← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 82

Sashe 24

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

2:23am ya sake duba agogon dake gefen gadon. Ƙaramin tsaki yaja tare da duban gefensa da Hajiya ke barcinta hankali kwance. Gaba ɗaya zuciyarsa a ƙuntace take, dan duk yanda yaso yau ma ya more taƙi yarda. Dataga ma zai takura mata sai ta jefeshi da bandir na 1k guda biyu wai ta saya. Duk da yaji zafin abinda tai masan haka ya ɗauki kuɗin yana binta da kallo. Itako ta ɗauke kanta tana wani faman cika da batsewa tai kwanciyarta tare da jan bargo. Dolo haka ya kwanta a gefenta ya haɗiye abinda ke masa kai-kawo. Sai dai duk yanda yaso barci ya ɗaukesa hakan ya gagara. Dan ya riga ya saba ba haka suke da Khadijah ba. In har ba tana period ba baya iya ɗaga mata ƙafa koda faɗa sukayi kuwa, kai koda ma tana period ɗin dole tai masa yanda zai samu nutsuwa. Amma sai gashi yanzu da matan har biyu bashi da wani ƙarfin iko a kansu. (Har Khadijah?) Wani gefe na zuciyarsa ya ayyana masa. “Kai ina, ita kam ai bata isa ba”. Ya faɗa a zahiri yana wani girgiza kansa da sake ɗaure fuska. Hajiya ya sake juyawa ya kalla, ganin barci take sosai ya sake jan ƙaramin tsaki, sai kuma ya lumshe nasa idanun yana fatan barcin ya ɗaukesa shima. Sai dai ina babu alamar hakan, sai ma wutar fitina dake sake ruruwa a jikinsa. Zaram ya miƙe ganin zai halaka, cikin sanɗa kamar wani ɓarawo ya sauka a gadon, da rarrafe ya isa ƙofa ya buɗe a hankali yana waigen Kainaat ya fita. Sai da yay ɗan jimm ya tabbatar babu wani motsi na alamun ta farka sannan ya miƙe ya sauka ƙasa, dan nasu ɗakunan na sama ne na Khadijah na ƙasa. Kai tsaye ɗakin ya nufa abinsa...

Cikin barci taji ana taɓata, firgigit ta farka sai dai bata da wani kuzari a jikinta. Sosai ta ware idanunta na mamakin ganin Dafeeq. Zatai magana ya wani rungumeta yana girgiza mata kai alamar kartace komai. Ƙasa cewar tai kuwa, ta cigaba da binsa da kallo kawai. Hakan ya bashi damar sake shige mata jiki alamar dai akwai abinda yake buƙata. Cikin rawar murya da sanyin jiki ta ce, “ALLAH bazan iya ba yunwa nake ji”.
Shiru yay yana kallonta, sai kuma yaja ƙaramin tsaki yana miƙewa ya fita a ɗakin. Jitai kamar ta kurma ihu ta ce ya dawo amma tasan halinsa bazai saurareta ba. Tana nan kwance hawaye har sun fara ziraro mata sai gashi ya dawo hannunsa riƙe da kwalin yogurt. Ajiyar zuciya ta sauke mai sanyi, kafin ma ya ƙaraso ta miƙe zaune. Kusa da ita ya zauna yana wani ciccin magani shi adole har yanzu haushinta yake ji. Da taimakonsa tasha madarar, ganin ta ɗan samu ƙarfi duk da jikinta akwai zazzaɓi sosai babu tausayi ya shiga neman hanyar cimmata. Sunyi nisa sosai a yanayin da suke ciki babu zato babu tsammani kawai sukaga haske ya karaɗe ɗakin.
Matuƙar firgita Khadijah tai tare da fashewa da kukan baƙin ciki ganin Hajiya Kainaat tsaye a kansu babu kunya babu tsoron ALLAH idonta ƙyar a kansu. Ga Dafeeq baida alamar ɗagata balle nuna firgici da wannan cin zarafi na matar nan. Batama san wani ƙarfi yazo mata ba ta hankaɗesa taja bedsheet ta cikukuye jikinta tana kuka.
Wani irin ihu Kainaat tai musu kamar zata kashesu. “Dafeeq ni zaka cima mutunci ka zubar min da kimata. Tsabar kai tataccen ɗan iska ne kwana na zaka ɗakko ka kawoma wannan kidahuman matar taka ɗan cin amana!! A ɗaura aurenmu jiya matsayin amarya kazo kana ɓarar min da mutunci a wajen wannan jakar da bata san ciwon kanta ba.....”
Wani kalan yunƙurowar ɓacin rai Khadijah dake kuka tayi, sai dai da sauri Kainaat ta dakatar da ita a zafafe. “Ke kuma karki sakamin baki dan banzo kanki ba tukunna, hasalima baki isheni kallo ba kiji ma da matsalar gabanki wawuya kawai wadda ta rako mata duniya. Ya gama jibgarki ɗazun nan amma da yake ke karya ce har ki amince yazo yay yanda yaso dake yanzu da dare. Koda yake banyi mamaki ba, dan kekam na kula bakin iyaye ke ɗawainiya ma dai da ke. Tunda har kika iya haukan kishi da jure zama da wanda ko sha'awar haɗa jini baida buƙatar yi da ke, wanda ke ɓarar miki da ciki domin buƙatar kansa ai kekam sai a shafa miki lafiya. Wlhy kikai wasa wataran janki zai a tsakar anguwa a titi ya yardama bola ƙaramar daƙiƙiy......”
“Kainaat!!!”.
Dafeeq ya faɗa a tsawace illahirin jikinsa na ɓari. Da alama maganganun ta sun masifar shigarsa. Wani kallon banza ta masa ta sheƙe da dariya. “Karka sake min tsawa Dafeeq, danni ba irin wannan bace, a daren nan sai kabar gidan nan kai da ita wlhy. Ƙarya nayi bakai ke zubar mata da cikin ba? Ai gaka gata ka rantse ba kai bane. Ni kuma a safiyar gobe saina kawo likitan da ke baka ƙwayar da kake zuba mata ta sha, bakai kace ɗan iska bane, a kwana ɗaya har kake tunanin nuna min halin maza! To baka isaba kuwa dan a tafin hannuna kake. Ka rabota da iyayenta da yake itama daƙiƙiyace ta yarda ta bika kazo nan kana cutar da ita har kake tunanin babu wanda yasan kanayi. To barima kiji ba zubar da cikin ba kawai har abinda zai hanaki sake ɗaukar ciki ya saka miki, shirinsa ya gama morarki ya watsar yaje ya sake auro dai-dai da shi lokacin ke kin tashi aiki mahaifar ta gama lalacewa, kuma in baki sani ba ki sani a yau ke ya maida wawuya da bata san darajar iyayenta ba shiko yana zuwa duba nashi duk ƙarshen wata, wannan kwana biyun na ƙarshen wata da yake miki ƙaryar Company ya riƙesu su masa aikin gyaran wajen da za'a saka kaya ƙarya yake ganin iyayensa yake zuwa yi. Wannan kaɗanne daga jaridar yarinya idan kina son sabon labari ki ƙara shiga gonata. Kai kuma zaka zo ka saman ne, zan tabbatar maka akwai banbanci tsakanin Kainaat Usman da wannan ballagazar matar taka da bata san ciwon kanta ba ƴar rakiyar mata duniya”....

🤔🤔Tofa
__________★
Chapter 24 · 0% Book details