← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 82

Sashe 59

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

......Zama tai a ɗan takure, sai dai a bazata taji ya saƙalo hannunsa ta bayanta ya kwantota saman kafaɗarsa, batare da ya sake magana ba ya cigaba da aikinsa. Ta jima idanunta a runtse dan kunya, kafin ta buɗesu a hankali tana kallon abinda yake a laptop ɗin. A haka masu aikin Mamy da suka kawo mata abincin sukai sallama. Zata tashi ya sake maidata yana amsa musu sallamar, sai kuma yace su shigo. Kamar Khadijah zata fasa ihu dan kunya, amma shi sai taga aikinsa ma kawai yake. Ta gefen ido ta kalla masu aikin, sai taga tunda suka musu kallo ɗaya basu sake yi ba. Ko gaishesu da sukai kawunansu a ƙasa suke. Shi hannu ma kawai ya ɗaga musu, sai itace ta amsa musu. Koda suka shiga kitchen ɗin ma suka fito sam basu kallesu ba har suka fice, a hankali ta sauke ajiyar zuciya har yana iya jinta. Sai dai baice komai ba face ɗan murmushi daya saki kaɗan ya cigaba da aikinsa. Kusan awa ɗaya suna a haka, tun tana noƙe jikinta harma ta saki wani barci-barci ya fara rinjayar idanunta dan ƙamshin turarensa ba ƙaramin ratsata yake ba da saukar mata kasala. Laptop ɗin ya rufe ya ajiye tare da sauke ƙafafunsa dake a table ƙasa. Sai kuma ya ɗan kalleta yana mai kai hannunsa saman fuskarta ya shafa. Firgigit ta buɗe idanun, ganin yanda fuskarsa ke gab da tashi ga hannunsa akan tata fuskar ya sata ɗaga kanta a kafaɗarsa da ɗan sauri.
“Da'alama kin gaji da yawa, ansha rawa wajen party shekaran jiya ko?”.
Juyowa tai da sauri batare data tuna dawa ma take maganarba, idanunta a ɗan ware bakinta na nuna alamun ƴar shagwaɓa ta ce, “Ni wlhy bana rawa, kuma dai ai kowa yasan banyi ba”.
Wani irin harmutsawa jinin jikinsa yayi saboda yanda tayi ɗin, ga idanunta sun sake wani haske har ƙyalli suke, baƙin ya ƙara baƙi, lips ɗinta sun ɗan tattare kaɗan. Samun kansa yay da jinjina mata kansa, idanunsa na a cikin tsakkiyar nata idanun, kamar mai raɗa ya motsa lips ɗinsa kaɗan. “Uhmm nima shaida ne bakiyi rawan ba, amma yanzu zakiyi min nawa a ɗaki ko....”
“Rawan!”.
Ta faɗa cikin ƙara waro idanunta sosai waje, irin nuna alamun matuƙar mamakinsa ɗin nan.
A wani irin sake kasancewa a kasalance ya jinjina mata kansa yana lumshe idanunsa da buɗewa cikin nata ya furta, “Uhhumm Baddo”.
Kamar wadda aka maido hayyacinta ta miƙe zabar, sai kuma cikin sassarfa ta nufi barin wajen da bashi amsa muryarta na rawa. “Ni ALLAH bana rawa”. Wuff ta shige ɗan lungu bedroom ɗin ta. Murmushi mai bayyana haƙora ya saki, sai kuma ya taune lips ɗinsa da ƙarfi yana ɗan kaima kansa ƙaramin mangari ya ce, “Abaan kai ɗin nan ko”. Sai kuma ya sake sakin murmushin da komawa cikin kujerar ya wani lafe. Shi gaba ɗaya ma ji yake yana neman rasa control ɗinsa akan yarinyar nan. Anya Ibrahim da Adams ba saida suka tofeshi ba kafin su kawo wannan batun ga Mamy. Abin da mamaki fa, sam mantawa yake da cewar Khadijah ta taɓa aure kafin shi ɗin, kallon wata ƙaramar yarinya budurwa sharaf yake mata, koda yake yarinyarce ai, 20years fa, ko ƙanwarsa daya bama shekaru masu tazara sosai ta girmeta fa. Ai dami a kala kawai ya tsinta...
Chapter 59 · 0% Book details