← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 82

Sashe 45

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥

*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_

*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*

*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*

*TSUTSAR NAMA Billynabdul*

*GUDUN K'ADDARA Huguma*

*AMEENATU Mamuhghee*

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na ashirin da biyar_

____________

*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥

*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_

*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*

*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*

*TSUTSAR NAMA Billynabdul*

*GUDUN K'ADDARA Huguma*

*AMEENATU Mamuhghee*

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

__________

.......Saki dai dole Dafeeq yayi sa, sannan akai komai a rubuce kowa ta saka hannu aka bama kowa nasa copy ɗin d.p.o ma ya ajiye nasa. Khadijah ta dinga sakin ajiyar zuciya da jinta sakayau tamkar wadda akaima rahama. Haka suka taho gida Dafeeq na kallonta harda cin tuntuɓe mahaifiyarsa na jansa tana masifa da hararar Babansa. Dan gaba ɗaya yama fi kowa bata takaici daya kware musu baya ya zaɓi bare akansu har yana gurfanen bada haƙuri akan abinda ita bataga inda sukai laifi ba.

Sosai Baba ya sake jerama su Baba Hakimi godiya. Suka kuma haɗa musu shatara ta arziƙi dan sun ce yau kam gida zasu kwana tunda an gama komai. Sanda zasu wuce Khadijah harda kukanta. Haka dai sukai musu sallama suka tafi badan rai yaso ba. Amma dai in sha ALLAHU Baba yace zuminci ya ƙullu kenan. Khadijah batai ƙasa a gwiwa ba bayan wucewar Baba Hakimi ta sake neman gafarar iyayenta dama ƴan uwanta. Suma basu ja zancen ba sukace komai ya wuce ai sun yafe mata. Baba da Mama suka sake mata nasiha da nuna mata illar abinda tayin. Ranar ma taci kuka dan harda su zazzaɓi tasha da ciwon kai. Daga ƙarshe dai ƴan uwanta suka koma tarairaiyarta suma...



A gidan su Dafeeq kam bala'i ne ya nema kaurewa tsakaninsa da Kainaat daya tattara laifin komai a kanta mahaifiyarsa na kareta. Amma ita sai tai biris da shi saina murmushi da take dan a ganinta dai ta baƙanta masa rai. Kuma koba komai iyayensa sun kwana a bayan kanta. Duk da ma ba haka taso ba wlhy. Taso ace anyi bala'i iya bala'i da iyayen Khadijah ta yanda sai Dafeeq ya wajigu kamar na wata ɗaya ya fita a hayyacinsa. Amma koba komai dai hakan ma nasara ce.
Tsawatawar iyayensa ya taƙaita wannan fitina. Sai dai a ransa ya ƙudiri aniyar wlhy sai tayi dana sanin masa wannan abun datai masa. Oho bata damu ba, dan itama dai ta shirya masa tsaff. Bai yi niyar su koma Adamawa ba sam. Sai dai fa maganganun mutane da ALLAH wadarai da akema iyayensa da shi kansa akan Khadijah ya hanashi sakat a anguwa. Musamman ma da akace yanzu Kainaat ya aura tare da jin labarin tushen auren nashi. Shike nan mutane suka samu nayi dan duk wanda dai ya kalla Kainaat yasan ba sa'ar auresa bace duk da dai a addinance bawai haramun bane. Amma dai ana fassara shi nashi auren akwai manufa a ciki tunda ance Kainaat nada kuɗi.
Hankali tashe ya tattara Kainaat suka koma inda suka fito akan sai komai ya lafa zasu dawo. Dan ya ƙudiri aniyar baro Adamawa zai dawo gida Kano da zama. Kainaat kuwa da ita wasan yanzu aka fara....

*_BAYAN WATANNI_*

Tafe take cikin ɗan sauri-sauri, sai dai hakan bai hana bayyanar nutsuwarta ba irin ta ɗiya mace. Hijjab ne har ƙasa a jikinta da niƙab dan babu ta inda ake ganin komai nata sai ƙwayar ido. Komai ya canja a rayuwarta, canjawar da take tabbatar da ita a sabuwar Khadijah Muhammad Kura. Duk da watanni bakwai ɗin nan da suka biyo bayan abinda ya faru sun sake zuwa mata da wasu abubuwa ne mabanbanta wanda tai tsammani babu abinda zatace da UBANGIJI sai godiya. Taso komawa ta cigaba da karatunta, amma sai Baba ya tabbatar mata da cewar ta makaro kuma. In dai a gidansa ne ta gama karatu kenan wannan shine horon da zai mata akan kuskurenta. Sai dai zai barta ta koma islamiyya bazai taɓa tauyeta a neman ilimin addini ba, na boko kam sai dai idan aure ta ƙara mijin ya maidata amma shikam badai shi ba. Duk irin roƙo da magiyar da taima baba bai saurareta ba. Haka tanaji tana gani dole ta jingine maganar makarantar boko ta koma islamiyya kawai ƴan uwanta ma bata sha'awa. Dama dai ta kusa sauka ta tafka waccan tsiyar, dan haka a yanzu ta sake dagewa sosai fiye da da gashi har tayi saukar tunda dama tana gab. Zakuma ai bikin saukar da ƴan uwanta ne a ranar ɗaurin aurensu da ya rage saura kwanaki huɗu kacal a yanzu. Sam bata kula kowa a yanzu. Kai ko kallon wani namiji da wata siga batayi, dan duk ta haɗasu ta musu kuɗin goro a littafin rayuwarta. Bayan kammala iddarta samari da yawa harma da magidanta sun fito da niyyar aurenta amma ta dakatar dasu. Shi dai Baba dama baice mata komai ba, hakama Mama iyakarta da ita nasiha da shawara. Sai su Ni'ima ne keta zugata akan ta fidda miji a haɗa bikinsu dan ALLAH. Murmushi kawai take musu tace ba yanzu ba, ita da aure ma tana jin har abada. Sukan nuna jin haushin maganarta, itako ta tattarasu ta share kawai....
Isowar napep da take jira ya katse mata tunani. Sai da ta sanar masa ina zata sannan ta shiga tare da fiddo wayarta ƙarama ta daddana dakai kunne. Daga can Zuhrah ta amsa mata. “Aunty kin taho ne?”.
Kai tsaye ta ce, “Eh, ina fatan dai kun gama gyaran jikin”.
“Eh muna kammala, kema muke jiran dan har an gama mana komai ma. Dan ALLAH ki maza kizo a miki kema. Kefa kaɗai ya rage”.
“K nifa ku rabani da wannan gyaran jikin. Kunbi kun takura min kullum aka gama muku sai kun takura an yaɓamin wannan kayan naku a jiki ina dalili. Yau ma kawai zanzo ne saboda biyanta kuɗinta da kuma Baba daya ce dole nice zan tsaya a kanku muna komawa gidan”.
Dariya Zuhrah tai da faɗin, “Aunty Khadijah masifa, shike nan sai kinzo mudai muna jiranki.” wayar ta yanke itama tana taɓe baki, minti kaɗan suka iso anguwar. Ta biya mai napep ɗin ta shiga. Ta samu an kammalama su Ni'ima komai. Kamar kullum yauma sukai kanta su da mai gyaran jiki sai da aka mata aka kuma tsareta tasha abubuwan da ake basu wai maganin sanyi, ƙyalesu kawai take ana tasan wani ba maganin sanyin bane ba. Dan kusan sati biyu kenan ita ke kawosu ta wuce islamiyya, idan an tashi ta biyo ta ɗaukesu su koma gida. Baba ne ya sata wannan aikin badan komai ba sai dan tsoron yau da gobe. Sai da aka gama mata komai batare da jira ya daɗe ba ta maida kayanta da hijjab suka wuce gida akan idan taje can tayi wanka. Dama haka take yi ita kullum. Daga haka sukai sallama da mai gyaran jiki akan ita zata samesu gida gobe dakai ƙunshi...
Chapter 45 · 0% Book details