← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 82

Sashe 11

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    “Wai mi kike shirin yi da wannan yaron da kika danƙarama wannan ƙyautar haka? Kainaat!. Ni gaba ɗaya kin birkita min lissafi wlhy”.
         Murmushi ƙyaƙyƙyawar matar da zata iya kaiwa shekaru talatin da huɗu ta saki. Sai kuma tai wani irin juya lafiyayyar kujerar office ɗin nata da salo irin na isa da ƙasaita tana kai bayanta kwance da lumshe idanu. Tsahon mintuna biyu kamar bazatace komai ba sai kuma ta buɗe idanunta a hankali akan wadda tai mata tambayar. Murmushi ta sake saki da motsa lips ɗinta dake ta shining na jambaki maroon ta ce, “Nadwa!”.
       “Na'am”.
   Nadwa ta amsa mata idanunta ƙyar a kanta.
     “Auransa zanyi”.
  Ta faɗa kanta tsaye babu shakku ko nuna damuwa balle kwana-kwana a zancen nata.
    A zabure Nadwa ta ce, “Aure!! Fa Kainaat? Da wannan abun dana tabbatar kin girma da kusan shekara goma? _Don_ ma da kuke shekarunku dai-dai da shi an miki sutu balle wannan jaririn. To ke da baki gama idda ba ma miya kawo miki wannan tunanin haka?”.
        Murmushi Kainaat ta saki tana wani limshe idanunta da sake buɗesu cike da yanga da ƙasaita. “Nadwa kenan, ai ƙarancin shekarun nasa ne suka ja hankalina da yin hakan garesa. Dan zan samu damar tafi da shirina yanda nake so. Rashin gama iddata kuwa ba matsala bace tunda ba yau nace a ɗauran aure da shi ba. Ina yin sharar fage ne kawai yanzu dan so nake ina gama idda a washe gari a ɗaura min aure da shi”.
     “Hummm wannan wane irin tunani ne yazo miki na rashin mafaɗi Kainaat? Kamarki matar riƙaƙƙen attajirin matashi ɗan ƙwalisa irin _Don Abaan_ ki rasa a inda zaki ƙare sai auren wannan gajan yaron da ko shekarun balaga bai gama cikawa ba. Anya duniya bazata miki dariya ba da kallon kinyi faɗuwar baƙar tasa kuwa? Ai shi kanshi Abaan zai sake jin izza da yarda ya fi ƙarfin naki kamar yanda yay iƙirari. Uwar tashi da ƙanwarsa da suka zama sanadin rabakun kuma sunci riba.”
       Murmushi Kainaat ta saki saki mai faɗi har ƙyawawan farare haƙoranta dake jere reras na bayyana. Idanu ta zubama aminiyar tata cike da ƙasaita. “Nadwa kenan, na fahimci har yanzu baki gama haddace ilimi akan halayena ba kenan. Ban so nace miki komai ba a wannan gaɓar amma ya kamata nace mikin domin ki tabbatar da ni Kainaat ba shasha bace. A tunaninki zan iya haƙuri da 1-0 a fagen wasa ne? Ai in har ba'ai 2-0 ba sai dai ayi draw wlhy, ko kuma a tashi babu ko ɗaya zai fi sauƙi ga abokin karawa. Bari na fito miki a mutum, saki ukun da Abaan yay min zan gyara na sake komawa gidansa dan aure ni da shi yanzu ne zai fara. Wlhy wlhy kinji na rantse, sai na raba Abaan da uwarsa da wannan shegiyar ƙanwar tasa mai kama da aljanu har abada. Sai na sakashi ya wulaƙantasu fiye da yanda suka sa ya wulaƙantani. Sai na shafe babinsu a zuciyarsa fiye da yanda ruwa ke shafe garin da aka gina akan hanyar wucewarsa. Zan ɗanɗana musu azaba sannan na wawashe kaf abinda ya mallaka a duniya ta yanda almajirin saman titi sai ya fisa kima da darajar kallo. Zan tabbatar musu ni Kainaat annoba ce a rayuwarsu. Talauci ga talaka kuma ba tambari bane adone”
       “Kin daina son Abaan ke nan?”.
   Wata siririyar dariya ta saki mai faɗin gaske. Kafin ta furta, “Bazan taɓa daina son Abaan ba har ranar mutuwata, sai dai kuma hakan bazai hana ni ɗan ɗana masa hukuncin laifinsa ba da na uwarsa da ƙanwarsa dan sabo da kaza a wajena baya hana na saka mata wuƙa a maƙoshi na yanka banza nai farfesunta na cinye”.
       “Humm amma kin san shi wannan yaron da kike son aure yana da mata? Sannan ba ɗan garin nan bane zuwa sukai nan aka ɗaura musu aure a gidan hakimi saboda mugun son da sukema juna shi da matar tasa”.
     “Wannan dalilinne yasa na zaɓesa ai. Batun matarsa kuwa idan ta kwantar da hankalinta ƙaruwarta ce. Dan bani da wata matsala da ita sai idan ta shiga gonata ne fa tabbas bazan barta ba koda ace zaman sati ɗaya nayi niyyar yi da mijin nata kuwa. Soyayya da kike magana kuma ni ban yarda akwaita ba. Dan naga abubuwa masu yawa a cikin idanun wannan yaron na hatsabibanci. Inda ace sonta yake da gaskiya bazai rabota da iyayenta ya kawota nan ya aura ba. Da sonta yake bazai dinga zubar mata da ciki ba a duk sanda ta samu....”
       “What! Zubar mata da ciki fa kika ce? Ke ko ina kika san duk wannan Kainaat?”.
     Wani shegen murmushi Kainaat ta saki tare da maida bayanta jikin kujerar ta wani kwanta........✍️

        _(Tofa wata sabuwa. Khadijah da Dafeeq laila da majnoon yaya dai?🚴🚴)._

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

   *_Typing📲_*

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na bakwai_

INA ƳAN KASUWA MASU SON ƘAWATA KASUWANCINSU TA HANYAN GRAPHIC DESIGN, DA MASU SHIRIN BIKI, KO SUNA, DA MASU SHIRIN WALIMAR SAUƘA, DA MASU SHIRIN YIN BIRTHDAY, KAI HARMA DA MASU ANNIVERSARY 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼

MAZA KU GARZAYO "UMMUH FARUQ GRAPHIC DESIGN "TA TANADAR MUKU DA HAƊAƊƊUN DESIGN MASU ƘAYATAR DA MAI KALLONSU.🥰🥰🥰

KAMA DAGA
*FLYER
*3D MOCKUP LOGO
*2D MOCKUP LOGO
*NORMAL LOGO
*IMAGE LOGO
*BANA
*STICKERS
*ADVERT VIDEO
*PROFESSIONAL INVITATION
*INVITATIONS CARD
*BIRTHDAY VIDEOS
*POSTER
*CERTIFICATE.AND MORE......

CONTACT ME ON
👇
09035390383

____________

.......“Please Kainat yaya kika san duk wannan wai?”.
     “Humm Nadwa kenan. Na faɗa miki Kainaat ba shashasha bace ba ai, kin san dai bazan jashi jikina ban san wanene shi ba. Inama da fiye da wannan game da shi, sai dai lokaci ne zai sa ki san sauran gaba ɗaya ba yanzu ba”.
Idanu kawai Nadwa ta zuba mata cike da mamaki da tsoro. Maganar gaskiya bata son ƙawar tata tace zata shiga tsakanin waɗan nan ma'auratan dake tsaka da cin ƙuruciyar soyayyarsu. Amma ta santa tasan halinta, in har tace tana son abu sai ta cimma burinta a kansa, dan ita shaidace ko akan Don Abaan da yanda ya fara sonta har sukai aure shirine babba...

       ★★★.....

“Ina ganin zuwa jibi zamu koma sabon gidan can dan mu samu albarkacin juma'a”.
Da wani irin razana Khadijah ta jiyo tana kallon Dafeeq da ke magana a dake hannunsa riƙe da rigarta data miƙa masa zai shanya a igiya. Babu alamar wasa a kan fuskarsa ga shi ya wani tsareta da idanu. Nata idanun ta rissinar ƙasa tana ƙoƙarin saita rawar da jikinta ya fara. Sai kuma ta shiga jinjina masa kanta dan in har tai magana sai hawayen da take riƙewa sun zubo mata.
“Miye wani ɗaga kai baki da bakin magana ne wai? Khadijah nikam wlhy na gagara gane miki gaba ɗaya. Da ace wani kemin wannan sabon halin naki sai na ɗauka baƙin cikine ko hassada. Gaba ɗaya kin hana kanki zama lafiya. Ki duba fa jiya na shigo da waya gidan nan amma koda na nuna miki baki ko taɓata ba a tsatstsaye kika wani ce ALLAH ya sanya alkairi kika kwanta...”
Duk yanda taso riƙe kukan ta gagara yin haka a wannan gaɓar saboda yanda yake mata magana a zafafe kamar ba Dafeeq ɗinta ba. Miƙewa tai da sauri daga gaban kayansu da sike wankewar ta nufi ɗaki da gudu hannunta toshe da bakinta. A zafafe shima Dafeeq ya miƙe, tana shiga falon yana shigowa shima. Wani kalar fisgota yay baya tai taga-taga zata faɗi ya hankaɗata saman kujera. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunsa sun gama kaɗewa, cikin nunata da yatsa tamkar zai mareta ya ce, “K! Wai mi kike nufi dani ne? Dan Kinga ina lallaɓaki kike ganin kin samu hanyar wulaƙantani da jana a ƙasa. Ubanmi na miki ba dai-daiba anan?”.
Kuka sosai Khadijah ta sake fashewa da shi, sai kuma ta kai hannu ta hankaɗashi baya iya ƙarfinta tana ƙoƙarin miƙewa. Taga-taga yay zai faɗi ƙasa ALLAH ya taimakesa ya dafe kujera.
“Taauuu!!”.
Kake jin wani lafiyayyen mari a fuskarta. A gigice ta dafe kuncinta tare da fashewa da wani sabon kukan. “Dafeeq ni ka mara?!”.
“An mareki ko zaki rama? Ke har kin isa ki dinga jana a ƙasa kamar wani yaronki! Har kina da ƙarfin min wannan abun. Ko kuma dole sai nayi abinda kike so saboda haihuwata kikayi ƴar marasa tarbiyya”.
“Dafeeq nice ƴar marasa tarbiyyar?!”.
“Kina da ita ne. Ko ƴa mai tarbiyya ce zata bar uwarta da ubanta ta biyo namiji wata uwa duniya. K! Nifa na fiki iya iskanci. Har ni zaki dingama baƙin cikin cigaban rayuwata saboda ke butulu ce. To bari kiji ki kama kanki kafin na sassaɓa miki kamanni a gidan nan. Dan wlhy kaɗan da ga aikina ne na haɗa miki jini da majina wawuya kawai...” fuuu ya fice kamar zai tashi sama.
Ragwaf Khadijah ta zube ƙasa tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya.. Tunda ta baro gidansu ta biyo Dafeeq yau itace rana ta farko datai mahaukacin kuka na tashin hankali da har ya saka mata masifaffen ciwon kai tare da jin wani abu kamar nadama nasan ɗarsuwa a ranta. Dan ko daren farkonsu tayi kukan azabar da taci a hannunsa amma baiko kai kwatankwacin wannan ba. Ita yau Dafeeq kema gorin bijirema iyayenta ta biyosa nan?, ita Dafeeq ya ɗaga hannu ya mara. Mari fa, mari mai suna mari da har take iya jin sayin yatsunsa biyar akan ƙyaƙyƙyawar black beauty face ɗinta. jama'a Dafeeq fa, Dafeeq ɗinta data zaɓa akan iyayenta da karatunta. Dafeeq data yarda ta bar komai ta koma mara komai ta ɗaukesa. ya arrahaman wannan wace irin rana ce haka da bata taɓa lissafawa a ciki lissafin rayuwarta ba. ya ALLAH kasa mafarki takeyi ba a zahiri bane ba. Ta sake fashewa da sabon kuka mai tsananin ƙona zuciya.....

(Hummm Khadijah kaɗan daga illar bijirema umarnin iyaye kenan. Ƴammata a dinga sassauta soyayyar da har zata iya saka ido rufewa a bijirema iyaye🤦🥲 dan zancen malam bahaushe nan fa na NAMIJI BA ƊAN GOYE bane gaskiya ne akan wasu mazan).

★★★......
Chapter 11 · 0% Book details