← Book details Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 82

Sashe 1

Cuta Ta Dau Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

*_Typing📲_*

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na ɗaya_

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._

........“Ango! Ango!! Ango!”. Itace kalma mafi rinjaye da tafi fita a bakunan taron matasan dake cike da ƙofar gidan. Yayinda wanda suketa faman kira da angon bakinsa ya kasa rufuwa dan farin cikin da yake a ciki a wannan rana data kasance ta aurensa da masoyiyarsa mafarkinsa. Magana da ɗaya daga cikin abokansa ya gwargwaɗa masa a kunne ta saka shi jan hannunsa suka koma gefe. Cikin ɗan nuna yanayin damuwa da hasala ya ce, “MB ya akai haka kuma? Nifa bana son matsala wlhy, duk abinda zan ɓatama Love rai bana son shi musamman a wannan ranar ma data kasance mana ta daban.....”
      “Na sani kwantar da hankalinka, kaima kasan dai bazan bari wani abinda zai ɓata farin cikinka faruwa ba JJ. Na faɗa maka ne kawai dan kar kaga an samu canji, dan yanzu haka ma nariga na daidaita matsalar, wajen da aka samu yanzu ɗin ma yafi wancan komai...”
     “Amma karka manta wajen farkon muka saka a invitation card”.
    “Hakan bazai zama matsala ba shima, dan kusa-da-kusa suke, dabarar da zamuyi zamu ajiye su Nure a ƙofar wancan hall ɗin duk wanda yazo sai su turosa inda aka canja ɗin. Yanzu sai ka sanarma amarya kawai, ko hakan baiyi ba?”.
          “A yayi, kunyi ƙoƙari, ALLAH ya bar zumunci bari na sanar mata”.

     *_DINNER HALL_*

       Matuƙar ƙyau da ƙayatuwa wajen yayi tamkar dama tun farko nan suka shirya yin shagalin. Kalar decoretions ɗin wajen kalar ankon ƴammatan amarya da suka sha ƙyau har suka gaji, haka suma abokan ango shar da su. Shigowar ango da amarya ta shafe duk wani ƙyawun kowa a wajen, dan adonsu na musamman ne. Atake hasken flash ya shiga tashi tako ina, tsakanin wayoyi da camaras, a gefe mc na faman kwarzantasu, yayinda dj ya saki wani cool music mai ratsa zuciya. Ta ko'ina dai taro ya cika taro kam sai masha ALLAH, abokan ango da ƙawayen amarya nata taka rawar gani irin na bajinta tare da dangi takowace ɓangare. A yanda aka tsara komai zaka iya saka masu bikin a layin masu hannu da shuni, sai dai sam ba haka bane ba, ana dai tsaka tsaki, wato babu tsiya babu hamshaƙin arziƙi. Sai dai akwai rufin asirin ALLAH ta kowanne ɓangarorin guda biyu. Anyi taro an tashi lafiya kusan ƙarfe ɗayan dare, ango na son maida amaryarsa gida da kansa yayarta tace karya damu yaje gida ya huta zasu wuce da ita. Babu yanda ya iya dole ya haƙura suka dunguma shi da abokansa zuwa hotel da suka kama. Amarya da danginta suma suka wuce nasu gida dan sai gobe in sha ALLAH za'a miƙata gidan mijinta.....

           *_WASHE GARI_*
Chapter 1 · 0% Book details