← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 82

Sashe 50

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

.......Shiru falon yay kowa ya zubama aunty Kubra idanu dake ma Khadijah guɗa da zazzaga mata turare.
“Aunty gafa amaren nan”. Wata Rumaisa ƙawar Ni'ima ta faɗa tana nuna su Zuhrah. Kai tsaye Aunty Kubra ta bata amsa da “Ai itama amaryar ce”.
Kallon juna aka koma yi, yayinda Zuhrah da Ni'ima suka wani irin miƙewa daga jikin Khadijah a zabure. Khadijah kam kamar wadda ta suma a zaune idanu kawai ta zubama aunty Kubra kamar ta sami hoton bango.
“Aunty Kubra kin san mi kike cewa kuwa? Aunty Khadijah ce amarya?”.
“Kwarai ma kuwa, itama an ɗaura mata aure tare da ku. Ayyyiririrrrriiii!!!!!”. Ta sake sakin ghuɗa akan Khadijah da su Zuhrah gaba ɗaya. Dai-dai nan Inna Zulai ta shigo kiran amaren su duka. Ganin tace harda Khadijah yasa mutane suka fara gaskata zancen aunty Kubra da kowa ke tunanin tsokanar Khadijahn take da farko. Sake dabircewa Khadijah tai dan har tana neman faɗuwa sai da Inna Zulai ta riƙota tana faɗin, “Hankali mana Khadijah”. Bata iya cewa komai ba, sai rawa da jikinta ke cigaba dayi. A haka suka fito ƙofar gidan dake cike da maza ƴan ɗaurin aure. Yawanci duk dangi ne sai ƴan anguwa da abokan Baba. Anguna daga ɗaurin aure sun tafi walimar da suka shiryama kansu, sai anjima kaɗan zasu iso nan wajen saukar Alkur'anin da za'ayi mai haɗe da walima da islamiyyasu Khadijahn ta shirya musu. A ɗakin soro aka shiga dasu, inda Baba ke tare da shiƙiƙan ƴan uwansa harma da kawunai. Bayan an zaunar dasu suka gaishesu, sai dai Khadijah har yanzu da alama bata gama dawowa dai-dai ba. Nasiha kowa ya fara musu mai ratsa jiki, hakan ya sake rikita Khadijah ganin su dukansu kamar ana musu ishara da sabuwar rayuwar da suka shigan, tsabar yanda komai ke mata yawo ji take kamar tacema kawunan nasu itafa banda ita. Sai dai babu damar hakan dole ta nutsu har suka gama faɗansu da nasihar. Kiran sunanta da Kawu Bala yayi ne ya sa gabanta sake faɗuwa. Muryarta har rawa take wajen amsa masa da “Na'am Kawu”.
“Matso nan kusa”.
Matsawa tayi kamar yanda ya buƙata. Sake cemata yay ta ɗago fuskarta, anan ma babu musu tai yanda yace. Dukansu dake ɗakin ya nuna mata, murya a dake ya ce, “Miye matsayinmu a wajenki?”.
Da rawar murya ta ce, “Iyayena”.
“Kin tabbatar da wannan sunan mun cancancesa a gareki?”.
Kanta ta jinjina musu hawaye na silalo mata a kumatu. “Alhamdullah” ya faɗa tare da cigaba da faɗin, “Munji daɗi da kika tabbatar da mu ɗin iyayenki ne. Dan haka a matsayinmu na iyayenki mun ɗaura miki aure kema a yau tare da ƴan uwanki. Kuma insha ALLAHU zakiyi alfahari da hakan da mukai miki. Ba kuma muyi haka dan ƙasƙantar da ke ba ko tauye miki hakki. A'a haka ALLAH ya ƙaddara wannan kuma ikonsa ne da tsarawarsa. Amma muma abin yazo mana ne a bazata. Dan kwata-kwata bai wuce sati biyu da suka shige zancen ya shigo ba, ba kuma muyi tunanin zai zama gaskiya ba sai a kwanakin satin nan da suka gabata. Mun ɓoye miki ne saboda gudun komawa ƴar gidan jiya. Muna fatan zaki kasance ƴa mai biyayya a wannan lokacin, dan in sha ALLAHU sai kinyi alfahari da wannan auren Khadijatul-Kair. ALLAH yay muku albarka. Ya baku zaman lafiya ku da mazajenku da zuri'a mai albarka. Ku zauna lafiya dan ALLAH kodan ku sake kwantarma mahaifinku da hankali kun daiga halin da ya shiga ciki a baya. To yanzu ku ya rage ku sakanka masa da ƙoƙarin sa gareku ta hanyar zama lafiya da mazajen aurenku kamar yanda kuka ga mahaifiyarku tana zaune da shi lafiya kunji. Aita haƙuri kuma, dan shi aure ba zaman nanaye bane da shargalle kamar yanda ku yaran zamani kuke kallo. Auren bautar UBANGIJI ne. Shi kuma bautar ALLAH sai da jajircewa ake yinta da tsafta sannan ai mata kwalliya da haƙuri sai a samu aljanna da ake fata.”
Sosai Khadijah ke ƙoƙarin riƙe kukanta. Harga ALLAH gaba ɗaya ma ta gama ruɗewa da gigicewa. Itafa aka ɗaurama aure a yau. Ya arrahaman ya akai haka ta kasance? Rashin amsa yasata ƙara daurewa, dan tayi alƙawarin a wannan gaɓar, koda mijin nata zai kasance gurgu ne. Makaho ne. Zata zauna dashi kasancewar su iyayenta suka zaɓa mata shi. Kai koda ace ƙazami ne, ko da ace jahili ne. Kai koda ma ace yanada wani mummunan hali in har bazai sakata saɓama UBANGIJI ba, zata zauna da shi. Ta kuma san ma iyayenta bazasu taɓa aura mata wanda zai ɗorata a hanyar zuwa wutar jahannama ba.
Nasiha sosai akai musu a ɗakin har iyayensu mata suma sun shigo suka ɗora nasu kafin a fito dasu saboda kiran sallar la'asar. Cikin gida aka shiga dasu wajen Mama. Kasa daurewa Khadijah tayi ta faɗa jikinta tana hawaye mara sauti. Rungumeta kawai mama tai batace komai ba. Dan harga ALLAH tana tausayin ƴar tata. Amma tana mata fatan alkairi a wannan auren. Suma su Ni'ima jikin Maman suka shige suna kuka. Hakan yasa dangi abokan wasa sukai musu caa da sheri wasu na karesu....

Bayan idar da sallar la'asar duk aka ɗunguma babbar harabar islamiyyar su da za'ayi taron. Komai an gama shiryawa manyan baƙi kuma duk sun iso dama sallar dai ake buƙatar fara gabatarwa sannan. Zaman amare da aka sakema shiga cikin dogayen rigunan abaya farare da adon golden da mintuna kaɗan tawagar anguna ta iso wajen. Nan take wajen ya ƙara cika taf. Sauka aka fara gabatarwa, inda komai ya tafi a cikin tsari da birgewa. Yayinda bakunan anguna ya kasa rufuwa. Sai dai babu wanda yasan wanene angon Khadijah har zuwa yanzu idan ka cire iyayenta maza. Sun sami ƙyaututtuka da suka bada mamaki musamman wanda suka fito da ga ogan abokan ango Abaan Omar Modibbo. Dan kuwa mukullayen motoci har uku ƙanana dai amma masu ƙyau da ɗaukar hankali ya bama amaren su duka ukun dan sun birgesa matuƙa. Bayan wannan ma wasu ƙyaututtukan sun biyo baya dan islamiyyar sun gayyaci manyan mutane sosai, hatta da su Baba Hakimi da suka taso tun daga Adamawa basu wuceba suma sun tsaya domin saukar, kafin a fara gudanar da lectures masu ratsa jiki ga anguna da amare. Har zuwa yanzu bawai Khadijah ta fita a ɗimuwar da take ciki bane ba. Dauriya kawai take da son tilasta kanta zama a dake, amma duk da haka jikinta zazzaɓi ne mai zafi sosai dan tunda suka zauna a wajen ma kanta na a kafaɗar Ni'ima kasancewar duk sanda ya ɗago sai ta kama ogan anguna da ake kira Alhaji Abaan Modibbo na kallonta, sai ta daina ɗagowar har sai da aka kirasu wajen sauka. Suna dawowa bayan an kammala ma dai kwance take shiru a jikin Zuhrah data koma kusa da ita a yanzun. Sauka ta ƙyatar sosai. Ansha hotuna kamar babu gobe. Anan ne ma dai mutane suka fara tsarguwa da hasashen wanda kowa kema kallon angon Khadijah ganin duk sanda za'ai hoto yana a kusa da ita ne, amma kuma basu da tabbas har aka tashi gab da magrib.

Bayan sallar isha'i akai shirin miƙa amare ɗakunansu. Sai dai kuma banda Khadijah. Ayanzu ne fa sukai asalin kukan rabuwa. Dan da ƙyar aka raba su Ni'ima da ga jikin Mama da Khadijah. Da aka kaisu yima Baba sallama ma nan ma ansha ɗan ƙaramin bidiri kafin. Har ƴan kai amarya suka je suka dawo Khadijah na kwance a ɗaki zazzaɓi yay mata rijif. Koda mama ta bata magani ma fakar idonta tai ta ajiye ta koma ta kwanta. Anata sam barka da gidajen amare. Abin farin ciki kuma suna a jere da juna ne komai nasu kuma iri ɗaya kamar wanda suka aura tagwaye. Koda yake Ibrahim da Adams kowa na iya kallonsu da tagwaye saboda shaƙuwarsu da ƙaunar fa sukema juna. To sai muce ALLAH ya sanya alkairi ya kuma basu zaman lafiya mai ɗorewa....

*_WASHE GARI_*
Chapter 50 · 0% Book details