Sashe 5
Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
........Da murnarsa ya shigo gidan yana faman washe baki. Tun a farkon tura ƙofar soron gidan yake ƙwala kiran sunanta tamkar mai shela. “My Queen! My Queen! Kina ina ne? Wai nikam. Fito! Fito ki gani fito My Queen!!”.
Har cin tuntuɓe take wajen saurin fitowa da ga bayin, tsabar yanda ta fito a rikice saboda kiran da yake faman ƙwala mata bama tasan da botikin wankansu da akoda yaushe yake a bayin ajiye ba ta fito. A ƙaramin tsakar gidan da bai wuce cin tabarma biyu ba sukaci karo. Kafin ma tace wani abu yayi wani kalar jawota ya rungume tare da ɗagata cike da farin ciki ya shiga juyi da ita. Ɗan ihu ta fara mara sauti tare da roƙon ya sauketa tana faman ɓoye fuskarta cikin jikinsa. Shiko duk da yasan bata son hajijiya sam bai sauketan ba, sai faman dariya ma yake abinsa yana cigaba da juyinsa. Sai da yay mai isarsa sannan ya afka ƙofar dake kusa da su, falone matsakaici dan kujerun da aka ƙawatasu da shi ma a mugun matse suke. Tsakar falon kuwa bai wuce girman sallaya ba, direta yay a saman doguwar kujerar yana hakki. Itako ta sake ƙanƙamesa har yanzu fuskarta na jikinsa. Sai da kusan mintuna biyu suka shuɗe taji hajijiyar ya saketa kafin ta ɗago kaɗan tana tura baki da kwaɓe fuskan tamkar zatai kuka.. a shagwaɓe ta ce, “Haba Husby so kake kaga bayana ne?”.
Dariya ya ƙyalƙyale da shi, cike da nishaɗi ya furta, “Ai mai ganin bayanki sai kin juya My Queen. Wlhy wani farin ciki ne na shigo da shi wanda na tabbatar idan kika jishi yau ƙyautata sai ta kasance ta musamman ne”.
“Woow Mijina bani nasha mana”.
“Ai dole kisha kuwa Matata, sarauniya ta, dan haka rufe idanunki”.
Ruf ta sufesu murmushi na sake ƙawata kansa a black beauty fuskarta mai wani irin sirrin laushi da sheƙi. Ga ɗan ƙaramin bakinta da yafi komai ƙawata sirrintaccen ƙyawun nata. Hannunta na dama ya kamo cikin nasa, yana cigaba da murmushin ya ciro abu a aljihunsa ya saka cikin hannun nata ya rumtse yana faɗin “Zaki iya buɗewa”. Buɗewar tai da sauri tare da ware tafin hannunta, ta ɗan zubama keys ɗin idanu zuciyarta na wani irin rawa-rawa. Sai kuma ta ɗago da sauri tana kallonsa da girgiza kanta. “Husby ka ɓaddani ALLAH. Keys ɗin miye haka?”.
Ido ɗaya ya kashe mata tare da jawota jikinsa ya rungumeta har zanin dake ɗaure a jikinta na kwancewa. Basu damu da hakanba su duka, suka ƙanƙame juna. A cikin kunnenta ya gwargwaɗa mata maganar da ta sakata ɗagowa da sauri tana kallonsa idanunta gaba ɗaya a waje. Cikin rawar lips idanunta na ƙiƙƙiftawa ta furta, “Naka fa Dafeeq?! Taya hakan zata kasance bayan nasan ko key na keke bamu da hanyar samunsa a gidan nan balle mota har ma da gida”.
“Ikon ALLAH kenan Deejoh na.”
A hankali ta ce, “Hakane. Sai dai komai ai yana da sila. Tayaya hakan ta kasance?.”
“Karki damu zan sanar dake komai. Amma fara mun haƙuri naɗan watsa ruwa ki bani abinci kuma naci. Dan yunwa nake ji ALLAH sosai. Banci komai a cikin nan nawa ba tun karin da mukai da safe”.
Duk da zumuɗin son jin da take haka ta daure ta danne. Cikin ƙarfafa kanta da ture abinda ke tsikarin zuciyarta ta miƙe tana murmushi. Fita tai a falon, babu jimawa ta dawo. Kusan a tare suka ɗaga labule, dan haka ta ɗan jaye baya ta bashi hanya. Fita yay yana sakar mata murmushi, ta maida masa murtani cike da son ƙarfafa kanta. Numfashi mai nauyi ta sauke lokacin da take sake kaiwa zaune a kujera idanunta akan keys ɗin nan dai. Ta kafesu da ido zuciyarta na ci gaba da kai-kawo. Haka kawai take ɗan jin kamar tsoro a ranta, sai dai bata san dalilin hakan ba, domin a zahirance ba tsoron ya kamata ace tana ji ba, murna ya kamata ace tafi kowa da wannan alkairin da ya samesu. Badan komai ba sai dan tuna baya, tuna baya akan rayuwarta da Dafeeq kafin aure, tuna baya kafin zamowarsu ƙarƙashin aure. Tuna baya bayan zamowar tasu ma'aurata har zuwa yau ɗin nan da suka wayi gari a matsayin da suke kafin wanda ke neman canjasu a yanzun nan...
Sunanta shine Khadijah, ɗiya ta farko a wajen iyayenta. Tana da ƙanne huɗu duk mata, sai namiji ɗaya daya kasance autansu. Mahaifinsu ba mai kuɗi bane, sai dai mai ƙarfin hali ne da wadatar zuci. Wannan imanin nasa ya sakasu tashi a gidansu matsayin ƴan gata, bama gidansu kawai ba har a cikin dangi da yaran anguwa sun kere tsara. Dan komai mahaifinsu tsaye yake wajen musu dai-dai ƙarfinsa. Hakama mahaifiyarsu tana nata ƙoƙarin da sana'arta ta saida kayan sanyi da kayan miya irinsu kuka, kuɓewa, magi, gishiri, daddawa. Kai duk dai wani nauyin kayan miya na gargajiya zaka samesa a wajen mahaifiyarsu. Dan haka gidansu ya kasace ɗaya daga cikin gidaje da ake zirga-zirga na sayayya. Ƙoƙarinta da ƙwazo a makaranta ya sakama mahaifinsu burin ganin tayi karatu mai zurfi ita da ƙannenta, amma kasancewar itace babba sai ya zam ita aka fara ƙoƙarin ginawa. Lafiya lau ta kammala primary ta shiga secondary ɗin dake ƙasan layinsu ta ƴammata, sai dai makarantar iyakarta jenior ce. Wato iya aji uku. Matuƙar ƙwazo da himma ta bada a karatunta, inda ta kasance ɗaliba mai ɗaukar first class a ajinsu tun daga jss 1 har zuwa jss 3. Sun zana jsce cikin nasara da jin kewar rabuwa da makaranta, musamman ita data kasance mai farin jinin malamai saboda ƙwazonta. Dan randa akai musu walimar fita ta samu ƙyaututtuka daban-daban da suka saka iyayyenta farin ciki tare da sake jin ƙaimi akan tsaya mata cigaba da karatu. Sun ɗanyi zaman gida har jarabawa ta fito, inda ta samu nasarar samun wata makaranta dake can wata anguwa, sai dai ita haɗe take ƴammata da samari. Makarantar babbar makarantace dan duk ɗalibin daya kasance a cikinta sai mai ƙwazon gaske. Saboda akan tsinto yara ne masu ƙwazo sosai daga makarantu daban-daban zuwa nan a duk shekara, itama ƙwazonta ya bata wannan damar. Tayi farin ciki matuƙa da zamowarta ɗalibar wannan makaranta mai farin jini da kowa ke fatan ganin ya sameta, hakama iyayyenta sunyi murna mara misali. Anan ɗin ma lissafin bai canja ba, dan ta matuƙar dagewa a tarm ɗin farko itace ta ɗauki ta ɗaya a ajinsu, ta kuma sami ƙyautar yarinya mai tsafta da kuma rashin yin latti. Iyayenta sunyi matuƙar farin ciki tare da ƙara ƙarfafata, dan har ƙyauta baba ya mata ma, hakama Inna ta siya mata kaza guda ta soya mata tace taita ci har ƙannenta na kukan an nuna musu wariya. Ta gama ss1 lafiya, a tarm ɗin da suka shiga ss2 komai ya fara, dan shine farkon labarinta tsakaninta da _Dafeeq Abubakar Ja'e_.......
★★★★