuwa washe gari ma dazai kaita makaranta haka ya sakata ta cire hijjab bayan ta shiga mota, zuciyarta bata son abin, amma kuma bata so ta ɓata masa rai saboda soyayyar da take ji tana masa. Tana masa wani irin mahaukacin so da take jin komi yace tayi dai-dai ne, duk da kuwa ita tasan ba dai-dai ɗin bane. Da zai ɗakkota ma hakance ta kasance. Wasa-wasa sai ta ɗan fara samun nutsuwa ganin har kusan sati biyu iyakarsa kawai yace ta cire hijjab ɗin ne idan zai kaita makaranta ko idan zasu dawo. Sai da suka cika sati na uku a haka ranar wata alhamis yake tambayarta miyyasa bata son saka ƙananun kaya ne?. Murmushi kawai tai batace da shi komai ba, kanta a ƙasa. Cike da makirci da yaudara irin ta azzalumai ya sake kwantar da murya. “My Anoosh ina bala'in son naga mace tasa ƙananun kaya, musamman ma ke da nasan zasu fi miki ƙyau fiye da kowacce mace a duniya, dan kinfi mata dubu bisa dubu ƙyau. Irinku fa nada wahalar samu Anoosh. Please ki koya sakawa kafin auren mu dan ina so sosai. Idan kuma kinfi son na dinga kallon matan titi dake sakawa to?”.
Da sauri ta girgiza masa kanta idanunta dake cikin glasses na cikowa da ƙwalla. Cikin alamar motsin lips ɗinta ta ce, “Ai Mommy bazata bari ba. Ko'a cikin gida na saka hijjab nake sakawa ko abaya”.
Murmushi ya saki cikin kannewa ya ce, “Ai hakan ba damuwa bane my Anoosh, idan kika sanya nima basai ki ɗora abaya ɗin ba kisa kuma hijjab. Kinga Mom bazata taɓa ta gane ba ai ko? Ko baki son farantama mijinki rai ne? Kinfi son yana kallon matan dake yawo a titi?”.
Kanta ta sake girgiza masa da sauri. Ya sakar mata murmushi yana riƙo hannunta a karo na farko. Duk da ya ga zaburar da tai da tsumar da jikinta keyi haka ya basar ya kai hannun bakinsa ya sumbata. Gaba ɗaya Anoosh ta gama daburcewa, sai dai ta kasa cemasa komai. Bayan ya sauketa har kuka tayi a aji cikin hijjab. Sam bata son abinda JJ ke mata amma ta kasa hanashi, ta kuma kasa faɗama wani. To wama zata faɗamawa? Ita ba ƙanwaba ba yaya ba, ba ƙawa ba. Sannan bazata iya tunkarar Mommy da wannan batunba ai, tasan zata iya halakata ma, kai ko Gwaggo bazata iya faɗawa ba.
_(Iyaye! Iyaye! Iyaye mu kula Please and please. Nasan wayonka ko dabaranka bashi zai kare maka yaranka ba. Amma mu daure, mu rage sabgogin gabanmu wajen jan ƴaƴanmu a jiki musamman ma ƴammata. Mu zama ƙawayen ƴaƴanmu ta yanda bazasu taɓa yarda da wata Aminiya ba a waje sai mu, balle har suji shakka ko tsoron tunkararmu da matsalolinsu. Jan yaranmu jikinmu kansa muyi saurin fahimtar sabon yanayi da suka tsinta kansu a ciki. Dan irin yaran nan da samari kan yaudara zakaga a farkon fara koya musu abubuwa ko sakasu yin wani abu suna cikin tsoron da idan uwa mai lurace zata iya fahimta. Sannan mu daina bama samarin ƴaƴanmu amanar yaranmu hundred percent, hakan kuskure ne wlhy, dan kawai muna son yarinyarmu ta samu mijin aure, ko kuma kada ya kuɓuce sai mu ɗauki dukkan yarda mu basa. Abinda fa muka kasa fahimta mafi yawan irinsu JJ da fuskar mutanen ƙwarai suke zuwa ga ƴaƴayenmu bada ainahin fuskarsu ta azzalumai ba. Sannan a matsayinki na uwa ya kamata ki zama maisa ido wajen fahimtar raunin ƴaƴanki akan abu, ko kuma ƙarfin sha'awarta tun daga sanda ta fara balaga, kija abinki a jiki da samun hanyoyin kare mutuncinta inba hakaba wlhy kina nan hankalinki akan neman kuɗin da zaki saya mata kayan kwalliya dana kayan ɗaki wani sakarai zai miki sakkiyar da ba ruwa. Yaranmu na yanzu sunada wayo, dan kafin sukai ko'ina sun san minene ma ake nufi da ɗa namiji da alaƙar dake tsakaninsa da mace, karki sakankance yarinya ce bata san komai ba. Humm ƴar uwa a wannan zamanin babu wannan batun na sakankancewa game da shekaru ko wayon yaro, komai dolancinta ko ƙanƙanta zata iya baki mamaki wlhy. ALLAH ka shiryemu baki ɗaya, ka kare mana yaranmu da ga sharrin fasiƙan maza irin su JJ😩🙏)_
Washe gari kamar yanda JJ ya buƙata haka Anoosh tayi, ta saka ƙananun kaya a ƙasa ta ɗora abaya da hijjab. Tana shiga mota ya sakata ta cire hijjabin da abayar. Tsabar yanda ya rikice baima san ya rungumeta ba. Duk yanda take kiciniyar ƙwacewa bai saketa ba sai da ya samu ƙaramar nutsuwa a haka. Bayan ya saketa ta hau masa kuka, sai ya shiga lallashinta cike da daɗin baki irin na mayaudara. Wai wlhy tsabar rikicewa da ƙyan da tayine. Amma ta yarda da shi shi ko hannun mace bai taɓa riƙewa ba sai a kanta, kuma itace ta ƙarshe. Nan fa ya kanainaye ta da zance harda su wa'azi. Dole ta haƙura, sai dai tunkan suje makaranta ta maida hijjab ɗinta. Daga ranar kuma saita ɗan fara ɗari-ɗari da shi. Ganin damar daya samu zata kufce masa ya sake sabuwar dabara.
Cikin weekend ya zo hira kamar yanda ya saba. Maimakon zama da Anoosh sai ya zauna da mamanta wai su tattauna akan kawo kuɗin aure. Hajiya Lailah taji daɗin wannan zance nashi. Bata ɓoye masa ba ta sanar masa zatama Gwaggo magana cikin dattawan layin nan mutum biyu su amshi kuɗin, dan bazata turashi wajen dangin mahaifin Anoosh ba saboda wasu dalilai da sai nan gaba zata sanar masa. Nunawa yay ai hakan babu komai, da yake shima zuciyarsa akwai tsatsa a ciki. Duk abinda suka tattauna Anoosh najinsu, sai taji ta samu matuƙar nutsuwa da sake jin ƙaunar JJ a ranta.
Kwana biyu dayin wannan magana iyayen JJ suka zo aka zauna. Sun kawo kuɗin gaisuwar farko har dubu ɗari cif, akan a sake basu lokaci suzo da sadaki da komai a saka rana. Ranar Hajiya Lailah ta kasance a cikin matuƙar farin ciki, sai dai abinda bata sani ba shine JJ iyayen ƙarya ya kawo musu, dan hatta su MB abokansa basu san ya cigaba da zuwa wajen Anoosh ba. Sannan Gwaggo alaƙarta da MB ta ɓangaren mahaifiyarsa ne, bata wani san iyayen JJ ba sosai musamman ma maza. Yarda datai da shi kuma yasa bata taɓa kawoma ranta zai aikata wani abu makamancin haka ba, ga shi kullum Hajiya Lailah cikin yabonsa take. Ga soyayyar da Anoosh ke masa. Ita kanta kusan duk juma'a idan ya shigo yakan kawo mata kayan marmari wani lokacin harda sabulai da omo, randa ALLAH ya cidata ma harda kayan shayi da nama. Gashi duk ƙwaƙwƙwafinka baka isa gane ainahin fuskar JJ ba, dan makirin mutum ne da ya iya takunsa, duk wani salo na cimma mace ya sanshi musamman irin su Anoosh salihan yara masu tarbiyya.
Kawo wannan kuɗi ya ƙara sakama Anoosh nutsuwa da JJ ita da mahaifiyarta, dan haka washe gari da yazo kaita makaranta koda ya rungumeta batai masa kuka ba, sai dai ta takure jikinta waje guda. Sai ca yay mata na murnar samuntane fa. Ko ita bata murna sun kusa zama ma'aurata. Cike da kunya tace tanayi. Hannunta ya kama ya sumbata, batare da ya bata damar sake cewa wani abu ba ya tada motar.........✍️
🚶🚶🚶🧑🦯Humm
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na goma sha shida_