← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 82

Sashe 15

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

          Sati biyu ta cika a tsakanin Dafeeq da Kainaat. Yayinda ɓangarorin biyu kowa ke nasa shirin. Sai dai duk yanda Dafeeq ya ɗauki al'amarin ƙarami game da tunkarar Khadijah da zancen zai ƙara aure hakan ya gagara. Duk da yanzu ta tattarashi ta ajiye bata masa magana akan komai da zai zo da shi gidan amma sai yaji ya kasa tunkararta da batun. Ya fara zuwa aiki, yayinda nauyin cefanen gidansa ya koma kan Kainaat a yanzu. Kullum cikin kawo musu kaji da kayan daɗi yake, ya baza ɗunkuna na alfarma tsakanin yadika da shaddoji. Ita kanta Khadijah ya mata kala goma masu tsada. Sabon gida ne dai basu kai ga komawa ba, amma mota tuni Kainaat ta koya masa da kanta a yanzu haka ma ita yake hawa.
     Hankalin Khadijah a matuƙar tashe yake, kullum sai tayi kuka amma tsoro ya hanata sake tunkarar Dafeeq akan wannan sabon yanayin da suka tsinta kansu a ciki. Duk da yana fahimtar halin ƙuncin data saka kanta bai taɓa zaman lallashinta ba. Sai dai yana cin abincinta, yana kuma biyan buƙatarsa a jikinta duk da ita batajin wani shauƙin hakan a yanzu. Yakan fita gida da safe sosai, baya dawowa sai sha ɗaya, wataran ma sai sha biyu. Daya dawo yay wanka yaci abinci zaice ya gaji suje su kwanta. Dole take bin umarninsa, ya sameta ya mora ya hau barcinsa. Itako bata iya runtsawa, dan sosai take kewar Dafeeq ɗinta na da. Wanda baida lokacin kowa da komai sai nata, kullum suna manne da juna. Hatta da aiki yakan makarane a kullum kafin ya fita. Sannan idan ya dawo gida baya sake fita sai salla, da an idar yake dawowa gida su cigaba da sha'aninsu cike da farin ciki da farantama juna. Hatta aikin gida tare sukeyi, wankin kayansu da fita zuwa gidan baba hakimi. Wataran ma haka nan zai ɗauketa suje su zagaya gari suyi ƴar sayayyar kayan ƙwalam dinsu ko suci a can su dawo gida. Wanka idan har yana gida tare sukeyi. Amma yanzu duk babu waɗan nan tattalin da soyayyar. Iyakarsa cin abincinta da kuma sauke gajiyarsa. Dariyarsa ma ta gagareta gani, idan ta nuna damuwa ko'a fuska yace ita ta cika matsala. Tasan fa da da yanzu akwai banbanci, yanzu yana aiki uziri ya masa yawa kaza-kaza. Bata da bakin magana, dole take haɗiye komai sai ya fita taci kukanta. Ga kaɗaici na cimata zuciya, sam kayan alatun da yake faman zube musu a gidan baya wani birgeta, ita saima ta yini bataci abinci ba. Duk ta fige ta fita a hayyacinta. Shiko yana mulmula uwar ƙibarsa fatarsa na ƙara wani fresh.

    Yau ya kasance laraba, saura kwanaki biyu a ɗaura auren Dafeeq da amarya Kainaat, dan haka ya yanke shawarar tunkarar Khadijah da batun nan dan baya so taji a waje. Tayi mamakin ganin ya dawo aiki da wuri. Dan ana idar da sallar la'asar ya shigo gidan. Wanka yayi yace ta kawo masa abinci. Bayan yaci ya ƙoshi yana mata ƙorafin ramar da tayi itako tana ɗan murmushin ƙarfin hali kawai batare da tace komai ba. Bai sake fita ba har akai kiran sallar magrib sannan, bayan yayi har isha'i ya dawo gidan da tsarabar kayan ƙwalama. Tsareta yay sukaci tare, ganin kamar ya fara dawo mata a Dafeeq ɗinta na baya taji ƴar nutsuwa harta saki jiki taci. Bayan sun gama wanka sukayi da brush, tayi mamakin jin yace da wuri zai kwanta, amma haka ta danne komai na wasi-wasi a ranta ta biye masa suka shige bedroom tun ƙarfe tara. Tana kwance a jikinsa shiru bayan ya gama biyan buƙatarsa taji ya sauke ajiyar zuciya. Kallonsa ta ɗan yi, kamar bazatace komai ba sai kuma ta nisa itama tare da sake shigewa jikinsa.
      “Husby kanada damuwa ko?”.
   Shiru kamar bazaice komai ba, bayan wasu sakanni ya sake sauke numfashi da fuskantar ta shima. A hankali ya ce, “Tabbas inada damuwa Khadijah, kuma a kanki ne.”
    A zabure ta kallesa tana mai nuna kanta da waro idanunta. “Ni kuma dai? Dan ALLAH miyasa zaka shiga damuwa a kaina Dafeeq. Wlhy in dai abinda ya faru ne a kwanakin baya ni na ajiye komai, na kuma maka uziri, sannan ina farin cikin cigaban da ya samemu tunda nasan duk dan ka faranta minne. Fatana dai ALLAH ya cigaba da rufa maka asiri ta hanyar halak, dan bana fatan jikunanmu su zama a cikin jikunan da wutar jahannama zataci sakamakon ci daga haram. Bana zarginka bazan kuma taɓa zarginka ba in sha ALLAH”.
       “Nagode da hakan. Sai dai ni ba'akansa nake damuwar ba. Dan nasan dai hakkin ciyar dake a kaina yake Khadijah. Sannan inada ƴancin neman arziƙina ko zuwa miki da sabon abu batare da shakkar karki tuhumeni ba. Abinda kawai na sani bazan taɓa aikata abinda nima zai wargazamin rayuwa ba akan neman abinda zan ciyar dake ko ƙyautata ratuwarki.”
     Duk da maganganunsa sun mata wani iri haka ta danne harda sakin murmushin ƙarfin hali. Cikin son danne hawayen da suka cika mata ido ta ce, “Hakane”.
      Tashi yay zaune fuskarsa babu alamar wasa, hakan yasa itama ta tashi zaunen da ƙyau. Sai da ya zuba mata idanu na wani lokaci tamkar mai nazartar ta kafin ya ce, “Khadijah!”.
    “Na'am”.
Ta amsa masa cike da girmamawa.
        “Mata nawa akace maza su aura a musulince?”.
    Ƙirjinta yay wata irin muguwar bugawa har sai da ta ɗago a zabure ta kallesa. Ganin yanda ya tsareta da nashi idanun ta haɗiyi wani abu mai kauri a maƙoshinta tana maida idanunta ƙasa cikin rawar murya ta ce, “Huɗu”.
      “Masha ALLAH” ya faɗa yana gyara zamansa. Batare da damuwa da yanayinta ba ya cigaba da faɗin, “To ALLAH ya karrama mijinki da zamowa cikin jerin maza da zasu ƙara aure, nima zan mallaki mace fiye da ɗaya kenan. Dan na samu wata baiwar ALLAH da muka dai-daita kammu har jibi juma'a ma za'a ɗaura auren in sha ALLAHU....”
     Sosai jikin Khadijah ke rawa Kaff-kaff tamkar wadda aka kaɗama gangi, yayinda idanunta tuni hawaye ya ɓalle a cikinsu. “Aure kuma Dafeeq!”. Ta faɗa cikin suɓutar baki da rawar lips ga hawaye share-share. Fuska ya sake tsukewa tamau, cike da gadara ya ce, “Ban cika namiji bane?”.
       Kanta ta girgiza masa da sauri. “A'a ba haka nake nufi ba. ALLAH ya sanya alkairi ya bada zaman lafiya”.
    A gatsine ya ce, “Amin” tare da komawa ya kwanta ya juya mata baya. Hannu tasa ta toshe bakinta jin kuka na neman kufce mata. Sai dai duk da haka sai da sautinsa ya shiga cikin kunnen Dafeeq. Ƙaramin tsaki yaja batare da ya juyoba ya ce, “Malama bana son wata damuwa fa. Idan kin kwantar da hankalinki ma ita wadda zata shigo ɗin ba sa'ar yinki bace ba. Sannan bata da lokacin wani yin ƙishi-ƙishin banzan nan dan tanada aji ta kuma san abinda yake yi. Ya rage naki ki kwantar da hankalinki kici arziƙi kema cigabanki ne”. Daga haka ya juya yay kwanciyarsa.
Kasa daurewa Khadijah dake jin kanta na juya mata tayi, da sauri ta dira a gadon ta nufi falo........✍️

_Humm Khadijah 😕🤌🏻_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na goma_

_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED

___________
Chapter 15 · 0% Book details