← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 82

Sashe 22

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gwaggo ita ta shigema JJ gaba wajen mahaifiyar Anoosh, dan kuwa mahaifinta ya rasu. Akwai mutunci da girmama juna tsakanin Hajiya Lailah da Gwaggo. Dan Hajiya Lailah na ɗaukar Gwaggo tamkar uwa a anguwa. Bata huɗɗa da kowa sai ita. Jin JJ nada alaƙa da Gwaggo ta bashi damar neman soyayyar Anoosh. Tare da roƙonsa kar yaci amarta. Ya mata alƙawarin da tabbatar mata sai dai ya zamewa Anoosh garkuwa bawai shi ya kutsama mutuncinta ba. Kalamansa sun tasirantu a zuciyar Hajiya Lailah, dan haka taji ta sake yarda da JJ. Dan kuwa dai da fuskar musulinci yaje gabanta.
Anoosh dai ita kaɗai iyayenta suka haifa. Mahaifinta ya rasu tun tana ƴar shekara bakwai a duniya. Mahaifiyarta Hajiya Lailah ta cigaba da kula da ita da bata tarbiyya duk da ta sake aure. Mahaifin Anoosh ya bar dukiya mai yawa, dan haka sabon mijinta yay amfani da wannan damar ya mamaye komai ya gudu. Lokacin Anoosh nada shekara goma. Wannan abu ya ƙona zuciyar Hajiya Lailah matuƙa, gashi bata san a ina zata nemosa ba, dan irin auren nan sukai na ƴan birni, tasan dai sunan garinsu amma bata taɓa zuwa ba shi kuma bai taɓa kaita ba. Gidansa da yake da matarsa zaune kuma sai bayan ya gudu tama san ba nashi bane, ya kwashe iyalan nasa sun gudu tare ashe haya yake. Haka taci kukanta ta haƙura dan ya bar mata takardar saki har uku. Taimakon da ALLAH yay mata sune sarƙoƙinta na gold da bai gani ba, wanda takema ɓoyo na tsiya, su kansu takardun kaddaririnsu ɓoyesu take, amma bata san yanda akai mijin nata ya gano takardun ba ya kwashe. Sarƙoƙin nan ta ɗiba dan hatta gidan da suke ciki ya sayar, ta tattara ƴarta mai lalurar rashin magana suka nufo garin Kano. A motar hayar da suka shigo ta haɗu da Gwaggo dake ta jan Anoosh da hira. Ance mai ɗa wawa, tuni Hajiya Lailah taji ƙaunar Gwaggo ta shigeta. Bayan sun iso Kano kowa ya sauka, Gwaggo tai musu sallama tanayi kamar karta rabu da Anoosh dan yarinyar ta shigar mata rai sosai, ga tausayi. Yarinya ƙyaƙyƙyawa ta gaske amma babu bakin magana. Har Gwaggo ta shiga napep Hajiya Lailah ta dakatar da ita.
“Dan ALLAH Baba idan bazaki damu ba zan so mu biki gidanki”.
Ɗan jimm Gwaggo tai tana kallonta, sai kuma tai murmushi da faɗin, “Karki damu shigo” dan dama ta lura matar na cikin damuwa tun a mota. Sosai Gwaggo ta karramasu, hakama mijinta. Bayan kwana biyu Hajiya Lailah bata ɓoye musu komai ba a kanta. Su Gwaggo sun tausaya mata, sun kuma cigaba da zama da ita a gidan har na tsawon wata bakwai, daga baya aka samu wannan gida dake kusa da su Gwaggo masu gidan zasu tashi sakamakon rasuwar mai gidan Hajiya Lailah ta saida gold nata suka saya. Duk da komawarsu wannan gida akoda yaushe Anoosh na nane da Gwaggo. Anoosh yarinya ce mai haƙuri sosai, bata da yawan hayaniya. Ga yawan murmushi. Duk da kasancewarta bebiya tana karatu, dan a yanzu haka ma jam'i takeyi anan b.u.k tana 100 level, suna gab da shiga 200. Tana da kaifin basira, gata ƙyaƙyƙyawa, duk wanda ya santa ya santane cikin hijjan akoda yaushe. Dan ko'a cikin gida zaka iya samunta da hijjab, sai ma idan Gwaggo ce ta tirsasa mata cirewa tasha iska. Shekararsu ɗaya a anguwar mijin Gwaggo ya rasu, mahaifin MB yaso ta tashi amma taƙi saboda su Anoosh, ga shi kuma gidansu ne sannan bata taɓa haihuwa ba. MB ba zuwa gidan yake ba sai salla-salla. Wani lokacin ma akanyi shekara biyu bai zo ba saboda karatunsa. Kusan yanzun ma hakanne, dan shekararsa biyu kenan rabonsa da gidan shiyyasa bai san batun su Anoosh ba sam.
Sj da su JJ abokan juna ne da suka zama ƴan uwa ma. Dan anguwarsu ɗaya, tare sukai secondary school suka kuma wuce ƴar aduwa University katsina karatu. Akwai shaƙuwa sosai a tsakaninsu, dan tun suna secondary sun iya yaudarar ƴammata. Iyayensu basu taɓa damuwa da abinda sukeyi ba, dan ana kallonsa a shirmen ƙuruciya har suka kammala secondary. Shigarsu JJ jami'a alƙibalarsu ta sauya, dan kuwa sunzo inda babu uwa babu uba babu wani ɗan uwa mai tsawatarwa. Ƙoƙarinsu a aji da iya gayu gasu ƙyawawa ya fara jan hankalin mata garesu, to dama gasu gwanayen yaudara. Tun ana iya yaudarar har suka fara huɗɗa da matan, takai in har zasu koyar da yarinya karatu sai sunyi duk yanda zasuyi sunyi amfani da ita. Tun suna samun irinsu har suka fara hure kunnen salihan yaran mutane. Al'amarin su ya gawurta dan har kawalci sukema malamai. Wannan hali nasu yasasu zama ƴan gaban goshin malamai, dama kuma gasu da ƙoƙarin su. Sun kammala karatunsu lafiya suka baro Katsina ana kewarsu, koda suka dawo gida maimakon abu yay sauƙi saima ya cigaba. Dan kuwa ALLAH ya taimakesu sun samu aiki da taimakon wani lecturer nasu da suka dingama kawalcin students. Duk da aikin ba wani bane koyar da yarane a makarantar boarding babu musu suka amsa. Wannan ma wani lasisi ne na cigaba da lalata yaran mutane a cikin makaranta da wajen makarantar ma, dan in har suka kwallafama yarinya sai sun cimma burinsu a kanta. Sai akai sa'a sunfi samun irinsu lalatattu, wanda suke lalatawa ta yaudara ƙalilanne. A yanzu haka suna shekara ta farko da fara aiki, sun haɗa kuɗi sun sayi mota acewarsu matan sunfi amincewa da mutum idan yana da mota.......✍️

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na goma sha huɗu_

........Sannu a hankali JJ ya fara shiga jikin Anoosh, tun bata kulashi harta ɗan fara sama-sama ganinsa kamar mutumin kirki. Dan a duk sanda zai zo gareta shigar mutanen ƙwarai yake yi, sannan kuma da fuskar musulinci. Bai sake yarda su MB sun masa rakiyya ba. A kuma gidan Gwaggo ake hirar. A haka suka share wata kusan uku, zuwa lokacin Anoosh ta fara sakin jiki da JJ sosai. Da wannan damar yay amfani ya dinga zuwa yana kaita school, idan ta gama lectures yaje ya ɗakkota ya maidota gida. Ganin babu wata matsala Hajiya Lailah ta barsu, sai dai tana saka musu ido sosai, sai da ta sake tabbatar da babu matsala sannan ta samu nutsuwar zuciya. Ta kuma faɗima JJ ya shirya Anoosh na shiga 300 level zata mata aure, karatu ta ƙarasa a ɗakinta. Ya nuna jin daɗinsa da hakan a zahiri, a baɗini kam dariyama abin ya bashi. Tayama kamarsa shi JJ mai buhu-buhu na ƴammata lafiyayyu dake binsa da roƙo ya ƙare da auren bebiya mai raunin gani sai da gilashi. Duk da dai Anoosh nada ƙyau sosai baya jin zai iya wannan sadaukarwar, adai cigaba da tirzawa ya samu abinda yake so yay gaba abinsa.
Tun daga randa Hajiya Lailah ta masa batun shirin aure ya fara hillatar Anoosh akan ta ɗan dinga saka mayafi mana, taya shi da zai aureta ace baida ikon ɗan ganinta kamar yanda sauran ƴammata kema samarin su yaji daɗi. Takan nuna masa ita bazata iya ba tana jin kunya, sai ya koma nuna mata to idan ta shigo motar tana cire hijjab ɗin in ya kaita school sai ta maida. Nan ma ta nuna bazata iya ba, yay fushi sai da ya kwana biyar baya kiranta a waya dan dama vc sukeyi, baya zuwa kaita makaranta. Tun abin baya damunta harya fara, dan da gaske JJ ya dasa rassan ƙaunarsa a zuciyarta ta yanda bazata iya cisgeshi ba koda taso hakan. Koda Hajiya Lailah ta lura da yanayinta da kuma daina ganin JJ na zuwa ta tambayeta sai cewa tai yayi tafiya ne. Murmushi kawai Hajiya Lailah tayi, tana mai jin tausayin ƴar tata dan ta fahimci itama irinta ce mai zurfafa soyayya akan mutum. Zata tayata da addu'a ALLAH ya sassauta mata, dan ita taga illar zurfafa soyayya wa namiji. A kwana na shida JJ yazo sakamakon kiran da Anoosh taima SJ ta vc tana kuka tace ya bashi haƙuri. Ƙin mata magana da dariya yay har ya kaita makaranta ya ajiye, haka ta nufi aji jiki a saɓule. Bayan ta gama lectures nata ta kirashi kamar yanda ta saba, uhumm kawai yace mata ya yanke kiran. Babu jimawa sai gashi nan ga fuskarsa babu alamar yasan minene dariya. Sosai ta sake shiga damuwa, dan haka suna shiga mota ta zare jijjab ɗinta hawaye na cika mata ido. Amma yaya zatai bata son cigaba da ganin ɓacin ransa. Sannan kuma a ganinta da wautar tunaninta ko addini ya yarda wanda zai aureka ya ganka. Wata irin wawuyar ajiyar zuciya JJ ya shiga saki a jajjere jikinsa na tsuma, dan kuwa tabbas Anoosh cikakkiyar mace ce data amsa sunanta mace. Irin matan nan ne da ALLAH ya azurta da ƙira ta asalin gwalbar fantar da ake faɗi. Dan duk da tana a shekara ta Ashirin ko ina na Anoosh cike yake dam gaba da baya. Ga wata lafiyayyar fata mai santsi da ɗaukar ido a dalilin yawan zama cikin hijjab. Gata fara tas tamkar madarar shanu sabon tatsa. Kai komai yaji dai, rashin magana da raunin idanu ne kawai tawayar Anoosh a rayuwa. Amma shi kam ana cewa mutum tara yake bai cika goma ba to a wajensa Anoosh ta cika harta zarta a ɓangaren halittar jiki. Da ace tana magana kuma idanunta na gani ras kamar a kowa shikam babu abinda zai hanashi yin wuff da ita.
Jin yay ɗiff yasa ta ɗagowa ta kallesa. Da sauri ya ɗauke idanunsa dake mata kallon ƙurilla da gaba ɗaya ya kaucema shari'a. A kasalance yaja motar suka tafi. Sai da sukaje ƙofar gida ya ce, “To sa hijjab ɗin”. Jikinta har rawa yake ta saka, dan tunda take a rayuwa bata taɓa shiga takura da matsuwa ba irin yau. Tana gama sakawa ko sallama batai da shi ba ta buɗe motar ta fice tana cin tuntuɓe. Rakata yay da wani makirin murmushi yana zuƙar baki kamar wanda yaci yaji, dan maganar gaskiya ta kwance masa lissafi. Baya jin akaf ƴammatansa ya taɓa cin karo da mai irin surar Anoosh...

_________★
Chapter 22 · 0% Book details