← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 82

Sashe 71

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

........Murmushi Nadwa tayi, sai kuma ta gyara kwanciya a jikin Doctor Giɗaɗo tana faɗin, “Ni dai shawara zan baki kamar yanda na saba. Kainaat ki nema iyayenki ki koma garesu, dan in dai Abaan ne ya miki nisa, kamar yanda yaƙi yarda da tayin aurena da naketa jelan masa, kema wlhy sai dai ki rasa dan ya miki nisa. Nisa irin na tsakanin samaniya da ƙasa. Shiyyasa nake ta fargar dake. A yanzu haka yana tare da ƙyaƙyƙyawar matarsa a gidansa cikin aminci da kwanciyar hankali. Dan haka ki riƙe shuga boy ɗinki yafi miki. Nasan zakiyita tunanin mune kuwa. Humm mune ɗin dai, a tunaninki bazan taɓa jin kishi a raina ba ne. Kefa ba ƴar kowan kowa bace. Mune mika ɗauke ki muka suturtaki da sutura ta ƙawa, muka kaiki ƙasar waje kikai ilimin da ya fiddoki har irinsu Abaan ɗin suka kalleki. Saboda mu ahalinsa suka yarda ya aureki ma. A tunaninki banda zuciyar da zanji a raina ni ya kamata na samu wannan bake ba. Nice fa keda komai ɗin, amma sai kika koma komai a kaina. Shiyyasa nai alƙawarin sai kin gama tattara mana mu kuma muji daɗin, dan na lura sam ke ba ƴar halak bace ba baki san halacci ba. Akwai fa lokacin da har gwadaki nai nace ki aramin 10mil zan fara Business amma matar nan kika nuna min baki da shi, ashe ƙarya kikeyi sai daga baya na gane hakan. Hummm kar dai na cikaki da surutu maybe idan kin haihu zan zo suna, ko in matar Abaan ta haihu nazo miki barka, a gaida angon jego Dafeeq byeeeee!🖖”.
      Ba Kainaat ba hatta shi uban gayyar jikinsa kakkarwa yake yi. Jin hajijiya na neman yadda shi ya wani zube a kujera. Dai-dai nan Kainaat ta fita gabansa. A bazata ta ɗaukesa da wani kalar wawan mari irin na bazatan nan. Domin kuwa bai tsammani zuwansa ba sai saukarsa yaji. A gigice ya ɗago, ta kuma sake ɗaukesa da wani haggu da dama. Rikicewa yay har kunnensa na masa wani dommmm.
     Nuna shi tai cikin fashewa da kuka ta ce, “Matsiyaci ɗan mage baka daɗin goyo. Azzalumi tsinanne, ashe da kai ma aka shirya komai” ta sake kai masa wani dukan. Gam ya riƙe hannunta yana huci, yanda nata jikin ke tsuma haka nashi keyi. Cikin rufewar idanu ya shiga kaimata duka tako ina. Ƙarfin mace da namiji ba ɗaya ba koda ace ta girmesa. Amma duk da haka tayi ƙoƙari itama ba kamar Khadijah ba. Dan duk abinda taci karo da shi wawusowa take tana ƙwala masa. Cikin ƙanƙanin lokaci sukaima kansu jina-jina. Sai da maƙwafta suka shigo aka rabasu anata mamakin yaushe ma suka zo gidan tunda ansan yanzu Dafeeq ɗin yayima gidan ƙaura. Tuni kuma an garzaya an sanarma Baba Hakimi abinda ke faruwa.
     Yanda suka jigata juna da raunika yasa dole suka nufi asibiti da su. Baba Hakimi kuma ya hana a sallamesu a ranar dan yamma tayi sosai sai washe gari. Da farko daya tambayesu abinda ya haɗasu shiru sukayi, sai dai bafade ya musu tsawa sannan Kainaat ta shiga zayyane komai tana kuka. Dan a ganinta mafitar da zata rabu da Dafeeq ɗin ce ma tazo mata. Sai dai me, maimakon samun yanda take ai nasiha Baba Hakimi ya musu. Batare daya kawo komai a ransa ba ya ce, “Kai Dafeeq in ma Khadijah ce ka kwantar da hankalinka. Dan yanzu haka tana gidan mijinta tai aurenta. Garama ka riƙe matarka ku zauna lafiya ku kuma ɗauki abinda ya faru matsayin ƙaddara. Dan kai da ita ɗin duk CUTA TA ƊAU CUTA ce kawai”.
        Tashin hankali kenan. Dan yanda Dafeeq ya miƙe zambar yana ɗura ashariya sai ma ka ɗauka ya haukace. Fadawa zasu saka a masa duka Baba Hakimi ya hana. Sai dai ya saka an fiddashi a fadar. Aiko a ɗimauce ya nufi gida ya fara haɗa kayansa sai Kano. Wannan al'amari ya sake haukatar da Kainaat, dan duk wanda ya ganta a ranar sai ta bashi tausayi. Kamar ba Kainaat ɗin nan ƴar gayu ƴar ƙwalisa mai ji da kuɗaɗe a gidan sanyi ba. Ta harmutse, ta hargitse, ta gama fita a hayyacinta abun ba'a magana....

       A haukace Dafeeq ya iso Kano, sai dai kuma ya samu amsar da yaji inama bai zo ba. Dan ta tabbata dai Khadijah tayi aure. Yanda ake zuzuta masa labarin ta auri wani babban mutum mai kuɗi a Abuja ya nema saka zuciyarsa bugawa. Sai ga Dafeeq da kwanciya ciwo rejiff. Mamansa taso wannan karon ma taje tayi tujara a gidan su Khadijah baban Dafeeq ɗin ya taka mata birki da tuna mata gargaɗin d.p.o, dole ta haƙura ta cigaba da tsine-tsinenta a cikin gida kawai.
     Washe gari sai ga Kainaat itama ta iso Kanon kamar sabuwar kamu a hauka. Ta tada musu hankali akan sai fa Dafeeq ya saketa. Babansa yace idan har ya saketa sai ya saki mamarsa shima ya kuma tsine masa. Ai sune dai-dai da juna dan haka su cigaba da kasancewa a tare. Dan kuwa a haukar Kainaat ta kwancema iyayen Dafeeq ɗin komai ne wai dan su sakashi ya saketa. Sai kuma ta ɗaure kanta da kanta. Da farko itama Maman Dafeeq ta ce ya saketa jin kuɗi dai babu su. Sai dai furucin mijinta ya gigitata. Sai kuma cikin da Ƙainaat ke ɗauke da shi ya sake saka jikinta yin sanyi, dan duk duniya kuma babu abinda take buƙatar gani a yanzu sama da jinin Dafeeq ɗin. Wannan shine sanadin zaman Kainaat da Dafeeq a Kano dan su duka biyun ciwo ya kwantar dasu. Ita laulayi shi jiyyar zuciyar rasa Khadijah. Akwai randa harda su aman jini, sai da aka garzaya da shi asibiti. Kusan satinsa uku sannan aka sallamosu. Itama jikin Kainaat ya rikice, nanma suka garzaya asibiti, sai ake sanar musu ai cikinta a bayan mahaifa yake, dole sai sun lura da bata kulawa har lokacin haihuwa a ciresa ta hanyar cs dan yana cikin ƙoshin lafiya. Ina kainaat ta birkice musu akan sai dai fa a cire ciki, dan wata ƙawarta data samu irin hakan cire mata akayi tun yana wata uku. Anta tafka bala'i Dafeeq da Mamarsa sukace bazasu yarda ba, daga ƙarshe dai sai da aka dangane da police station, acan ne aka musu iyaka. Babu yanda zatayi dole ta haƙura dan bata da gurin zuwa yanzu, saboda satinta ɗaya da zuwa Baba Hakimi ya lodo kayansu a mota da ƴan rakiya aka kawo Kano. Acewarsa ya amshi gidansa Dafeeq ya cigaba da zama a gidansu. Dole fa aka share musu ɗakin ajiye-ajiye na gidan suke zaune anan. Idan fatara ta ishesu a zari wannan a siyar, a cire wancan a siyar, wataran ma Maman Dafeeq ɗin ke sata ta sayar basu sani ba. Dama dai kayan Ƙainaat ne masu daraja a ciki. Ga faɗa kullum kamar kaji. Yanzu basa jin nauyin ɗaga hannuwa su shararama juna mari. Saboda yana marinta itama take ware hannu ta sauke masa. Sai in zasu harƙume dambe ne Babansa ya tsawatar tare da tuna musu lalurar dake jikin Kainaat ɗin....
      __________★

         Yau ta kasance weekend, dan haka tun kusan sha biyu Abaan da Khadijah suka fita domin ɗan hutama ransu. Tunda aka kawota bayan asibiti babu inda ta taɓa zuwa sai yau. Yawo yayi da ita sosai wajaje daban-daban da suka nema juye kan Khadijah ta sake tabbatar da ganin Abuja yafi jinta ma. Dan wani wajen ma idan suka shiga ita mantawa take Nigeria ce fa. Bata wani ɓoyewa taita santi abunta da nuna al'ajabinta. Shiko Abaan na mata dariya da tsokanarta wai baƙauya. Sunsha hotuna, dan duk inda akeje cewa take suyi hoto dan ta nuna ma su Ni'ima. Tun yana tayata shikam harya gaji ya miƙa mata wayar tasa ta cigaba da ɗauke-ɗaukenta. Sai yamma lis suka dawo gida a gajiye. Washe gari kuma yace ta shirya zai fara koya mata mota. Jitai kamar ta suma a zaune dan sai da ya taɓata tai firgigit. Muryarta har rawa take ta ce, “Hamma mota fa?”.
      Murmushi ya sakar mata mai sanyi, sai kuma a hankali ya kwanto da kansa saman cinyarta. Hannunta ya kamo yasa a ƙirjinsa ya rungume. “Ko jirgi kike son koya zan kai ki a koya miki na sayo miki shi Khadijah. Kin san waye mijinki kuwa. K dai kawai kiyita bani farin ciki wlhy zan zame miki fiye da bawa. Ba koyan mota kawai ba, nan da sati uku zaki fara zana waec ɗinki in sha ALLAHU. Dan ina son ki samu kwalin Sakandire sai mu tattara inamu-inamu mu koma abroad ki cigaba da karatunki har sai kin kammala zamu dawo. In sha ALLAHU sai kin gogema iyayenki hawayen da kika sakasu zubarwa a shekarun baya. Sai kin zama abar kwatance. Yanda mutane da dangi suka dinga jifanki da ALLAH wadai a shekarun baya sai sun koma sanya miki albarka. Yaron nan daya zaluntar min ke sai kin koma kece mai taimakonsa a rayuwa. Fatana ni dai ki zama mai gaskiya, mai amana, mai kuma jajircewa......”
      A hankali hawayen da suke kwaranyo mata suka shiga ɗiga a kan fuskarsa. Murmushi ya saki tare da kai hannu ya share mata su. Sai kwai ta rungume kansa ta saki kukan mai ƙarfi. Tashi yay camak ya ɗauketa yay bedroom da kayarsa. Daga haka labarin ya canja salo...
Chapter 71 · 0% Book details