Sashe 17
Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Guri ɗaya suka sake dunƙulewa sosai. Dan hatta malaman kansu a wannan gaɓar zukatansu bugawa suke da sauri-sauri. Sai dai basu yarda sun saki addu'oi ba. Masu ragguwar zuciya kam tuni fitsarin daya taru musu ya fara ɗiga, wasu ma gab suke da fashewa da kuka tsabar tashin hankali. Dan wannan al'amari ne da a film kawai suka sanshi bawai zahirin rayuwa ba.
Tsahon mintuna biyar wutar ta sake kawowa. Wani irin ihu mai jijjiga gida suka saki kusan su duka idan ka cire Baba da malaman nan sakamakon bayyanar Alimah a mummunar siffar horrors dan bata da maraba da su. Fuskarta da jikinta sunyi wani irin fari tamkar an baɗa mata hoda. Wajen idanunta yay wani zummm kamar wadda tai kukan jini, hakama bakinta duk jini ne, ga gashi a wargatse da uban tsaho har yana jan ƙasa, ta saman kanta akwai ƙahuna guda biyu. Hakama ƙafafunta kofataine, hanyenta da wani irin farcina zaƙo-zaƙo tako ina dai bata da ƙyawun gani. Dan su kansu tunda sukai mata kallo guda idanunsu suka rumtse babu wanda yay gigin sake maimaitawa.
Shuuuuu!! Ta wani irin zagayesu kamar mai tafiya a takalmin taya tana ɗaura zabgegen yatsanta a saman baki da faɗin, “Shiiiii!!!” alamar sumata shiru daga ihun da sukeyi. A tare suka shiga haɗiye ihun sai hawaye dake fita a fuskokin masu raguwar zuciyar cikinsu. Jaruman kuwa rawar jiki kawai suke yi, gashi a zagayesun da tai ɗin nan ashe ɗauresu tayi da igiyar da sudai basu gani a hannunta ba.
Kwas! Kwas!! Kwass!! Ta dingayin wani taku tamkar wadda ke jerin gasar ƙyau ta duniya. Sai kuma ta wani kwashe da dariyar data nema fasa zukatan su. Sai da tai mai isarta tana faman zagayesu kafin ta tsagaita, da wata kalar kakkausar murya ta ce, “Ku miyasa bil adama kuke da son shiga abinda babu ruwanki ne? To gashi nan shishshigin ku ya jawo muku mutuwa!!!”.
Cikin rawar baki da suɓutar baki Baba ya ce, “Baiwar ALLAH kiyiwa ALLAH ki haƙuri. Wlhy mu muzo ne domin ceton matar Jazool. Amma ki taimaka ki yafe mana”.
“Hahahaha tsoho! Idan kai wannan ya kawoka su waɗan nan miya kawosu? Sannan da kukazo ɗazun ban muku gargaɗin farko ba?!”.
“Kin mana wlhy, kin mana. Dan ALLAH kiyi haƙuri. Babu wanda zai sake maimaita kuskuren nan”.
“Wanda ma ke son maimaitawa ya maimaita. Dan ganin gawawwakin ku sai ya saka ƙafar wani bazata sake tako cikin gidan nan ba. Ɗanka kuma yanzu ya fara amsar sakamakonsa a hannunmu, dan sai ya tabbatar da bakowace mace ake taɓawa a zauna lafiya ba. Sai mun barma ire-irensa tarihin tunawa a wannan duniyar”.
A yanzu kam idan ka cire baba da malaman nan kowa kuka yake jin wai zata kashesu, sukam ganin ƙwam bai musu rana ba. Wata irin gigitacciyar tsawa ta daka musu. Sake dunƙulewa sukai waje guda suna mai sake ƙan ƙame junansu, masu fitsari na sake sakin second round. Cikin ƙarfin hali shugaban malaman ya fara karanto suratul baƙara. Da rawar jiki wanda suka iya suka fara suma. Kecewa da dariya Alimah tayi, sai kuma ta haɗe rai tare da tafa hannunta ta buɗesu. Sai ga bakunansu sun ƙage kowa ya kasa magana.
“Hahaha!! Ni zakuma karatu. Ni nan kuke tunanin ƙonawa? To kafin ku ƙonani ni bari na shafe babinku.” ta wani irin sake tafa hannaye sai ga wasu mugayen halittu na fitowa ta cikin bangwayen gidan a kowace kusurwa. Gaba ɗayansu sun gama rikicewa. Hatta da su baba a wannan gaɓar kam babu sauran jarumta a tattare dasu. Kowa zufa yake kashirɓan jiki na rawa Kaff-kaff kamar waɗanda aka kaɗama gangi. Yanda suke sake curewa waje guda sai sun matuƙar baka tausayi. Masu ƙarancin ƙarfin zuciya tuni sun fara sumewa dan ganin halittun nan kawai ba ƙaramin tashin hankali bane mai rikita tunani. Balle kaga kai suke dimfarowa tamkar mayuntan zakuna suna wani irin nishi da fesar da wuta a bakunansu. Suna gab da isowa garesu ta sake tafa hannayenta suka ɓace. Dariya ta shiga ƙyalƙyalawa tana kallonsu. Kafin ta wani irin fesa musu ruwa da hannunta data ware a kansu kamar mai musu daƙuwa. Sharaf suka jiƙe, waɗanda suka suma duk suka farfaɗo. Kuka ƴan maza suka shiga fashewa da shi suna roƙonta tayi haƙuri sun tuba ta yafe musu. Tamkar bata jisu ba ma ta koma jikin bango ta maƙale.
Shugaban malaman nan ne cikin galabaita da sauke numfashi ɗai-ɗai ya ce, “Baiwar ALLAH kiyi haƙuri. Ki sani akwai hisabi tsakanin aljan da bil adam. Yanda makomarmu take a tsakanin aljanna da wuta haka kuma makomarku kenan. Mu bamu zo nan domin cutar dake ba. Dan ALLAH kema kada ki cuta mana. Bamu san komai tsakaninki da Jazool ba. Amma zamu roƙeki shima ki yafe masa, ki kuma fita a jikin matarsa dan ALLAH ki barsu suyi zaman aure kamar kowa.....”
“Har abada hakan bazata faruba! Nace maka har abada! Har abada JJ bazaiyi aure ya zauna da wata mace ba. Kuma bazan taɓa iya yafe masa ba!!” sai ta fashe da wani irin mahaukacin kuka daya sake firgitasu da gigita su. Sosai tai kukan kafin ta ɗago kanta dake lulluɓe cikin dogon gashinta tana kallonsu. Ƙasa duk sukai da kawunansu. Muryarta na rawa da karkarwa ta ce, “Zan baku dama ta ƙarshe saboda wasu dalilai. A cikinku akwai bayin ALLAH, akwai masu ƙananan yara, akwai masu taimakon marayu, akwai masu ƙoƙarin bautama UBANGIJI, akwai masu ƙyautatama iyaye, akwai masu yawaita karanta Alkur'ani. Duk da dai akwai tamtirai irin JJ kuma sun san kansu. To sunci alfarmarku, zan barku ku tafi, amma ku sani, duk wanda ya sake gigin shiga gonata saina sabauta masa rayuwa. Alimah kuma kuje JJ ya fara sanar muku *_WACECE ANOOSH_*, ni da kaina zanzo gareku da Alimah. Kuma ku sanar masa ko ƙoƙarin yin ƙarya yay akan Anoosh ina gefensa zaisha mamakina, dan duk inda yake ina a tare da shi kamar yanda zuciyarsa da jininin jikinsa ke tare da gangar jikinsa. Na barku lafiya”. Ta wani irin harba hannunta kamar mai san ture abu. Sai gasu a tsakar anguwa an watsosu kamar kayan wanki.
Wayyo ALLAH zo kaga yanda ƴan maza ke rige-rigen tashi suna cika wandunansu da iska. Sai dai kaji garamm an buga ƙofar gida an shige. Wasu ma ba gidajensu suke ƙoƙarin shiga ba. Sai mai gidan ya farga ya jawosu waje shi ya shige yana faɗin, “Tafi gidanka”. Su baba da su Malam daba anguwar sukeba kam sun ma manta da motocinsu kowa ƙafarsa ce motarsa har zuwa titi. Babu mai sauraren ɗan uwansa kowa ƙoƙarin tare abin hawa yake. Burinsu kawai su gansu a nasu gidajen suma......✍️
_🚴🚴🚴To Bara nayi takaina Nima dai, malam na neman ƙafar zuwa gida, ni kuma Bilyn ku fa🤣🤣😂😂_.
Mura ta rikeni kwana biyu🤧🤧🤧.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na goma sha ɗaya_