Sashe 20
Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Wani irin shurinta yay da ƙafa tare da cilla mata mayafi yace, “Tashi dan ...” ya mulmula mata ashariya. Ganin bata da niyyar tashi yay wani irin fisgarta tana tirjewa yana janta kamar wata dabba har waje. Kasancewar anguwar babu wuta gashi wata yay nisa ya buɗe motarsa ya cillata baya ya rufe. Gidan ya kulle shima ya zagaya mazaunin driver yaja motar a fisge. Har suka iso katafaren gidan Khadijah na kuka. Maigadi ya wangale musu gate ya shige. Koda ya fito nan ɗin ma janta yay zuwa ciki kamar abar banza, a wani haɗaɗɗen falo ya shigo da ita, ɗaki na farkon shigowa ya buɗe ya cillata ciki ya maida ƙofar ya kulle ya wucewarsa sama abinsa...
Gaba ɗaya kukan da take ya tsaya cak saboda azabar wahalar buguwar da kanta yayi da gado a dalilin wullota da Dafeeq yayi. Tuni goshinta ya fara ɗigar da jini saboda fashewar da yayi. Kwanciya kawai tai yaraf tana sauke wasu irin ajiyar zuciya kamar wadda numfashinta ke barin gangar jikinta. Kafin dogon lokaci jikinta ya ɗime da zazzaɓi mai zafin tsiya. Gab-gab ta fara rawar ɗari saboda ac dake aiki a ɗakin. Tana kwance a cikin wannan wahalar take jin shigowar motoci da guɗe-guɗe alamar yanzu ne ma ake kawo amaryar. Zuwa can taji sun shigo falon. Yanda suke shewa da arerewa yasata fahimtar bama su da yawa ƴan rakkiyar amaryar. Zuwa can taji kiɗa ya fara tashi, sai kuma ta jiyosu suna ihu da shewar ango-ango. Hakan ya tabbatar mata da Dafeeq ne yaje inda suke kenan, da alama ma rawa yake shi da amarya kamar yanda take ji a kalamansu. Kusan awa biyu da wasu mintinan suka ɗauka a gidan, dan sai sha ɗaya taji gidan ya ɗauki shiru. Daga haka bata sake jin motsin kowa ba har dare ya raba tana dai kwance a wajen jinin dake ɗiga a goshinta ya fara rinjayar idanunta alamar jiri...
A ɓangaren amarya Kainaat da ango Dafeeq kam bayan wucewar ƙawayenta su Nadwa cak ya ɗagata daga tsakkiyar falon cikin kuɗin da suka musu liƙi yay sama da ita. Dan Kainaat dai bata da jiki sosai can, amma fa a murjenta take suɓul-duɓul kamar alalar gwangwani. Kai tsaye ɗakinsa ya wuce da ita suna faman sakarma juna murmushi, ya direta a tsakkiyar gadon yana hakki, dan duk da bata da ƙiba tanada nauyi, ƙarfin haline kawai da son ya birgeta ya sashi jurewa har ya kawota nan. Haƙuri ya bata akan bari yaje ya ɗakko wayoyinsu. Ta jinjina masa kai tana murmushi. Gudu-gudu sauri-sauri ya dawo falon, sai da ya waiga bayansa ya tabbatar Hajiya bata biyosa ba sannan ya durƙusa ya tattare dollars ɗin da ƙawayenta suka musu liƙin da ƴan dubu-dubu sabbi ƙal. Taf ya cika hularsa harda dannawa da ƙyar, bakinsa a washe dan yasan waɗan nan kuɗin ba ƙaramin kuɗi bane ba. Wayarsa da tata dake a Centre table ya ɗauka ya koma saman bayan ya kashe fitulin falon da kwasar ledojin kayan sayen baki. Da dabara ya zira hannu daga waje ya kashe wutar ɗakin sannan ya shiga, kai tsaye gaban gadon yaje ya tura hularsa mai ɗauke da kudin nan ƙarƙashin gadon sannan ya ajiye sauran kayan yana ƴar dariya da faɗin wasu maganganu wa hajiyar tashi irin shi ya kashe fitilar ne duk a cikin soyayya. Kainaat bata damu ba, dan itama dai zuciyarta ta tafi wajen tunanin ta yanda zata zille masa ne. Sai da ya gama ɓoye kudinsa da ƙyau ya kunna fitilar...
Anci ansha tsakanin amarya da ango. Sannan ya buƙaci suyi salla. Kai tsaye tace masa tana period. Ƙarara taga damuwa a fuskarsa, a ranta tace shege ai maganinka zanyi, dan daga gani mayen yaro za'ai anan. Suna haɗa ido ta sakar masa murmushi, shima dai mayar mata yayi cikin yaƙe. Jiki babu laka ya tashi ya canja kayansa zuwa na barci, itama yaje ɗakinta ya ɗakko mata. Amsa tai ta shiga bayi ta canja, bata fito ba sai da ta turama Abaan saƙo kamar yanda ta saba a kullum naban haƙuri da good night. Koda ta fito bata kula Dafeeq ba ta kwanta, dan zuciyarta ta tafi wajen Abaan ne kamar yanda ta saba a kowane dare bata iya barci sai da tunaninsa, mafarkinsa shine abin yinta a kullum kuma. Babu zato babu tsammani taji Dafeeq a jikinta, hankalinta ne ya tashi, ta shiga son turesa, amma ya tabbatar mata shifa ko rage zafine sai yayi gaskiya. Bataƙi ba anan, dan koba komai tana kewar abokin rayuwarta, musamman daya kasance ita bata iskanci ko'a yanzun.
Dafeeq shegen yaro ne, dan sai da yay yanda yay ya shagaltar da Kainaat har ya binciketa yaji babu wani period da takeyi batare data fargaba sai jinsa tai yana ƙoƙarin kai hari. Hankalinta ya tashi matuƙa, ta shiga turesa amma ya nuna mata shi sabon jinine, sannan ƙarfi ba'a shekaru yake ba, namiji kuma duk ƙankantarsa dai sunansa namiji...
★ Busowar iskar asuba mai sanyi da ni'ima ta farfaɗo da Khadijah. A hankali ta shiga buɗe idanunta tana karanto addu'a. Ganinta ba'a ɗakinta take ba ya sata maida idanunta ta rumtse komai na dawo mata dalla-dalla. Hawayene suka shiga sakko mata, itafa har yanzu kallon komai take kamar almara. Sannan wani gefe na zuciyarta na tabbatar mata Dafeeq ɗinta baya cikin hayyacinsa. Dole ne matar nan asiri ta masa. Ɗari bisa ɗari ta yarda da wannan tunanin, dan haka ta yinƙura ta tashi da ƙyar. Goshinta ta shafa, jinin ya tsaya, sai dai wajen ya mata nauyi kuma yana mata raɗaɗi. Mikewa tai gaba ɗayanta cikin ƙarfin hali ta nufi bayi. Bata damu da kallon ko'ina ba dan komai baya birgeta a gidan duk da ita kanta tasan ya haɗu. Ta jima tana kallon kanta a madubi kafin ta wanke busashen jinin goshinta zuwa fuska. Ashema raunin da taji ba wani babba bane can sosai. Alwala tayo tazo tai sallar asuba. Daga haka ta jingina da gado ta fara rera kuka, sai da taji kanta na barazanar tarwatsewa sannan ta haƙura. Har rana ta hasko windown ɗakin bataji motsin kowa na gidan ba, ga shi ya kulleta ta baya, dole ta haƙura ta zubama sarautar UBANGIJI ido kawai.......✍️
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na goma sha uku_
_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_
_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED
_____________