Sashe 30
Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Headphones ɗin data saka ta cire kunne ɗaya kaɗan dan taji koya haƙura ya tafi, a zabure ta miƙe jin yana dukan abu kamar mutum yana zage-zage. Abinka da dare gaba ɗaya gidan amsawa yake yi. Bama tasan sanda ta zabura zuwa ƙofa ba ta buɗe. “Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un ” ta ambata jikinta na rawa idanunta gaba ɗaya a waje. Ganin fa da gaske zai iya kashe yarinyar mutane a gidanta ya ja mata masifa tasa dukan ƙarfinta wajen hankaɗashi gefe da faɗin, “Kai ko kanada hankali yaron nan? Kasheta kake son yi ne?”.
“Yaro yana bayan uwarsa ke kuma! Idan na kashetan miya shafeki? Ko kinada alaka da ita ne?”. Ya faɗa a zafafe.
“A'a ALLAH ya rabani haɗa alaƙa da wannan. Kai dai da kaji ka gani kaita kaya. Amma maganar gaskiya bazakai min kisan kai anan ba. Ɗaukarta ku koma inda kuka fito idan ka gadama ma kayi bandarta bai daman ba. A gidana ne dai baza'ai kisan kai ba dan babu mai sakani a masifa ina zamana lafiya.”
Harara ya zuba mata jikinsa na tsuma, ji yake tamkar itama ya rufeta da dukan ma. Sake watsa mata hararar yay da yarda belt ɗin hannun nasa ya shige ɗakin data fito. Itama hararar ta raka bayansa da ita, kafin ta nufi hanyar ƙasa dan ita kam bataga dalilin da zaisa ta bari su kwanar mata gida ba, musamman ma Khadijah dake nishin mutuwa. Babu jimawa sai gata ta dawo da maigadi. Khadijah dake kwance a sume ta nuna masa. “Kaga ɗauketa ka fitar min da ita a gida, inda ma zaka taimakan ka kaita can bakin titi dan ALLAH tunda ba wani nisa bane”.
Cike da tsoro maigadi ya ce, “Hajiya bakin titi yanzu a daren nan, idan aka kamani fa? Karki manta mace ce fa wani ma sai ya ɗauka fyaɗe namata ai”.
“Bamu da wani zaɓi ai Dauri sai wannan. Dan wlhy kaga wannan yarinyar ta mutu a gidan nan kaima bazaka sha ta daɗi ba. Inada dukiyar da zan iya tsallake ƙasar nan batare da ansan ina naje ba. Wannan mahaikacin dana jajiboma kaina wlhy a daren nan zai iya haurewa yabar garin nan shima faɗamin wanene a ruwa?”.
Rawa jikin Dauri maigadi ya fara, dan tabbas gaskiya Hajiya tafaɗa. Shiko idan hakan ta kasance ai ya shiga uku. Kwata-kwata watansa na biyu kenan da yin aure. Amaryarsa nacan ya baro a ƙauyensu. Kuma Hajiya tasan garinsu koya gudu zata iya saka ƴan sanda su bishi. Ɗaff ya raba Khadijah da ƙasa cikin karkarwar jiki yay sauka zuwa ƙasa. Har cin tuntuɓe yake ga nauyin mutum ko yace gawa dan a yanzu Khadijahn bata da banbanci da hakan. Yana sauka Dafeeq na buɗe ƙofar ya fito, takarda ya jeho batare daya kalla sashen da yabar Khadijah ba. “Karna tashi na ganki a gidan nan da safe. Kije na sakeki saki. Abinda zaki tarar acan ɗin ma ya isheki daga ke har iyayen naki wawuya kawai ƴar iska. Ai ba'a haifi macen da zata maran ta zagan na barta ba, idan kina tunanin kinyi na farko kinci riba yanzu bazaki cita ba kuwa. Dolene kije ki ɗanɗana hukunci mafi tsauri dan nasan rabuwa dani shine mafi girman bala'i a rayuwarki, sai dai ki wuce Legas ki kama ɗaki matsayin karuwa dan waɗan nan iyayen naki masu kama da kafiran farko musamman ubanki ba sake kallonki zai ba”. Daga haka ya koma ciki tare da bugo ƙofar da ƙarfi har sai da Kainaat da ke tsaye galala tana kallonsa da saurarensa ta zabura. Takardar ta ɗauka, cikin matuƙar mamaki ta ware idanunta, dan kuwa da gaske sakin ne har biyu ya rubuta. Ita dake shirin aje mata wajen malami akan hakan sai gashi ta samu cikin sauƙi haka. Kai gaskiya ita ɗin ƴar baiwa she ma to. Wani shegen murmushi ta saki mai ƙayatarwa da sanyaya zuciya, babu tausayi ko ɗar a ranta ta sumbaci takardar da kashe ido ɗaya ta ce, “Kin zama labari a tarihin rayuwar Kainaat Khadijah. Karki damu nima kwanaki biyar ya ragen na biyo bayanki, sai dai banbancina da ke ni wajen mijina masoyina abin alfaharina zan koma”. Dariya ta saki, sai kuma ta dafe bakin da sauri ta sauka ƙasa da gudu. Ta sami Dauri na ƙoƙarin buɗe ƙofar falo zai fita da Khadijah. Cike da nishaɗi ta saƙala takardar a cikin rigar Khadijahn sannan ta buɗema Dauri ƙofar da kanta ranta fes babu tausayi ko ƙanƙani a ranta....
(Hummm😶).
___________★
Sosai Anoosh ke laulayin cikin nan. Ga JJ yaƙi zuwa har kwanaki biyu sun wuce. Kullum cikin kiransa Hajiya Lailah tare yana kawo mata uziri. Ganin an tafi sati uku baida alamar zuwa ta fahimci yawo kawai yake da hankalinta. Ranta ya sake kaiwa ƙololiwar ɓacin da ta kasa cigaba da riƙe abinda ke ranta ranar tai masa wankin babban bargo a waya. Tare da tabbatar masa saita wulaƙanta rayuwarsa fiye da yanda ya wulaƙanta mutuncin ɗiyarta. Dan haka ya saurari sammaci.
Ko tari JJ baiyi a wayar nan ba yayinda Hajiya Lailah ke masifa, sai da ta gama tsaff yaja tsaki kawai tare da kwashewa da dariya ya ce, “Lallai Hajjaju baki san wanene ni ba kenan. Ni kike tunanin wai ki wulaƙanta? To bissmilla ga fili ga mai doki saura sukuwa. Ƴarki kuma da kike maganar na shiga mutuncinta ki tambayeta ai tare muka ji daɗin, hasalima da kanta take kawo min kanta. Dan haka sai ki shirya wulaƙantani da wulaƙantata dan a tafin hannuna take saboda ni bana ƙwaina sai da zakara Hajiya. Ki duba WhatsApp naki ga saƙonan na tura miki, sannan ki shirya taki wulaƙantar ke da ballagazar ƴarki kafin ki shirya wulaƙantanin kinji. Dan na fahimci kin manta duk abinda NAMIJI yayi ado ne, MACE ita ce cikin ruwa tsundum. Na barki lafiya, idan ta haihu namiji a saka masa sunan babanta, idan mace ne kuma Lailah. Kar kuma a haifamin bebiya dan ALLAH hhhahahah”. Ya ƙare maganar da wata irin mahaukaciyar dariya data saka jikin Hajiya Lailah rawa. Gaba ɗaya ma ita ta kiɗime, tsabar yanda komai ke neman juye mata ta rasa ina zata kama. Da ƙyar ta iya kaiwa zaune ta shiga WhatsApp jikinta na rawa. Gigitacciyar ƙara ta saka mai firgitarwa tare da sakin wayar ƙasa ta sulale a sume. Da gudu Anoosh dake kwance a ɗaki cikin bargo ta fito, zubewa tai gaban mahaifiyarta tana mai kwala kiran sunanta da girgizata. Babu alamar numfashi a tattare da ita, baki ta sake buɗewa zata ƙwala kiran sunanta mararta tai wani kalar masifar ƙullewa. Da sauri ta saketa tare da dafe cikin da duka hannayenta biyu. Azaba ta sata kwanciya ta naɗe jikinta waje gudu hawaye masu zafi na tsiyaya a idanunta. Shirun ta ya sata jiyo sautin muryarta daga cikin wayar mahaifiyarta, sauti ne mara daɗin ji da gigitar ta tunani, duk da azabar da take ciki haka takai hannunta dake rawa da ƙyar ta ɗauka wayar, (innalillahi...) Kawai ta iya ambata a zuciyarta wayar na suɓucewa daga hannunta. Ɗaukewar numfashinta dai-dai da ɓallewar jini da ga jikinta tamkar an buɗe fanfo...