Sashe 40
Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Matuƙar mamaki da ruɗani Kainaat ta shiga a washe gari, dan bata farka ba sai washe gari. Ta dinga kallon Dafeeq da yay fuska abinsa, sai dai ta gagara cewa komai. Ko salla batayi ba sai da tai kiran Nadwa. Sai dai ta yi shuka a idon makwarwa batare da ta sani ba. Dan duk abinda ta tattauna da Nadwa shima ya jisa. Dan haka tana gama wayar ya fara borin kumya sakamakon yin wani tunani. Exactly yanda yaji sun tattauna akan halin da malamin yace zai tsinta kansa a ciki ya fara gwadawa. Kafin wani dogon lokaci faɗa ya harƙe tsakaninsu. Ranta fes da farin cikin tunanin aiki yaci. Dan haka itama ta fuske ta biye masa kamar yanda malam ya bata shawarar kunnashi. Al'amarin kamar wasa sai ya zama gaske sakamakon fahimtar da tai babu wasu muhimman abubuwanta data adana a ɗakin a washe garin cikarsa kwana biyu da dawowa gidan. Dan faɗa sosai sukeyi ta buƙaci ya bata abubuwanta. Shi ko bai musa shine ya ɗauka ba dan kai tsaye ma har takai shi da tabbatar mata idan tana son saki sai ta bashi sauran takardun Companyn ta. Idan kuma tai tunanin sanarma wani shima zai sanarma Abaan ɗin da take harin komawa komai, ya ɗan balgata mata wani sirrinta daya ɗauka a cikin waya daya shafi Abaan ɗin.
Matuƙar tashin hankali Kainaat ta shiga. Gaba ɗaya ma ta rikice. A take ta shiga bincike sosai a ɗakinta. Tako samu ya yashe komai harda kuɗin dake a cikin bank nata duka biyu. A takaice dai bata da wani ƙarfi ma da take tunani na dukiya da zaisa ta iya masa rashin mutunci ko gayyato hukuma cikin al'amarin nasu. Sannan maganar zai kaima Abaan wani yankin sirrinta ma wani tashin hankali ne gareta da bazata taɓa fatan ya kasance ba. A cikin ƙanƙanin lokaci komai ya canja a gidan. Ta fahimci hatta wayarta idan tai kira ko aka kirata shima tana zuwa cikin tashi wayar. Sai ma tarasa ina zata kama taji daɗi. Gashi ƙiri-ƙiri ya kulle ƙofar gate yama sallami Dauri maigadi da kuɗi masu yawa wai yaje ya huta zai nemesa. Yayi magana da Manager na Companynta da wayarta cewar a cigaba da al'amura shi da Madam sunyi tafiya zuwa Lagos honeymoon. A haka suka kwashe sati ɗaya a gida babu wani cigaba sai na tafka rikici da masifa. Kowa kuma yaƙi zuwa gidan sakamakon bin duk wanda yasan zai iya nemanta a waya ya tura masa text message cewar sun tafi honeymoon sannan ya kashe wayar ma gaba ɗaya. Tayi masifar tayi zagin tayi kurarin amma yaƙi bata wayar. Ta nema iya nema amma ta kasa gano a inda ya ɓoye. Shi kuma wayar hannunsa babu ma wanda yasan layin sai iyayensa kawai balle wani ya kirashi yasan suna gari. Tun Kainaat na ɗaukar al'amarin wasa harta fahimci yafi ƙarfin wasan fa yaron nan da gaske yake shirin mata ɗibar albarka yake da gaske. A yau suna cikin rikici ta maresa ya rama. A take dambe ya nema harƙumewa a tsakaninsu. Sai dai ƙarfin mace da namiji ba ɗaya ba, ya bubbugeta dan Dafeeq dai akwai zuciyar banza. Sannan duk da ƙananun shekarun nan nashi baya ƙaunar raini kowa ya sani tunma bai kai haka ba. Itama dai ta samu nasarar ƙwala masa plate a goshi harta jimasa ciwo. Hakan yasa shi nufar bayi domin wanke jini batare da ya lura da wayarsa data faɗi ƙasa ba. Yana shiga kira na shigowa, dan haka Kainaat ta ɗauki wayar da sauri, a mamakinta sai taga mamansa ce. A take zuciyarta ta bata shawarar ɗagawa, dan ta fara zargin lallai uwar tasa tasan komai dake faruwa tunda ita kaɗai ke kiransa a layin nan sai babansa. Ɗakin da Khadijah ta zauna ta shiga, ta maida ta kulle ƙofar sannan ta ɗaga wayar tana gab da tsinkewa. Tana kaita kunne Maman Dafeeq na kwaɗa sallama.......
____________★