Sashe 6
Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
A hankali yake buɗe idanunsa da sukai wani masifar nauyi. Da sauri ya ɗan rumtsesu ya sake buɗewa again. Sai dai yanzun ma dai a hankali yake motsasu. Fankar dake juyawa kaɗan-kaɗan ya zuba ma su na tsawon sakanni goma. Tun yana kallonta dishi-dishi har idanun nasa suka fara gani tar-tar. Tabbas ba gidansa bane, dan anan ɗin normal selling ne saɓanin gidansa da akaima sabon lafiyayyen p.o.p da yasha fitulu. Sake ware idanun yay da ƙyau tare da motsa jikinsa, jin hannunsa na dama yay masa nauyi sosai ga zafin daya ratsashi saboda fisgar da yay masa ya sashi ambaton “Wash ALLAH na”.
A karo na farko duk wanda ke ɗakin suka juyo garesa, sai kuma duk suka zabura kowa na ambaton sunansa. Idanunsa ya sake buɗewa da ƙyau yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Mahaifinsu ne, sai yayunsa biyu da abokinsa MB da SJ, sai ƙaninsa guɗa ɗaya. Jin yanda suka rufesa da tambaya da sannu ya sashi motsa bakinsa da yay nauyi a hankali ya furta, “Abba ina ne nan ɗin?”.
“Asibiti ne Jazool, an kawoka ne baka da lafiya tun jiya”.
Yayansa ya bashi amsa cike da nuna alhini da tausayawa. Da ɗan sauri JJ ya dubi hannunsa, ganin ruwa ake ƙara masa ya sashi yarda da zancen yayan nasa. Ƙoƙarin tashi yake zaune sai dai ya kasa, cikin sauri MB da yayansa na biyu suka kamashi. Zaunen suka tadashi, tare da jinginasa jikin bango da Nuhu ya gyara filo suna cigaba da masa sannu. Kai kawai yake iya gyaɗa musu shi dai, ransa fal mamakin miya kawosa asibiti shi kam.. Idanunsa ya rufe ruf, tamkar wanda ake sarrafawa da remote sai kuma ya buɗe da sauri jin abinda MB ke faɗa...
“Sannu kaji abokina, gaba ɗaya ka ɗaga mana hankali, amarya da ya kamata ace ita ke jiyya sai kuma kai a naku labarin amarcin ya juye kaine kwance a gadon asibiti? Ni dai ALLAH yasa ba pills ɗin dana baka bane ya jawo maka wannan bala'in tun jiya ake abu ɗaya kamar bazaka rayu ba”.
Rawa jikin JJ ya farayi, ya ɗan juya ya dubi sashen da Abba da Yayunsa suke, can ya hangosu a bakin ƙofa alamar magana sukeyi, sake maido idanunsa yay kan MB da SJ dake tare da shi kawai. Muryarsa na ɗan rawa ya ce, “Yaushe aka kawoni nan? Waye kuma ya kawoni?”.
SJ ne ya bashi amsa yanzun kam da “Tun jiya da safe aka kawoka. Amaryarka ce kuma tai kiran Rabi'ah tana kukan cewar azo a taimaketa ka mutu kamar yanda Nuhu ya sanar mana. Hankali tashe su Yaya Mujee suka nufi gidanka. Inda aka taddaka yashe a ƙasa baka numfashi kuma duk an jimaka ciwo a fuska da jikinka kamar da farauta, itama amaryarka jikinta duk jinin da yake biyo mata ta hanci da gefen baki alamar dukanta akai...”
Da wani irin gudu abinda ya faru tun daga barinsu gidan zuwa komawarsa ciki ya shiga dawo masa. A take jikinsa ya fara kakkarwa. Muryarsa dake a disashe na rawa ya ce, “Duka? Ita Alimah ɗin?”.
“Ƙwarai da gaske, dan tare ma aka kawoku asibitin nan, sai dai ita tun jiyan aka sallameta bayan Doctor ya dubata sosai, ya kuma tabbatar da marinta akai bakinta da ya fashe, jinin hancin kuma haɓo ne tayi. Kaiko an yayyageka da farauta ne aka jijji maka ciwukan nan. Dalilin sumanka ne dai har yanzu basu ce komai akansa ba, dan jiyan ma da ƙyar aka samu ka farfaɗo kusan sha biyun dare, shine sukai maka allurar barci sai yanzu ne kuma kake farkawa”.
Cikin rawar lips mamakin zantukan MB ras akan fuskarsa ya buɗe baki zaiyi magana, sai dai shigowar likita tare da Abbansa da yayunsa ya hanashi cewa komai. Duk fita likita yace suyi, yayinda shi kuma ya shiga duddubashi yana jera masa tambayoyi akan yanda yake ji a yanzu. Da ƙyar ya iya bama likitan amsa da cewar shi yanzu baijin komai, sai kansa da yay masa nauyi da kuma mararsa.
“Insha ALLAH suma zasu sakeka. Ciwon kan normal ne na daɗewa da kai a sume. Na maran ne dai ƴar damuwa itama kuma bamai tada hankali ba. Da ka samu kasancewa da matarka zaka koma normal. Pills daka sha ne suka haifar maka da hakan. Amma sai ka kiyaye gaba dan bincikenmu ya tabbatar mana daka jima kana amfani da irinsu, hasalima ƙarfin maganin da rashin sauke nauyin da suka saukar maka ne ya haddasa maka sumar nan kayi kuma nauyin farfaɗowa. Ka godema ALLAH ma kuma da baka samu haikema yarinya a wannan yanayin ba tunda naji ance amarya gareka, dan ƙarfin maganin nan zai iya sawa ka mata babbar illa musamman idan ta kasance virgin. Dan ALLAH ku dinga bincike akan abu kafin kuyisa, dan hakan wautace sosai. Musamman idan mukai dubayya da su yaran da ake kai muku basu san komai ba, binsu a hankali akafi buƙatar kuyi tunda al'amarin ba damben gwada ƙwanji bane ba. Kaga gashi nan wajen ceton kanta ta jijji maka ciwo itama ka jimata ciwon ta hanyar marinta da kayi. Hakan ai kaga baida amfani sam a daren farko fa kuma....” Likitan ya ƙarasa maganar cikin zafi-zafi. Shi dai JJ kallonsa kawai yake kansa a wani irin juye. Dan gaba ɗaya yama gagara auna maganar doctor ɗin a muzubin hankali kona fahimta. Shi harma a yaushe yay yunƙurin yin wani abu da Alimah. Ya san dai yasha pills kam tabbas, yana kuma cike da ɗokin yin shagalinsa, amma bai ko ɗau hanyaba. Kai shi bama wannan ba fa, abinda ya faru tsakaninsa da Alimah ɗinne abu mafi girman ɗaga hankali da buƙatar yin tunani, sai kuma yanda yaji labarin na neman canja kansa zuwa wani bigire daban a bakin wannan likitan. Ɗan zabura yay zai sauka a gadon har yana buge likitan. Da mamaki ya ɗago da ga rubutun da yake ya dubesa, ganin yana neman direwa a gadon yay saurin riƙesa da faɗin, “Ya ALLAHU! Lafiya kuwa?”.
“Babu ita Doctor, Alimah nake son gani”.
A halin da JJ ke ciki da yanda Doctor ya fahimci al'amarin akwai banbanci, dan haka yay murmushi yana ɗan laɓe bakinsa. “To baban soyayya kwantar min da hankalinka nan Please. Indai amaryace yanzu zaka ganta har nan inda kake duk da ma dai zamu sallameka ne muma kaje gareta a yau ɗin nan in sha ALLAHU kaji”.
“Doctor plea....”
“Shiii!!!” doctor yay saurin katsesa. Daga haka ya juya yana fuskantar ƙofar da faɗin, “Zaku iya shigowa”.........✍️
_😂To JJ dai ALLAH yasa kar a nuna hali anan ma🚴_
https://chat.whatsapp.com/ImF9JpXmBISJCvMBGkTKLc
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na huɗu_