Sashe 3
Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
_Alhamdullahi inata alƙawarin gareku na yin free book ALLAH bai ƙaddara hakan ba sai yanzu. To Amin afuwa gani zan cika alkawarin in sha ALLAH. Ina fatan wannan littafi zai ƙawatar da ku tako wace fiska, cakwakiya, nishaɗi, ƙalubale, ƙaddara, son zuciya, kai abubuwane da yawa ya wawuso tako wace fuska, zakuma ku fahimci saƙon da yake son isarwa, dan salon na musamman ne, idan nace na musamman ina nufin na musamman a gaba ɗaya musamman ɗin😉👌.
*Kumuje zuwa gidan ango muji yaya zai ƙare da wannan daren farko nasa, dan naga na musamman ne fa 🚴🚴🚴😆😆🤫🤫.*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na biyu_
........“Ai babu gurin zuwa, saboda da hannunka ka rufe duka ƙofofin guduwar Mr JJ ango mijin amarya Alimah”. Muryar da baya jin zai manta a rayuwarsa ta ratsa kunnuwansa. Dauriyarsa ta ƙare, hakama ƙarfin halinsa ya kai ƙarshe. A take jikinsa ya fara rawa kar-kar. Gashi an riƙesa irin riƙon da ko numfashin kirki ya gagara yi. Jin saukar numfashin mutum a fuskarsa ta saka shi buɗe idanunsa da sauri. A matuƙar razane ya fasa gigitacciyar ƙarar data ɗauke numfashinsa gaba ɗaya sai gashi ƙasa wanwar a sume.....
A firgice ta buɗe idanunta itama tamkar wadda aka farkar da ga nannauyan barci. Waige-waige ta fara ƙirjinta na wani irin luguden daka. To ita yaushe ma barci ya ɗauketa ne, ba yanzu babu jimawa suka shigo ɗakin nan tare da angonta JJ ba. Dan fitarsa babu daɗewa rakkiyar abokansa ko cikakken minti biyu baiyi ba ya dawo, batama jin yabar jikin ƙofar falon. Cike da zumuɗi da aka san duk wani ango da shi ya koma ya zauna inda ya tashi a kusa da ita. Batare da yayi magana ba kawai ya jawota jikinsa ya rungume yana shinshinar wuyanta. Kunya ta sakata shiga wani yanayi, a take jikinta ya fara mazari ta shiga noƙewa. Dariya ya sakar mata cikin kunne da faɗin, “Ai yau dai kunya ta ƙare Love, miya rage kin zama matar JJ, JJ ya zama mijinki. Please ki ajiye wannan kunyar da safe ƙya maidata dan kin san yau ɗin ta musamman ce fa”.
Bata iya tace da shi komai ba, dan a matsanancin tsorace take ga kuma kunya. Sai dai hakan baisa ta hanashi yin yanda yaso da ita ba. Bayan ya gama shinshinar ta ne da rungumeta ya ɗakkota cak zuwa wannan ɗakin yana faɗin, “Yanzu dai muje muyi sallah kafin komai ko. Dan nasan matar tawa ustaziya ce”.
A karo na farko ta sakar masa murmushi, tare da tura kanta a jikinsa dan kunya takeji matuƙa kamar me. Dan tunda take a rayuwarta bata jin wani ya taɓa riƙe mata hannu, sai a jiya wajen dinner da JJ ya aikata hakan gareta. To ita dai tasan sun shigo ɗaki, daga haka kuma bata san miya faruba sai ƙarar ihun nan da bata san daga ina ya fito ba da ya farkar da ita, a yanda kuma taga kanta alamu sun nuna barci tayi. Gadon ta sakko da sauri, sai kuma tai tsamm ta dakata saboda jin motsin ruwa a toilet ɗin ɗakin, hakan na nufin JJ na ciki kenan. Numfashi ta ɗan sauke a hankali, tare da komawa ta zauna tana gyara mayafinta, zuciyarta na tabbatar mata wanka ya shiga kenan, ita kuma barci ya ɗauke ta, ihun da taji kuma maybe a maƙwafta ne. To amma abin mamakin anan taya tayi barcin? Haka cikin ƙanƙanin lokaci? Rashin amsa ya sakata ɗan sauke numfashi kawai.. dai-dai nan JJ ya fito a toilet ɗin babu alamar wanka yayi sai dai ko alwala. Kanta ta duƙar ganin ita yake kallo, shi kuma ya saki murmushin da har ta iya jiyo sautinsa da ga inda take tare da faɗin, “Naga a takure kike, jeki falo ki jirani”.
Kamar mai jiran jin hakan ta mike zumbur, har harɗewa take wajen fita tana mai sauke ajiyar zuciya, sai dai mamaki fal kanta dan sai take jin kamar wani banbarakwai hakan nan....
(Bake kaɗai ba amarya, ni kaina fa man kai na ya tsiyaye. Dan na gagara fahimtar komai, shin JJ ɗin ne ba mutum ba ko ke kanki? Masu karatu ko akwai mai amsa min?🥱😆🚴).
★★.....