← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 82

Sashe 21

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.........A ɓangaren amarya da ango kuwa kowa ya tashi da mabanbancin yanayi. Ango na cikin farin ciki da nishaɗi, duk da kuwa ya shaida ya kuma tabbatar da amarya fa batako kama ƙafar Khadijahn sa ba. Dan a daren jiya ya tabbatar da zancen nan na mata sun bambanta. Tunda yake da Khadijah bai taɓa ganin tasha wani magani domin gyara jikinta ba yanda yake jin mata nayi, har bincike yasha mata amma bai taɓa cin karo da komai ba. Amma yarinyar nan ALLAH yay mata baiwa ta musamman da shi kaɗaine yasan wannan sirrin. Amarya kam da fushi ta tashi, duk da ango yayi wasan kura da ita tamkar ba ƙaramin yaron data raina ba taji a ranta Abaan ɗinta daban ne. A lokacin data samu kanta a hannun Dafeeq hawaye taitayi, dan gani take taci amanar Abaan ne. Ta jima tana hawayen kafin barci ya saceta. Basu farka ba sai yanzu da hasken rana ya hasko windown ɗakin. Itace ta fara tashi, ta zubama Dafeeq dake barcinsa hankali kwance ido ƙurr tamkar mai son tantance wani abu a jikinsa. Zuwa can kuma taja siririn tsaki tana ƙoƙarin sauka a gadon caraf taji an riƙe mata hannu. Da sauri ta jiyo, sai ko suka haɗa idanu da Dafeeq. Murmushi ya sakar mata ita kuma ta ɗan kauda kanta. Lips ɗinta dake motsi alamar tana son yin magana ya zubama ido, kamar wanda ya gama karantar abinda take son faɗa ya wani fisgota ta dawo baya. Idanunta ta rumtse da ƙarfi, cikin son sassauta fushinta ta ce, “Ranafa tayi, gashi bamuyi sallan asuba ba”.
Bai tanka mata ba, sai ma shigewa jikinta yay da jan bargo ya rufesu yana magana cikin kunnenta a hankali. Idanu ta waro waje tana turesa a jikinta. Amma ko gezau, sai ma abinda yay niyya ya fara aiwatarwa. Tana ji tana gani sai da yay yanda yake so da ita kafin ya kalleta yana dariya cike da shaƙiyanci. “Hajjaju karfa ki manta sadaki na biya”.
Harara ta zabga masa, a zuciyata tana faɗin (kaji ɗan iskan yaro. Ka biya kona biya maka) kamar yasan mi take faɗa, ya wani lakace mata hanci da faɗin, “Duk da fa ke kika bani na biya ni ne dai na biya a idon kowa”.
“Hummm”.
Tace kawai tana mai yunƙurawa ta tashi, da kallo ya bita harta shige toilet. Jin ta rufo ƙofar harda murza key yay wani kalar kwashewa da dariya. Sauka yay a gadon ya jawo handbag ɗinta mai ƙyau sosai. Tsaff ya bincike jakar, babu komai a ciki sai gold nata da ƴan kunne da sarƙa da su awarwaro data sanyo jiya da dare, ya jima yana kallonsu kafin ya wani taune lips ya maida ya ajiye. Da kansa ya gyara gadon, gamawarsa dai-dai tana fitowa. Baiyi magana ba ya shige bayin. Shima dai wankan yay ya fito, bata ɗakin, ta kuma ɗauke handbag ɗinta. Salla ya gabatar, sannan ya jawo hularsa dake ƙarƙashin gado ya shirya ƙuɗaɗen jiya tsaff ya nufi wadrobe ya ajiyesu a ƙasan kayansa. Cikin ƙananun kaya ya shirya. Kai tsaye ƙasa ya sauka yanata bulala ƙamshi, ɗakin da ya jefa Khadijah jiya ya nufa, yasa key ya buɗe...

Tana zaune a inda tai salla har yanzu, gyangyaɗi take ga hawaye sun bushe mata a fuska. Idanu ya zuba mata na tsawon minti ɗaya. Haka kawai yake jin wani iri a ransa mai kama da tausayi. Da kyar ya ture tunanin gefe dan kuwa duk abinda ya shirya bazai fasa ba. Khadijah tana cikin plans ɗinsa akan mallakar Hajiya da komanta, sannan ita kanta Khadijah yay alƙawarin sai yay punishing nata akan baƙin ciki da hassada da kuma maganganun data gaya masa jiya dan nan gaba ta kiyaye. Saboda shi dai yasan wannan yaƙin da zaiyi sai tafi kowa mora ai.
Saukar mari ya saka Khadijah farkawa a gigice. Yanda take shuri yasa Dafeeq daka mata tsawa. Babu shiri ta nutsu, dan harga ALLAH tana tsoron Dafeeq. Saboda tafi kowa sanin baida mutuncin. Gaidashi ta shiga yi jikinta na mazarin rawa. Bai amsa ba, sai harara daya zuba mata ya juya zai bar ɗakin yana bata umarnin ta biyoshi. Sai da ta share hawayenta sannan ta miƙe ta biyoshi, dan tayi alƙawarin matar nan tasa bazata taɓa ganin kukanta ba, yanda ta ƙwace mata Dafeeq da asiri itama zata ƙwato abinta da addu'a. Babu kowa a katafaren falon, sai ƙamshi mai daɗi da sanyin safiya. Wani banzan kallo yama Khadijah da nuna mata wata hanya. “Ga kitchen, ki haɗama amaryata break fast mai ƙyau da daɗi, awa ɗaya na baki. Bake kina da bakin yimin rashin kunya ba, zaki gane kuranki ne”.
Komai batace masa ba ta raɓa ta gefensa ta wuce. Da kallo ya bita ƙasa-ƙasa harta shige, sai kuma ya kalli inda Hajiya take tsaye tamkar sai yanzu ne ya ganta. Kainaat da tun fitowarsu da ga ɗaki itama take sakkowa ƙasa da mamaki take kallon Dafeeq da shima tun fitowar tasu ya ganta amma ya basar. Kamar bazatace komai ba, sai kuma fuska a yamutse ta ce, “Dafeeq wannan fa?”.
Tasowa yay ya kama hannunta, kamar wata ƴar yarinya ya kawota ya zaunar a cikin kujera. Zama yay shima kusa da ita yana wani kwanta mata a jiki. Idanunsa a lumshe yana shinshinar ƙamshinta ya ce, “Uwargida”.
Idanu ta waro sosai, dan duk da tasan matarsa ance mata yarinya ce batai zaton haka sharaf ba sosai. Dan Khadijah nada ƙaramin jiki, sannan bata cika tsayi ba can. Idan ma baka sani ba bazakace takai 19years ba yanzu. Tana kallon fuskarsa sosai ta ce, “Haba Dafeeq. Yaya zaka saka matarka mana girki. Ni fa ban aureka dan ka wulaƙanta matarka ba, fatana ma mu haɗe kai mu zauna lafiya”.
“Nima burina kenan hajjaju, sai dai ta nuna ita ba haka take buƙata ba. Jiya ban san munafukin daya kai mata hotonki ba na samu bata gida da yammar nan bayan gama ɗaurin aure. Sai bayan magriba ta dawo bata san zata saman a gida ba. Koda na tambayeta ina taje sai cewa tai gidan Baba Hakimi. Na ƙwace jakarta na duba sai ga ƙulle-ƙullen maganin asiri da hotonki da nawa, wai mu zata kai gidan boka ama asiri yarinyar nan”.
Ruɗewa matuƙa Kainaat tayi, dan duk da tasan itama ta taɓa yima Abaan asiri bada kanta taje wajen bokan ba, Mommyn Nadwa ce ta aiki mai aikinta. Kuma tun daga nan bata sake amsar wani maganin tsubbu ba, wancan ma tayi ne dan bata da mafita akan Abaan. A tsorace sosai ta ce, “Na shiga ukuna ni Kainaat wajen boka kuma? Baby dan ALLAH idan da matsala ka sakan kawai nan da sati guda. ALLAH ina masifar tsoron harka da masu asirin nan”.
Wata dariyar ƙeta Dafeeq yay a ransa, dan Kainaat bata san yasan duk manufarta na auren kisan wuta bane ba. A zahiri kam sai ya gimtse fuska kamar zai yi kuka. “Haba-haba Hajjaju daina wannan batu dan ALLAH. Ai ni da ke mutu ka raba takalmin kaza. Sai dai wata ƙaddara kuma amma bata wannan shashashar ba mara aji. Ki barni da ita zan horata a gidan har sai ta zama baiwarki, kema kuma na baki damar sakata duk aikin da kike so dan ki sallami masu aikin gidan nan suje su huta ita zata cigaba dayin komai”.
“Kana ganin babu wani damuwa baby”. Kansa ya jinjina mata da sauri. Ajiyar zuciya ta sauke a zahiri. A baɗini kam zuciyarta ce ke tafarfasa. Bata auresa dan shiga sabgar matarsa ba, balle ma wannan cilikowar da ko autan gidansu ya girmeta, ko shi Dafeeq ɗin sai dai suyi sa'anni da autansu balle ita. Amma kuma dolene kafin ta rabu da Dafeeq ta barma yarinyar nan tarihin ruwa ba sa'an kwando bane ba. Har ita zata kai gidan boka. An faɗa mata zama tazoyi ne. Fitowar Khadijah da tray bayan kamar awa ɗaya yasa Kainaat zuba mata ido, a cikin sakanni ta gama tsara gwada Khadijah taga shin da gaske yarinyar kishi take da ita ɗin....

________★
Chapter 21 · 0% Book details