← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 82

Sashe 75

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Da gaske ku ma'aurata ne a yanzu?”. Cewar Kainaat cikin rawar murya da zubar hawaye. Kafin Abaan da Khadijah suyi magana Noor ta amshe a gadarance.
“Yess su ɗin ma'aurane. Masoyan juna na bugawa a sararin samaniya bama bango ko dutse ko jarida ba. Gasu ma har ALLAH ya azurtamu da samu rabo, nan da watanni uku in sha ALLAHU ɗanmu ko ƴarmu sun shaƙi iskar duniya. Ya kukaga haɗin dan ALLAH”. Ta ƙare zancen da ƙyalkyalewa da wata shegiyar dariya har sai da Abaan ya harareta. Kuka Dafeeq da Kainaat suka fashe da shi a lokaci guda tamkar wasu ƙananun yara. Yayinda Mahaifiyar Dafeeq ke tayasu. Cikin kuka tana faɗin, “Yanzu duk ƙoƙarina na kar Khadijah kiga Dafeeq dai ko ya ganki haƙata bata cimma ruwa ba kenan. Oh ni oh ni duniya haka zakimin. Yau ga Khadijah gaban ɗana tamkar matar shugaban ƙasa. Ga ɗana a ƙasƙance gabanta kamar almajirin gidanta. Dafeeq ka cuci kanka ka cucemu daka kwaso mana wannan KARA DA KIYASHIN da bakin iyaye ke ɗawainiya da rayuwarta. Gamunan ta goga mana ƙashin tsiyarta matsiyaciya kawai tsinanniya mai yawo da tsinuwar iyaye aka....”
“Ashaa mama haka bai ƙyautu ba. Ai daga ɗanki har matarsa duk ɗaya suke a gareki. Hakan garesu kuma rubutaccen al'amarine da babu hannun da ya isa ya goshesa a cikinsu. Haka ALLAH ya tsara, batare da mun taɓa sanin juna ba amma ya auri mace ya saka na aura, na saka nima ya aura. Wannan wani hukuncine da ga UBANGIJI......”
“CUTA TA ƊAU CUTA... ALKAIRI YA ƊAU ALKAIRI ba Hamma”. Noor ta katsesa tana wani balla musu harara. Aiko atake jama'ar da suka cika tsakar gidan duk da ana korarsu sun ƙi fita suka shiga faɗin, “Wannan haka yake.dan babu wanda bai san soyayyar da Khadijah ta gwadama Dafeeq ba. Amma yaci amanarta shi da uwarsa. To gashi nan ya rabu da ita saboda abin duniya ya auro dai-dai da shi mai fama da bakin iyaye. Dan tuni a surutun Dafeeq da mahaifiyarsa sun fayyacema mutane wacece Kainaat. Kullum cikin mata gori ake a anguwa. Tana son zuwa ga iyayenta bata da ko kuɗin motar barin Kano. Data fara tarawa kuma Dafeeq ke sacewa. Haka zasu ci uban dambe su jigata juna ta haƙura. Hakan kuma bai hana ta sake tarawa ya sace su.
Jin al'amarin nasu dai babu daɗin ji Abaan ya basu kuɗi. A take Khadijah ma ta basu daga jakarta sukace suje asibiti suka fito suka barsu dan Mamy nata kiransu lokaci zai ƙure musu gashi jirgi zasu bi. Haka dai suka dawo gida jiki a sanyaye. Yayinda suka bar Dafeeq da Kainaat da mahaifiyarsa na rusar kuka. Da ga ƙarshe faɗa ya nema hargitsewa tsakaninsu akan kuɗin. Dafeeq na son nuna musu ƙarfa-ƙarfa daga uwarsa har Kainaat ɗin sukace bai isa ba kowa yaje yaji da kansa. Dan haka maimakon asibiti ma camix suka je aka duddubasu kowa ya matse kuɗinsa. Burin kainaat gobe asubar fari ta nufi Niger neman iyayenta ta nema gafararsu ko hakan zai sa ta samu sassauci kamar yanda mutane keta bata shawara. Maybe hakan zaisa ta samu Dafeeq ya saketa ta dawo ta auri Abaan. Shiko Dafeeq nasa hangen ya haɗe kudi ya fara kasuwanci ko shima ALLAH zai azurtashi Khadijah ta dawo garesa.......
✍️

_Niko nace Hummm hauka maganinka ALLAH. Ai an baro shiri tun rani Kainaat da Dafeeq 🥱🥱😆🧑‍🦯._

*_NACE KIN MALLAKI NAKI👋??._*

*_NAKI NAKE NUFI KIN MALLAKA KUWA👋🏻👋??_*

*_TIKITIN SHIGA JIRGIN TAWAGAR ZAFAFAN LITTATAFAN NAN NA ZAFAFA BIYAR NAKE MAGANA SISTER KIN MALLAKA👋👋👋🤔??_*

*_KIN SAN KUWA A WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA DABBANCE. IDAN NACE DABAN INA NUFIN DABAN A CIKIN DABAN_*

*_A 2024 ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN NAKU SUN SAKE ZUWA MUKU DA WASU SABON SALO NA MUSAMMAN DA ƘAYATARWA AKAN FARASHI KAI SAUƘI DA RAHUSA. DAN HAKA INA GAYA MIKI ƳAR UWA KADA KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE_*

_Littatafan sune kamar haka 👇🏻_.

*_KWANKWASON JIMINA....._*
_(NA MSS XOXO)_

*_GUDUN ƘADDARA_*
_( NA SAFIYYA HUGUMA)_

*_TSUSTAR NAMA....._*
_(NA BILYN ABDULL)_

*_AMEENATU_*
_(NA MAMU GEE)_

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏_*i

*_Typing📲_*

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na arba'in_

*ZAFAFA BIYAR FAMILY*🫂🫂🫂🫂🫂

🔥 *me kike jira ne da har yanzu baki shige ahalin zafafa ba*

*_ZAFAFA BIYAR_*❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥

❤‍🔥 *_SABUWAR SHEKARA_*

❤‍🔥 *_SABON TSARI_*

❤‍🔥 *_SABBIN LABARAI_*

❤‍🔥 *_TSUMAMMIYAR SOYAYYA_*

❤‍🔥 *_CAKWAKIYA_*

❤‍🔥 *_LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DAKE TAFE DA WANI IRIN SALO_*

❤‍🔥 *_SALON DAKE DAUKE DA ZALLAR GOGEWA DA QWAREWA WAJEN SARRAFA ALQALUMA_*

❤‍🔥 *LABARANSU NA MUSAMMAN NE DAKE DAUKE DA WANI IRIN SALO ME RATSA JIKI_*

*_KWANTAR DA ZUCIYA_*

*_CIRE DAMUWA DA SABUNTA SOYAYYAR MASOYA_*

*QAWATATTU KUMA TSARARRUN LABARAN 2024 DIN SUNE KAMAR HAKA*

*KWANKWASON JIMINA* _ME WUYAR TABAWA_ (miss xoxo)

*TSUTSAR NAMA* _ITAMA NAMA CE_ (Billynabdul)

*AMEENATU* (Mamuhghee)

*GUDUN K'ADDARA* _GUZURIN TARAS DA ITA_ (Huguma)

*_KOWANNE LABARI NA DAUKE DA SUNA ME HARSHEN DAMO,KAMAR YADDA GUNDARIN LABARIN KE DAUKE DA SALON DA ALQALUMAN ZAFAFA BIYAR NE KADAI ZAI WARWARE MUKU SHI_*

*_Biya naki ta wadannan lambobin domin ki zamo cikin ZAFAFA FAMILY HOUSE_*

*TSARIN SHINE KAMAR HAKA*

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*THANKS FOR CHOOSING US*🫂🫂🫂🫂

_______________________

........*_YEARS LATER_*. Shekaru sun ja, rayuwa ta canja. Tuni jiya ta sauya daga yau zuwa goben wasu. Al'amarin tamkar mafarki ko labari suma sun zama iyaye. Wannan Abaan ɗin da kowa ya sani a matsayin matashi yanzu sunan dattijo yake amsawa. Hakama Khadijah ɗin nan ta zama babbar mace uwa mai ƴaƴa har huɗu jinin Abaan. Ɗiyarsu ta farko suna kiranta Mimi, wadda taci sunan mahaifiyar Abaan ne. Sai na biyu Muhammad. Na uku Abubakar Sadiq. Sai auta Umar Fharooq. Dukansu kamanni suke da Abaan, babu wanda ya ɗako Khadijah a kamanni sai dai jini shi baya ƙarya, duk wanda ya gansu dai yasan itace mahaifiyarsu.

    Ƙarfe biyar da wasu mintuna zuƙeƙiyar mota ta shigo ƙaton harabar gidan. Driver na kammala parking a gaggauce ya fito domin buɗe mata. Hamshaƙiyar mace da hutu ya nuna kansa a jikinta ce ta fito cikin yanayin gajiya. Tana sanye cikin shiga ta alfarma. Dan wani lass ne mai masifar ƙyau da ɗaukar idanu a jikin nata. Sai farar riga ta likitoci ƙal dake tabbatar da ita ɗin wacece. Sannu direban ya shiga jera mata ganin yanda take ta faman yamutsa fuska alamar a gajiye take. Ta sakar masa murmushin nan nata mai sanyi batare da tace komai ba. Kafin ta raɓashi ta wuce zuwa cikin gidan. Tarkacenta dake a mota shima ya tattaro ya biyota.
         A kusan tare ƙyawawan samarin yaran dake a falon kowa na harkar gabansa suka ɗago. Sai kuma duk suka miƙe suka nufota kowa na faɗin oyoyo Ammie. Hannayen ta ta buɗe musu duk suka shige abinsu. Jikin nata suka bari kowa na jera mata sannu da nuna tausayawa. Itako na faman musu murmushi. Babban da zai iya kaiwa shekara goma sha biyar ne ya kama hannunta har tsakkiyar falon ya zaunar. Sai kuma ya duƙa gabanta yana mai kama ƙafarta ya zare takalmanta ya na danna mata ƙafafun da sukai ɗan fushi. Da sauri autanta da zai iya kai shekara goma shi kuma ya iso gabanta da ruwa yana faɗin, “Ammie tun ɗazu na fito miki da shi a freight ya huce dan kar kisha mai sanyi kiyi mura.”
     Fuskarta da murmushi ta furta, “Oh my AUTA ALLAH yay muku albarka. Yanda kuke ji dani ALLAH ya baku mata da zasu ji daku kuma da ƴaƴa”.. 
       A tare suka amsa da Amin cikin ɗoki harda na tsakkiyar da zai iya kai shekaru sha uku. Shi kuma kayanta dake hannun driver ya amso.
    “Daddy fa?”.
Ta faɗa tana kallon babban. Sauran ƴan uwansa ya kalla sai kuma ya kwashe da dariya. Harararsa Khadijah tayi da faɗin, “Miye abin dariyar?”.
        AUTA ne ya matsar da bakinsa saitin kunnenta. Cikin raɗa ya ce, “Ammie ya ɓuya a sama ne. Wai idan kin dawo muce bai dawo ba. Kuma ya kashe phones nashi sai kin ruɗe sosai zai sakko. Ammafa kar kice ni na faɗa”.
      Murmushi Khadijah tayi mai sanyi tana girgiza kanta. Sai kuma ta miƙe tana kallonsu da kulawa. “Shike nan bari naje na watsa ruwa. A haɗamin shayi kar a saka suga. Ina Mimi?”.
        Shiru yaran sukai saboda tambayar ƙarshe. Sai kuma babban ya ja numfashi muryarsa da alamun ɓacin rai ya ce, “Ammie ta fita. Kuma da alama wannan shegen yaron ne yay kiranta. Ta ƙofar baya ta fita batare da tasan na ganta ba. Naso binta sai nai tunanin kar Daddy ya ji”.
    Shiru Khadijah tai tana kallon yaron nata. Sai dai gaba ɗaya fara'ar dake saman fuskarta ta gushe. Wani kalar bugawa zuciyarta keyi da sauri-sauri. Dan al'amarin yarinyar tata ya fara caja mata ƙwaƙwalwa. Ɗakinta ta nufa, sai kuma ta fasa ta nufi upstairs. Da kallo samarin yaran nata duk suka bita fuskokinsu cike da damuwa. Dan sun san al'amarin yayar tasu shine abu mafi zama damuwa ga mahaifiyar tasu a kwanakin nan...
Chapter 75 · 0% Book details