Sashe 74
Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Duk wanda ke a cikin wannan ahali yau kasan yana cike da ɗunbin farin ciki mara misali, dan hatta doctor daya tabbatar da ciki a jikin Khadijah yasha ƙyaututtuka. Tuni Abaan ya rungume Khadijah a gaban Mamy babu ko kunya, turaren ko da tace bata son ƙamshinsa duk da tsadarsa haka ya ɗauka ya bama Awwal shi, yace an bar sakawa. Sai ya koma idan ma zai saka turare sai ta zaɓi wanda ƙamshin yay mata koda shi baya so kuwa. A haka ta cigaba da rainon cikinta da kulawa, dan kowa tattalinta yake kamar ƙwai a cokali a gidan. Batun tafiya karatunta kuwa dole ya tsaya dan boss yace sai ta haihu kuma. Bata damu ba, dan abinda mijinta ke so shi take so itama.
Cikinta na wata shida Ni'ima ta haihu. Da farko dai Abaan yaso ya hana zuwan, amma ta saka masa rigima dan tunda sukai aure zuwanta ɗaya Kano bata sake ba. Sai dai Auta da Jamila sun zo mata hutu sau biyu, yanzu haka ma so take jamilar ta dawo kusa da ita saboda yanayin cikinta. Sai da Mamy tasa baki ya yarda taje jin cewa har Mamy zata je. Haka suka ɗunguma sai Kano ta dabo.
Sun sami tarba ta mutunci da girmamawa. Dan Mama tata roƙon Mamy akan su sauka anan, hakan kuwa akayi. Kasancewar ana gobe suna suka je washe gari tunda safe suka nufi gidan Ni'ima mai jego, inda suka sami itama Zuhrah na fama da nata cikin, dan tsakaninsu da Khadijah kaɗan ne. Babu zato sai ga Abaan, ta dinga harararsa dan bata san zai zo ba. Shiko yana mata dariya ƙasa-ƙasa dan yana tare da su Adams ne da wasu abokansu. Yaro kuma an masa takwara da Abaan ɗin ne. Zokaga murna wajen Khadijah da Abaan. Aiko yaron nan yasha ƙyautuka. Suna ya ƙayatar sosai, Abaan yasa rigimar ranar zai koma da matarsa har sai da Mamy ta tsawatar masa. Aiko yace in dai bazata koma Abuja ranar ba shima bazai koma ba yana nan Kano har sai sanda zasu tafi. Mamy tace yaje ya ƙarata.
Kwanakinsu uku a Kano sukai shirin dawowa Abuja. Kusan sha ɗaya na safe Khadijah ta shirya dan zuwa ta gaida wani kawunsu dake can ƙasan su. Hakan yasa Abaan da yazo yace tazo ya kaita. Dama tare suke da Noor. Tafe suke a mota cike da nishaɗi suna hirarsu. Da wani kalar sauri Abaan ya taka birki dan kaɗan ya rage ya buge wata yamutsatstsiyar mata goye da yarinya a baya ta fito a wani gida a guje da icce a hannu tana ɗura ashar manya-manyan. A harzuƙe ya taka birki, sai dai kafin yay magana sai ga wani mutum shima ya fito da nasa iccen a hannu yana zagin shima na rashin mutunci. Matar ya wulwuloma iccen, saura kaɗan akan Khadijah da ke ta saitinsu tayi zuru tana kallonsu kamar mai son tuna ina ta sonsu.
Tofa, an taɓo abinda Abaan bazai iya haƙuri ba, tuni ya ɓalle murfin mota Noor na take masa baya. Amma mi yana fitowar ya iso gabansu da nufi masifa yaja yay turuss kamar yanda matar nan mai goyo tai tsaiwar sojan badakkare ta zuba masa ido kamar zata suma. Dan namijin har ya ƙaraso gareta zai wanka mata mari sai kuma shima ya tsaya cak jin cikin wata irin murya mai rawa da karkarwa ta ambaci “ABAAN!!”.
Kasa amsa mata Abaan yayi, dan shi ƙoƙarin tuno ina yasan fuskar tata ma yake amma ya kasa. Sai da Khadijah data kasa haƙuri ta fito da sassarfa. Kainaat ta nuna sai kuma ta kalli Dafeeq da ya wani mugun rama yay rakwaf a tsaye kamar wani ɗan shekara arba'in da ɗoriya saboda wahala. Cikin son tabbatarwa ta ce, “Wai da gaske Kainaat da Dafeeq ne?”.
Da sauri Abaan ya kalleta ya ce, “Kainaat kuma Baɗɗo am?! Dama kin santa ne?”.
“Yess Hamma nasanta, ai itace ta auri Dafeeq gashi nan.”
Juyawa yay ya kalli Dafeeq ɗin da jikinsa ke rawa. Dan wani kalar kallon Khadijah yake kamar idanunsa zasu zazzago ƙasa dan tashin hankali da ruɗanin Ganin Khadijahn tamkar wata baƙar balarabiya, ga cikinta ya fito ɗas yay mata ƙyau. Wani shegen kishi ne ya ziyarci zuciyar Abaan. Hannun Khadijah ya kamo ya riƙota jikinsa. Batare da yace komai ba ya nufi mota da ita. Sakata yay, shima ya shiga ya zauna. Hakan yasa itama Noor dakema Kainaat wani kallon ƙyama da tsana ita da Dafeeq ɗin taja tsaki ta shige mota. Ko kallansu Abaan bai sake yi ba ya birga motar sukai gaba. Har sukaje gidan kawun babu wanda ya sake magana. Kusan awarsu ɗaya a can suka sake dawowa gida. Ƙofar gidan da suka bar su Dafeeq suka samu cike tamm da mutane, Abaan yayi niyyar wucewarsa sai dai kuma ya tsaya jin mike faruwa?.
Wata mata ce ke sanar musu ai Dafeeq da matarsa ne wani mai napep ya buge yay tafiyarsa. Yay musu horn yay musu amma suna tsaye a tsakiyar titi kamar gunkina shiko yabi takansu dan barikinsu ba ɓoyayya bace a anguwar. Kullum ne sai sunci uban dabe har titi, a garin dabben nasu ne ma suka makema uwar Dafeeq ɗin ido yanzu haka ido ɗaya ne da ita ɗayan ya tsiyaye. Ubansa kuwa tuni ya gudu garinsu yay aurensa. Har Kainaat ɗin nada ciki haka suke zuba dambe, yanzu ma data haihu kuma basu daina ba, a kullum faɗan nasu bai wuce kan abinci sai kace karnuka. Dan shi dai Dafeeq ɗin baya aikin komai balle sana'a sai zaman gulma a majalisar abokai, yanzu haka suma sun gaji sun korosa. Ita kuma Matar tasa wahala tasa tana bin gidajen mutane tana wankau ana bata sauran abinci da kuɗin da basu taka kara sun karya ba. Shi kuma da son zuciya idan ya gani yace zai ƙwace hakan ke haɗasu faɗa kullum a tsakkiyar anguwa. Yau kuma ance wai shi tsohuwar matarsa ya gani, ita kuma tsohon mijinta sun zama mata da miji suma shine sukai sumar tsaye har mai napep ɗin yazo yay awan gaba da su. To yanzu dai gasu can anyi cikin gida da su......
Noor ce taja tsaki saboda gajiya da surutun matar, cikin hasala tace, “Please Hamma mutafi Mamy na jiranmu muka zauna jin wannan shirmen banzar”. Numfashi ya ɗan sauke kawai yana ƙoƙarin tada motar Khadijah ta ɗaura hannunta a saman nashi. Kallonta yay kamar yanda take kallonsa itama. A hankali ta sakar masa murmushi mai sanyi. Shima murmushin ya sakar mata, sai kuma ya girgiza kansa kaɗan ya ce, “Ya akayi Baɗɗo am”.
“Hamma mu taimaka musu, Aunty Noor kiyi haƙuri kinji. Babu abinda yafi rama sharri da alkairi nasara a rayuwa. Mu musulmai ne, masu tarbiyyar koyarwar MANZON ALLAH (S.A.W). Ya mana dukkan ni'ima ta rayuwa badan munfi saura daraja da kima ba, sai dan kawai haka yaso. Wannan wata damace UBANGIJI ya bamu, idan mukai amfani da ita mune da riba har abada”.
Kusan a tare Abaan da Noor suka saki ajiyar zuciya. Wata irin ƙaunar Khadijah na sake ratsasu....
Da ƙyar suka sami ganin su Dafeeq da aka zagaye anama fifita. Ga mahaifiyarsa da alamu suka nuna bata gani da ƙyau nata kuka a gefe. Haka yarinyarsu sai tsanyara kuka take itama da rauni a goshinta. Hannu Khadijah tasa ta ɗauke ta, duk da kuwa yarinyar duƙu-duƙu take da datti har wani tsami-tsamin dauɗa take da zarni. A zabure Dafeeq da Kainaat suka tashi kamar basu ne kwance magashiyan anama firfita ba suna nishi da ƙyar.