← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 82

Sashe 36

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tunda ta shige gidan suma suka fito a motar. Sai dai Awwal ne kawai a waje shikam yana daga cikin mota ya dai buɗe murfin ne kafafunsa duk a waje. Magana Awwal ya jiyo da nufin masa sai ga Baba an sauke a napep tare da Ni'ima, da ga asibiti suke, ta raka baba amsar magani. Ni'ima na kama da Khadijah sosai, dan haka a kallo ɗaya suka gane ƴar uwarta ce. Baba da tun fitowarsa a napep ɗin ke kallon motar ta su da Awwal ya ƙara so garesu yana mai dogara sandarsa, dan yanzu baya iya tafiya sai da ita. Sallamar Baba ta saka su juyowa su duka garesa. Bayan sun gaishesa yake tambayarsu ko suna neman wani ne?.
Awwal ne ya amsa masa da faɗin “Eh Baba, muna neman mai gidan nan ne”.
Murmushi Baba yay da jin jina kansa. Cike da dattako ya ce, “Ni ne mai gidan yaro. ALLAH yasa dai lafiya ba laifi nayi ba”.
Murmushi shima Awwal yayi, sai dai kafin yace wani abu Yayansa da tun bayan gaisuwa bai sake magana ba ya ƙarɓama Baba da cewa, “A'a Baba bakayi laifin komai ba. Alkairi ne tafe damu.”
“To masha ALLAH. Bissmilla. K Ni'ima shiga ciki ki amso tabarma ko”.
Da to Ni'ima ta amsa masa bayan ta gaishesu. Sai dai tana nufar shiga gidan Yaya ya ce, “Baba bama sai ta amso tabarmar ba. Dan muna saurine”.
Idanu baba ya ɗan zuba masa, dan haka kawai yaron ya birgeshi saboda nutsuwarsa da cikar kamala. Kansa ya jinjina tare da dakatar da Ni'ima, sannan ya sake juyowa garesu yana nuna musu dakalin dake ƙofar gidan. Shi da Baba ne suka nufi dakalin, Awwal na daga tsaye jikin motar. Sai da ya sake gaida baba sannan ya ɗaura da faɗin, “Baba dama muna nemanka ne adalilin wata yarinya datai mana kwatancen gidan nan muka kawota. Mun taho da itane tun daga Adamawa......” tsaff ya kwashe komai ya sanarma Baba, tare da miƙa masa takarda ya ɗora da faɗin, “Wannan a jikinta ta faɗo da alama itama bata san da ita ba”.
A hankali Baba da jikinsa ke tsuma ya ɗago hannunsa ya amshi takardar. Sai kuma yay ƙoƙarin maida hawayen da suka cika masa ido da sakin murmushin ƙarfin hali ya ce, “Nagode yaro, ALLAH yay maka albarka. ALLAH ya kareka da sharrin duk wani abun ƙi. Ban san yanda zan misalta maka jin daɗina ba akan wannan taimako da kukai mata. Amma na maka alkawarin addu'a a gareku a kowace sallata. Zan so kuma ace kumu shiga ciki kusha koda ruwa ne”.
“Kayi haƙuri Baba mun gode sosai. Hakan ma ALLAH ya saka da alkairi. Zamubi jirgin ƙarfe bakwai ne zuwa Abuja shiyyasa. Amma in sha ALLAH na maka alƙawarin watarana zan shigo domin gaisheka.”
Godiya sosai Baba ya ƙara musu da sanya albarka. Sai da zasu shiga mota Awwal ya sauke wasu manyan ledoji yace a bama Khadijah...

Bayan wucewar su Baba ya shigo gidan yara biye da shi da ledojin nan. Har yanzu Khadijah na zube a tsakar gidan tana kuka Jamilah da Kamal na taya ta. Yayinda Ni'ima da Zuhrah da suka kasance kamar sakonta suke tsaitsaye kawai ransu a ɓace. Dan sukam dai sunada wayonsu sosai a lokacin da Khadijah tabar gidan, sannan komai daya faru kafin ta gudun basu manta ba. Mama ko na zaune a yanzu kanta a ƙasa, dan tunda hajijiya ta nema zubar da ita Zuhrah ta taimaka mata ta zauna. Sallamar Baba ta saka Khadijah ɗagowa da sauri, idanu ta zuba masa. A take zuciyarta tai wata irin girgiza tamkar zata fito ta baki ganin yanda gaba ɗaya kamannin Baba suka sauya fiye da mama. Ya rame sosai yayi duhu ga shi yana jan ƙafarsa ga kuma sanda a hannu alamar itace ke taimaka masa a tafiyar. Shima dai kallon nata yake daga sama har ƙasa. Kusan mintuna biyu y kauda kansa batare da yace uffan ba ya nufi tabarmar da Ni'ima tai saurin shimfiɗa masa ya zauna.
Rarrafowa Khadijah tayi har zuwa inda yake tana kuka. “Baba ku yafemin, dan ALLAH na roƙeku ku yafe min. Nasan nayi kuskure babba na bijire muku nabi wanda kansa kawai ya sani. Baba nayi nadama, nayi dana sani, wlhy bazan ƙara ba baba....” kuka mai nauyi ya sake sarƙeta. Maimakon cewa wani abu daga baba sai kawai ya dubi Ni'ima ya ce, “Kubata abinci”. Da ga haka yaja buta da Jamilah ta kawo masa ya fara alwala dan an fara kiraye-kirayen sallar magrib...

__________★

METAFORCE online business ne Wanda malamai suntabbatar da halascinta masana suntabbatar da ingancinsa ba iri kasuwancin da'ake gudunmma mutane da kudin subane shi wannan an centralized ne ko Wanda ya kirkira bazai iya kulleshiba saboda Yana kan block chained.
METAFORCE zakashiga da kudi kadan ka dauki da yawa ummu khalilwacce take zaune akasar Nigeria sananniyace akan harkar METAFORCE ta kawomana hanyar sauki dansamun cigaba.
Zakasamu kudi Mai tarinyawa dawayar hannunka insha Allah
Yana da matakai 1....12
Level 1 anafarawa da 5$
Level 2 anadarawa da 10$
Level 3 anafarawa da 20$
Hakadai har zuwa level 12
Alkhairan metaforce
Kingama register za'abaki TR coins na adadin level din da kika bude
Samun reffaral bonus
Ga garabasar spillover
Da dollars suke biya zaka iya cirewa kamaida kudinka account nantake
Babu faduwa Babu asara aciki
Kishiga kasuwanci Mai tarin alkhairi zaka kwashi kudaden musamman kana gayyato al'umma.
Metaforce alkhairine ga duniya insha Allah

Phone number 07038708382/09069163665

____________★

Kwana biyu cur Dafeeq na hotel abinsa hankali kwance a dalilin yarda da zuciyarsa kan Khadijah na gidan baba hakimi. Dama ya zare layinsa da yasan za'a iya samunsa da shi. Tsaf ya gama shirya yanda zai fara tafi da Kainaat tare da fara aiwatar da shirinsa kamar yanda yasan itama tana can ta gama shirya masa da batun jiran saki.
Tunda ya baro hotel ɗin murmushi ya gagara barin ƙyaƙyƙyawar fuskarsa. Bai wuce gida kai tsaye ba, sai da ya biya wani waje ya amshi saƙo kafin yay sayayyar kayan ƙwaɗayi. Ana sallar isha'i ya shigo anguwar mara yawan hayaniya, tsayawa yay shima yayi sallar sannan ya ƙarasa gida. Ganin motocinta uku a harabar gidan ya tabbatar masa tana gida, amma duk da haka sai da ya tambayi maigadi. Maigadi ya tabbatar masa da ai tumma daya bar gidan bata fita ko ina ba tana gida, sister ɗinta dai tazo ta kwana jiya ta wuce gida. Kai tsaye ya fahimci Nadwa ce, dan ta sanar masa sister ɗinta ce batare da tasan yasan alaƙarsu ba.
Cikin gidan ya nufa hannunsa ɗauke da ledojin tsarabar daya kwaso mata. Yana tura ƙofar ya shigo wani ƙamshi mai daɗi ya daki hancinsa ga sanyin ac. Shaƙa yay ya lumshe idanunsa tare da sauke ajiyar zuciya sannan yay sallama. Da sauri Kainaat da ke zaune cikin kwalliya ta ɗaukar hankali kamar tasan da dawowar tasa ta ɗago. Kallon ido cikin ido sukaima juna, a mamakinsa sai yaga ta wani sakar masa lalataccen murmushi, sai kuma ta taso a hankali cikin takun isa da yauƙi na ƴan ƙwalisar mata a bazata ta rungumesa tana kai masa kisses a kumatunsa da saman lips ɗinsa. Sosai Dafeeq ya shiga ruɗani a wannan gaɓar, amma da yake shima shegen kansa ne sai ya dake abinsa domin ganin iyakar gudun ruwanta da son gane manufarta. Hannu biyu yakai bayanta shima ya rungumeta da ƙyau. A cikin kunnenta ya raɗa mata, “Ki yafe min amaryata. Gwuyawuna bisa ƙasa Hajjaju na”.
Makirin murmushi ta saki tana mai ɗagowa ta kashe masa ido ɗaya. Cike da kissa ta ce, “Ni ya kamata na baka haƙuri ai mijina, domin na fusataka da yawa har ka kai gamin yaji na kwanaki biyun amarcina. Dan ALLAH kayi haƙuri bazan sake ba Baby”.
“Ai ke baƙya laifi Gimbiya. Ni ne mai laifi dana tafi na barki, nayi hakanne kuma domin nesanta kaina da ke har sai kin huce. Ki yafe min abinda na aikata sharrin shaiɗanne, amma in sha ALLAH bazai sake faruwa ba, dan yanzu ke kaɗai ce mai Dafeeq babu wani shamaki a tsakaninmu na har abada”
(Zakaci ubanka ne) ta faɗa a zuciyarta. A zahiri kam saita sakar masa murmushi da kai yatsarta saman lips dinsa ta ce, “Shiiii!!! Karka sake cewa komai. Abinda ya faru ya riga ya wuce har abada, na kuma yafe maka mijina muje kai wanka kazo ga abinci na shirya maka...”
“Abinci fa? Sai kace wadda tasan da dawowa ta?” ya faɗa cikin tarar numfashinta. Sai da gabanta ya faɗi, amma sai tai azamar gyara yanayinta da faɗin, “Akoda yaushe cikin tsammanin dawowarka nake gareni ai, shiyyasa nake shirya abinci safe, rana, dare batare da jin gajiyawa ba Baby. Ba gashi an dace ba yau kuma ka dawo ka sameni a yanda nake fata”.
“Hakane! Ina godiya Gimbiyar mata”. Ya faɗa yana shafa fuskarta da sakin murmushi. Sai dai a zuciyarsa yana jin lallai akwai wata a ƙasa. Fakar idonta yay ya watsa mata harara, a ransa ya ce, (Tsuntsu mai wayo, ta baki ake kamashi hajjaju). Shima kuma yana juya baya ta zabga masa hararar a zuciyarta tace, (Yaro yaro ne, yaro bai san wuta ba sai ya taka. Ƙiris ya rage na shafe tarihinka a nawa)

😂😂Cuta ta ɗau cuta kenan🚴🚴🚴🚴🚴.

_________★
Chapter 36 · 0% Book details