← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 82

Sashe 55

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abin duniya ya gama dabaibaye Kainaat, ta rasa ta inama zata ɓulloma mayen yaron nan daya zame mata akwatin maciji. Tayi haukan, tayi kissar, tayi lalashin amma kamar tana ma ƙaramasa ƙarfi ne. Har sallamarsa tai daga Company aiki amma ya tabbatar mata bata isaba. Idan kuma ta dage to wlhy zai tona mata asiri wajen staffs dinta game da aurensu. Kainaat mace ce mai son girma, sannan tana da son adana sirrinta ga na ƙasa da ita shiyyasa ta kasance mai matuƙar taka tsantsan. Hakan yasa ta janye maganar sallamarsa dan sam bata buƙatar abinda zai zubda mata daraja a wajen staffs nata. Sai dai ta sake kasawa ta tsare akan komai na Companyn ta yanda Dafeeq bazai iya mata suruf bahana ba.
A tare kullum suke zuwa aiki su kuma dawo tare, dan sun adana matsalarsu a iya gidansu batare da wani a gefe ya sani ba idan ka cire Nadwa da Kainaat kan sanar mata domin ta bata shawara. Sai dai ma kamar Dafeeq ɗin na gani har hanji ne, dan duk shawarar da Nadwan ta bata sai ya wargazata. Yauma kamar kullum a tare suka baro office ɗin. Dafeeq ne ke tuƙi ita kuma tana gefensa tana danna sabuwar wayar data saya, tuni ta maido komai nata na waccan tsohuwar wayar dake a hannunsa anan. Ta kuma sami nasarar dawo da kuɗaɗenta na bank da Dafeeq ya kwashe ta hanyar wani ɗan uwan su Nadwa Manager ɗin bank ɗin da kuɗin ke a ciki. Dan sun kai report bisa shawarar Nadwa akan cewar ɓarayine suka sace mata bag. Sa'ar da aka samu shi Dafeeq bai kwashe kuɗin daga account nashi ba. Baifi kwana uku kenan da dawowar kuɗin ba, sunci uban faɗa kuwa dan harda marinta yay ta rama. A yau ne ma suka ɗan shirya har suka nufi office ɗin tare. Dafeeq kuwa ya sakko ne saboda wani shiri da yake ƙullama zuciyarsa, yayinda ita kuma ke faman masa shan ƙamshi.
Kallonta ya ɗan yi yana mai sakin murmushi, sai kuma ya sake damƙe steering da ƙyau tare da maida idonsa ga titi yana faɗin, “Dan ALLAH bamu birgeki ba, jibemu shar damu kamar ka sace ka gudu. Hajjaju mu kauda wannan abubuwan mu zauna lafiya mana Please”.
Shiru kamar Kainaat bazata kulashi ba sai kuma ta ɗan ɗago ta kallesa. Ganin hankalinsa na akan hanya ta maida kanta ga wayarta da faɗin, “Wani abun kake shiryawa kenan?”.
“Oh oh, ke shikenan baza'ai zaman lafiya ba sai ana shirya wani abu. Hajjaju karfa ki manta soyayya ce ta haɗamu, kece kuma kika fara min tayinta, sai da na zurma sosai kike neman mani illa kuma”.
“Oh saboda ni na fara maka tayinta shine ka amsa da manufa?.”
“Ko ɗaya baki canka dai-dai ba. Da zuciya ɗaya na amshi soyayyarki, tunda ke shaidace saboda ke na rabu da matata da nake tsananin so da ƙauna. Idan ma kina faɗin hakane saboda kwashe kuɗinki na banki da takardu ni nayi duk wannan ne saboda gano kece kika aureni da manufar rabuwa da ni bayan cikar kwana bakwai. Haba hajjaju, wane sakaraine zai sami zuƙeƙiyar mace irinki ya saki. Da ace tun farko kin sanrmin auren kisan wuta zakiyi bazamu kai ga wannan matsalar ba, amma kika shirya mun rufa-rufa. Ni kuma shiyyasa na kwashe kuɗi da takardun Companyn danna ɗaureki. Nasan dai suna hannuna bazaki taɓa rabuwar dani ba zaki ce saina baki”.
Tsaff kalamansa suka tsaru akan Kainaat, dan kamar wadda jikinta yay sanyi ta ɗago tana kallonsa. A bazata yaji ta furta “Yanzu a ina kaji wannan zancen haka Dafeeq?”.
Murmushi yayi mai bayyana haƙora, sai kuma ya ɗan kalleta da faɗin, “Zancen duniya ai baya ɓuya Hajjaju. Amma karki damu in dai nine ban ɗauka da zafi ba duk da da farko naji haushi. Amma yanzu na yafe miki. Fatana kawai shine ki janye ƙudirinki nima zan janye nawa harma na baki sauran takardun hannun nawa. Amma zan baki lokaci kiyi tunani dai”.
Kai kawai ta jinjina masa zuciyarta na wani irin rawa kamar zata faɗo. Amma batace da shi komai ba ta fita a motar dan sun riga sunzo gida. Da kallo ya bita yana wani cije lips, sai da ta shige falonsu ya kwashe da dariya yana buga sitiyari da faɗin, “Shegiya zaki gane kuranki tsohuwar guzuma kawai kin sa na rabu da ƙyaƙyƙyawar mamata ƴar shilax, wlhy kika yarda kika faɗa a wannan tarkon nawa kin gama kaɗewa. Khadijah kuwa tana gab da dawowa gareni. Dan wani zan nema ya aureta ya saketa batare da shi da ita sun san plan ɗina ba. Zan saida Companyn naki na ɗauke Dijoh na mu bar ma ƙasar gaba ɗaya”. Ya sake ƙyalkyalewa da dariya harda ƙyaƙyƙyawa na ƙeta..
A falo ya samu Kainaat kwance tana hutun gajiya, ido suka haɗa, a bazata ta sakar masa murmushi. A ranta kuwa faɗi take (shegen kaya kenan, ai nasan wannan kwantar dakan naka na sabon shiri ne. Amma babu komai zanyi amfani da shirin naka na gama da kai cikin sauƙi batare da ka kawo min wata tangarɗa ba. Kafin ka farga ka dawo tafin hannun Kainaat. Zan tabbatar maka ni da kai CUTA CE TA ƊAU CUTA... shegen yaro mai wayo kamar ɗan dila).
Martanin murmushin ya mayar mata, tare da takawa a hankali inda take ya zauna. Ɗagota yay ya rungume a jikinsa. Hakan yasa itama rungumesan suka saki ajiyar zuciya a tare. Daga haka labarin ya fara canja salo. Duk da Kainaat taso dojewa daga baya ya hanata kowacce irin dama.. Sai da ya tabbatar ya samu abinda yake so sannan ya barta yana dariyar ƙeta. Danne zuciyarta kawai tai tana biye masa da murmushin fatar baki, a haka sukai wanka tare, sannan suka dawo ƙasa ta dafa musu noodles sukaci a tare. Bayan sun gama falo suka sake komawa suka kunna kallo, tana zaune shi kuma yana kwance yay filo da cinyarta. Lokaci-lokaci sukan kalli juna su saki murmushi, a ƙasan rai kuma kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa, dan su duka babu wanda hankalinsa ke akan kallon..
Dafeeq ne ya katse shirun da faɗin, “Bakice komai ba Baby. Dan ALLAH ki ajiye makamanki mu zauna lafiya mu rungumi junanmu. Na tabbatar miki zan koma miki fiye da bawa a gidan nan”.
“Humm Dafeeq ina tsoron na sallama ne kaci amanata”.
“Babu wannan maganar ki yarda dani”.
Ɗan jimmm tayi kamar mai nazari, sai kuma zuwa can ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Okay shike nan na amince. Amma zamuyi komai a rubuce ka yarda”.
“In dai nine baki da matsala dani a yanzu. Tunda kin san gidanmu, kin san iyayena, mi kuma ya rage to”.
Cike da gamsuwa ta ce, “Hakane”........✍️

_Ni dai nace Humm😂. Kufa masu karatu kuna da abin faɗa?🥱._

_________

Ina kuke manyan mata da hajiyoyi munsamar muku sauqi Ina masu shaawar futa Egypt karatu ko yawan bude ido to gadama tasamu kaidai kawai kaiwa wannnan number magana 01017018846

Ba nan ummu khalifa ta tsaya ba tana kawo original Egyptian abaya da shoes da duk abinda mutum keso tana kawowa zuwa gida Nigeria

Ummu khalifa 01017018846

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na talatin da ɗaya_

_____________

*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥

*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_

*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*

*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*

*TSUTSAR NAMA Billynabdul*

*GUDUN K'ADDARA Huguma*

*AMEENATU Mamuhghee*

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

______________
Chapter 55 · 0% Book details