← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 82

Sashe 34

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

.......Wani irin jijjiga zuciyar Dafeeq tai a dalilin jin amsar da maigadi ya bashi cewar ai tunda safe wai Khadijah ta fita a gidan. Baki ya buɗe zai masa masifa sai kuma ya fasa tamkar wanda ya tuna wani abu. Ciki ya koma, babu jimawa sai gashi ya dawo da key ɗin mota a hannu. Dan zuciyarsa na sanar masa Khadijah na can tsohon gidansu ne. Sosai ya dinga gudu duk da babu nisa sosai, cikin ƙanƙanin lokaci ya iso. Ji yay ya ɗan samu nutsuwa ganin gidan kamar ba'a kulle ba, dan haka ya afka ciki yana wani cika da batsewa shi a dole zaiyi hukunci. Sai dai me, tako ina babu alamar Khadijah a gidan, kai hasalima kamar babu wanda ya shigo gidan.
(Kodai gidan Baba Hakimi ta tafi) zuciyarsa ta ayyana masa cike da ƙarfafawa. “Tabbas hakanne ma, dan nasan ko giyar wake tasha bazatace zata tafi Kano ba kuwa. To inama taga kuɗin motar tafiyar ne. Aiko bazan je ba, ta gama guje-gujenta har sai nan da kamar wata ɗaya ma zan leƙa gidan baba Hakimin sannan ta gama galabaita. Barima na cire layin da duk ƴan gidan suka sanni da shi ta yanda zan ƙara dafata da gigita rayuwarta”. Ya ƙare faɗa yana wani murmushi da ciro wayarsa a aljihu ya cire layin da yasan su baba Hakimi zasu iya samunsa da shi. Fitowa yay ya kulle gidan, daga haka ya tattara batun Khadijah ya watsar gefe, dan daga nan gidan abinci ya nufa yaci ya ƙoshi sannan ya fito zuwa wani hotel ya kama ɗaki dan itama Kainaat ɗin yay alƙawarin sai ya mata yaji na kwana biyu, sannan ya tsara yanda zai fara aiwatar da shirinsa a kanta dan ya fahimci itama ƙwalluwar kanta ce dole sai ya tashi tsaye...

🚴🚴🚴Hummm

___________

Babu wanda ya iya ƙwaƙwƙwaran motsi a tsakanin Baba da su Mujee. Sun zubama JJ dake kuka ido kawai zukatansu na duka tamkar zasu ɓallo ƙirazansu su fito waje. Tsahon mintuna biyar sannan cikin ƙarfin hali mahaiyarsu da suke kira Inna ta share hawayenta muryarta na matuƙar rawa ta ce, “Jazool kai ne ka aika aka kashe su kenan?”.
“Wlhy Inna ni bance su kashesu ba.” JJ ya faɗa cikin shaƙewar murya da karkarwar harshe hawaye na kwaranya a idanunsa....
A fusace Yaya Inusa ya ce, “Munafuki ƙarya kake yi. In ba kai kasa su kashesu ba ya akai sunanka ya fito a bakinsu. Dolene dasa hannunka a mutuwar bayin ALLAHr nan Jazool. Ka zaluncemu ka ɓata mana sunan gida, ka zubar mana da mutuncinmu. Idan aure kake so miyyasa bazaka faɗa mu maka ba. Duk da mu bamasu ƙarfi bane na tabbatar bazamu gagara maka aure ba harda ginin muhallin zama. Miyasa ka aikata wannan zalincin Jazool? Miyasa kasa a kashe su? Mi suka maka innalillahi wa-inna ilaihiraji'un...” kuka ya sarƙeshi.
Yunƙurawa JJ yay zai tashi amma ya kasa sai jikinsa ne ke rawa. Dole ya koma ya kwanta yana jujjuya kai ga hawaye na zuba kamar an buɗe fanfo. “Yaya wlhy bance su kashesu ba, na turasu ne kawai su amso min wayoyinsu su kuma kwaso min takardun gidan, nayi hakanne dan na ɓoye duk wani abinda Hajiya Lailah zata iya amfani da shi wajen tona min asiri. Takardun gidan kuwa zan mata barazana da shi ne bayan ta yarda bazata fidda maganar ba sai na maida mat.....”
Tauuuu!!!!. Ka ke jin saukar wani gigitaccen mari a kan fuskarsa. A take kowa ya gigice a ɗakin aka shiga waige-waige. Yayinda JJ ya dafe kunci ya fashe da wani irin marayan kuka tamkar zai shiɗe. Wani marin aka sake ɗauke fuskarsa da shi, sai gashi zaune dingan gan yana kwara ihu da waige-waige. Amma abun mamaki babu alamar wanda ke marinsa. Sake ƙwala gigitacciyar ƙara yayi yana zabura da mamuƙe cinyarsa. Dai-dai nan Alimah ta bayyana a cikin idanunsa da wuƙa jazurr alamar an sakata a cikin wuta ne. Dan gaba ɗaya inda ta ɗora masa wuƙar ma ya yaye. Sai azaba mai ratsa kwanya dake shiga har a tsakkiyar ƙwalwar kansa. Sauran ƴan ɗakin ba ganinta suke ba, dan haka duk sukayo kan JJ ɗin suna tambayarsa mike faruwa da ƙoƙarin ganin cinyarsa daya riƙe gam.
Bai iya basu amsa ba, sai kuma da yake yana faɗin, “Dan ALLAH kiyi haƙuri zan faɗi musu gaskiya, ki taimakeni ki bar ƙonani, dan ALLAH kada ki kasheni na tuba. Wlhy ni ne nace su sakama gidan wuta bayan sun ƙwace komai nasu, amma wlhy bance suma mahaifiyarta fyaɗe ba. Nayi tunanin kuma zasu gudu subar gidanne dan wlhy bance a saka musu wutar dan su mutu ba ne. Kuma koda sukazo suka sanar min abinda suka aikata na musu masifa har nace bazan biyasu sauran kuɗin aikin ba mukai faɗa da su, sukace zasu tona min asiri shine na haƙura na basu cikon kuɗin, ni kuma na cire kuɗin Hajiya Lailah dake account ɗinta dana Anoosh dan duk naga komai a cikin takardun gidan da alama ta rubuta ta ajiye ne saboda Anoosh ɗin. Sannan ko auren Anoosh dana yarda nayi batare da saninku ba nayi ne dan mutane karsu zargi komai a kaina, sai kuma sanadin hakan akaita kawo kuɗin gudunmawar kula da ita a asibiti daga ƴan anguwar da mutane, sai kuma Anoosh ɗin ta rasu kafin ayi aikin. Da kuɗinne na fara kasuwanci na kumayi gini na sai mota sannan na gyara gidan nan”.
Salati aka sake ɗauka a ɗakin matan na sake fashewa da kuka. Mamaki da al'ajabin JJ na sake kashesu. Dan bazaka taɓa zaton zai iya aikata hakan ba. Duk cikin gidan yafi yaran shiru-shiru, idan ma ka kallesa saika ɗauka shine ustazun gidan saboda ƙarancin yawan kwaramniyarsa a zahiri. Ashe a can cikin rai sheɗanin kansa ne ƙanin iblis....

★★★

Sun iso Kano cikin ƙanƙanin lokacin da ya bama Khadijah mamaki, duk da dai ba'a cikin hayyacinta take ba ma dan hankalinta sam baya tare da ita. Tun a airport ɗin aka sakata a wata ƙyakykyawar farar mota tare da Awwal aka wuce da ita asibiti. Ba haka taso ba, taso ace gida suka wuce da ita ko suka barta ta tafi, sai dai bata iya tayi magana ba dan tana jin jiki sosai. Ga ƙarfinta ya gama ƙarewa saboda jigatar dukan da tasha wajen ƙaton banza Dafeeq, ga yunwa ga barazanar fashewa da zuciyarya ke neman yi na damuwa da tashin hankali abinda zata iya tararwa. An kaita wani clinic mai ƙyau da bata ko san a wace anguwa ne ba. Babu ɓata lokaci aka shiga bata kulawa ta musamman mai nuni da cewar ansan Awwal a wajen, kuma yana da faɗa aji, ko kuma wanda taji yana kira da yayansan ne mai faɗa ajin tunda shine ya turosu nan ɗin shi kuma ya wuce sabgarsa...
Chapter 34 · 0% Book details