← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 82

Sashe 57

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kamar yanda Dafeeq ya buƙata Kainaat ta amsa da hannu biyu kam, dan akwanikan nan da suka gabata suna zaune lafiya sai dai ta ciki na ciki. Yanda yay alƙawari ya dawo mata da duka takardunta, hakan ya sakata jin matukar farin ciki har wani sashen zuciyarya na mata kokwanton anya kuwa bada gaske Dafeeq keyi ya zubar da makamansa ba? Sai dai wani sashe na kwaɓarta da hakan kuma. Dan haka ta cigaba da saka masa ido kamar yanda ta shirya masa, tare da fara aiwatar da plan ɗinta itama.
Idan ka gansu a yanzu zaka ɗauka wasu masoyan arziƙi ne. Dan kowa na ƙoƙarin ɓoye mummunar manufarsa akan ɗan uwansa. A zukata kam da wahala a haɗu ba'a zagi juna ba. Kullum tare suke zuwa aiki su dawo. A gidan ma suna manne da juna ko yaushe. Kamar yanda ya saba zuwa gida Kano duk ƙarshen wata wannan watan ma yay shirin hakan. Harda yima Kainaat tayin ko zataje. Kamar tace a'a sai kuma ta canja shawara tace da shi zataje. Sun gama shiri tsaff tun a daren jiya yau da safe ta wayi gari da ciwon ciki mai tsanani. Hankali a tashe tun asuba suka nufi asibiti, tako samu kulawar gaggawa kasancewar likitan nada alaƙa da Abaan, dan kusan ma shine silar saninshi da tayi. Bayan sun rabu kuma bata daina zuwa wajensa ba, shi kuma bai taɓa tunanin bama sa tare da Abaan ɗin ba tunda alaƙar likita da maralafiya ce kawai ta haɗasu. Ko aure da yasamu labarin yayi a kwana uku da ya wuce wani abokinsa ne ke faɗa masa, shine ma ɗazu yay kiransa ya tayasa murna. Ganin Kainaat kuma a yanzu ta sashi tunanin toko suna ma a Adamawa ne anan akai bikin? Sai dai yayi mamakin ganin wanda ya kawota dan shi Awwal kawai ya sani makusancin Abaan dakan iya kawo matarsa ko ƙanwarsa ko Mamansa asibiti. Amma dai sai baice komai ba ya shiga bata kulawa yanda ya kamata. Har kusan azhar sannan ya sami nutsuwar zama, result ɗin gwaje-gwajen daya bada amata aka kawo masa. Cike da farin ciki da zumuɗin ganin abinda sakamakon ya bada ya shiga laluben neman Abaan a waya batare da yayi tunanin fara magana da wanda ya kawota ba. A kiran farko ba'a ɗaga ba, sai baiyi tunanin komai ba tunda yasan Abaan da sabgogi. Kusan mintuna goma tsakani sai ko ga kiran Abaan ɗin ya shigo masa. Fuskarsa ɗauke da murmushi ya ɗauka tare da rangaɗa sallama ta girmamawa.......✍️

_😂Kai dai wannan likita sam baka da man kai gaskiya_

Ina kuke manyan mata da hajiyoyi munsamar muku sauqi Ina masu shaawar futa Egypt karatu ko yawan bude ido to gadama tasamu kaidai kawai kaiwa wannnan number magana 01017018846

Ba nan ummu khalifa ta tsaya ba tana kawo original Egyptian abaya da shoes da duk abinda mutum keso tana kawowa zuwa gida Nigeria

Ummu khalifa 01017018846

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na talatin da biyu_

____________

*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥

*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_

*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*

*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*

*TSUTSAR NAMA Billynabdul*

*GUDUN K'ADDARA Huguma*

*AMEENATU Mamuhghee*

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

___________

.......Alhamdullah ƴan rakkiyar amarya da wasu a dangin ango duk sun wuce. Sai gidan yayi tsitt kasancewar babu mai yaro a wanda suka rage. Kuka sosai Khadijah tasha a sashenta daya rage babu kowa sai ita kaɗai. Mamy dai ta tura mata masu aiki sun gyara ko'ina tsaf. An kuma kai mata abincin rana. Sai da akai sallar la'asar kuma sai ga Noor da baƙi ƙawayen Mamy. ALLAH yasota babu jimawa tai wanka. Dan ɗan barcin da tayi bayan ta gama kukanta yasata jin nauyin jiki, shine ta watsa ruwa lokacin data shiga yin alwalar la'asar. Cikin girmamawa take gaida ƙawayen surukar tata. Wayayyun mata ƴan boko da naira ta gama nuna kanta a jikinsu. Duk da acikin su akwai wanda sukaso Abaan ya auri ƴaƴansu hakan bai hanasu yaba ƙyawun Khadijah da nutsuwarta ba. Sun kuma tabbatar da Abaan ɗin ya samu dai-dai shi a yanzu ba irin Kainaat ba mai buɗaɗɗen ido sa'ar shekarunsa. Haka dai suka fito suna sambarka da ambaton masha ALLAH. Koda Noor ta musu rakkiya nan wajen Khadijah ta dawo ta ɗan tayata zama, dan ɗazun dama tazo ta samu tana barci. Hakan yayma Khadijah daɗi sosai, dan ta rage kewa, sannan Noor ɗin ta taimaka mata sun gyaro sashen Abaan kamar yanda ta bata shawarar suyi. Sai gab da magrib ta koma nasu sashen, tabar Khadijah da kewa da zullumi. Dan ji take kamar tai tsintsuwa ta koma Kano, sai dai kuma tasan bakin alƙalami ya riga kuma ya bushe.....

_________★

Ƙarfe biyar da kusan rabi motarsa ta shigo gidan. Kamar kullum yana tare da Awwal. A yanda ya fito motar a kasalance zai sa ka fahimci a gajiye yake. Dan hatta ƴar saman suit ɗinsa riƙe take a hannunsa ya ɗan sagalata a kafaɗarshi. Kai tsaye sashen Mamy ya nufa, ya bar Awwal na tattare masa tarkacensa kamar yanda ya saba.
Sassanyan muryarsa ta fargar da su Mamy dake hira zuwa garesa. Duk da tunkan ya shigo dama ƙamshinsa ya musu sallama. Cike da girmamawa ya gaida gwaggonninsa biyu da suka rage basu wuce ba. Sai wasu mata biyu da suma suka gaishesa cikin girmamawar. Sai Noor da itama ta gaishesa, sannan shima ya maida hankali ga Mamy dake binsa da kallon tausayi, dan gani taima kamar ya ɗan rame mata yau ɗin. Amsa masa tai da kulawa, tare da ɗorawa da faɗin, “Baffah kaci abinci kuwa yau ɗin nan?”.
Murmushi yay mata mai sanyi, sai kuma a hankali ya ce, “Mamy naci snacks da drink....”
“Baffah na drinks da snack aiba abinci bane. Shiyyasa naga ka rame min a ido wlhy. Kaga maza jeka wajen matarka an kai muku abinci dan ALLAH ka zauna kaci, sannan itama ka tabbatar taci kaga baƙuwace ita”.
Murmushin ya sake yi nan ma yana miƙewa, sallama ya musu ya fice dan shima dai yasan yana matuƙar buƙatar hutawar kam...
Chapter 57 · 0% Book details