← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 48

Sashe 6

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kam mamaki matan nan masa suke bashi ko wacce ta girma a cikin su amma basu daina mararin neman wani abuna wajan sa ba, shi Wauka yake gabaWaya ma an Wauke musu wata sha'awar sa tunda ko wacce har jikoki tana dasu. Har gwara ma Mama tafi Mamy ™arancin shekaru amma Mamy tafi Maman nunawa. Shafa fuskar sa yayi dan shi kam yana da Wanye jini a waje bai ga abinda zai nema a wajan wannan tsofaffin matan nasa ba, shiyasa ko a jikin sa in suna wannan abubuwan, duk wacce ta kawo kanta ita ta sani, shi ban damu ba.

Nana Haleemad'þ>ØBÝ

*BAYA DA ˜URA*

FitattuBiyar2025

Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

    ©þ *Nana Haleema.*

https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp

*BOOK 1*

*Page 004*

A daren Manal suna zaune da Mama a falo cikin hasken fitilar da ya haske falon nasu Manal tace, "Mama gobe da safe zamu koma

Asibiti." Mama tace, "Manal ni ba sai mun je ba lafiya lau nake jina, in mun je goben wani maganin zasu sake bayarwa kuma ba wani kuWi ne a hannun Baban naku ba yanzu."

Manal tayi dariya tace, "za'a samu Mama, Allah dai ya nuna mana goben. Kuma kin ga wajan Dr Huzaifa ne."

"Eh gaskiya, yana da kirki ya Wauke ki kamar ™anwa, sai a Wauka ma ya jima da sanin mu."

"Auu na manta fa wajan likitan zuciya yace muje a kai masa wannan result Win, Allah ya kaimu goben da wuri zan fita dan ance ba wani kirki ne da likitan goben ba."

Mama tayi murmushi tace, "to Allah ya nuna mana. Yadda kike kula dani Allah ya baki mai kula dake Manal Win Mama." Tayi murmushi ta amsa da amin Mama tace, "Ya sayyadi bai yi waya ba?." Manal tayi dariya tace, "Mama kina bani kunya, ni nace miki Ya Sayyadi ba sauryina bane kawai muna gaisawa ne."

"Nima ai baki ji nace saurayin ki bane ba ai, Yayan ki ne." Tayi dariya kamar yadda Maman take yi Manal ta kalle ta tace, "Wallahi Mamana kina da kyau sosai."

Mama tayi murmushi sosai tace, "duk kyauna bai kai na Manalin Mama ba." Manal tayi dariya kawai Mama tace, "Allah ya kawo miki miji na gari wanda zai kula min dake ya inganta rayuwar ki ya cika miki burin ki na zama shararriyar mai dafa abinci ta duniya ma gabaWaya." Manal tayi dake ya tace, "Mama ta duniya fa kika ce?."

"Ko baza ki iya bane?."

"Zan iya mana, amma ta duniya yayi girma."

"Kina wasa da ikon Allah?."

"A'a Mama."

"To kice amin kawai."

"Amin Mamana. Amma ni bazan yi aure ba."

Mama tayi dariya tace, "wannan kalma ta baza ki yi aure ba na faWa miki bana  son ji." Cikin sha'agwaSa tace, "ni dake zan rayu Mamana, indai kuma zanyi aura sai dai mijin yazo nan mu zauna ko mu tafi dake." Mama tayi dariya sosai tace, "Allah ko Manal?."

"Allah Mama. In na tafi waye zai kula min dake?" Ta faWa jikin ta nayi  tunawa fa da gaske wata rana zata yi auren ta bar Maman ta. Jin yadda Manal Win tayi magana sai Mama tace, "ki cigaba da addu'a kawai, duk inda alkhairi yake Allah ya kawo miki shi." Ta amsa da amin bata ce komai ba.

"Ashe yau da arzu™in nepa a unguwar" aka faWa ana shigowa cikin falon. ko ba'a ce sun san wacce ta shigo. Manal ta kalle ta tace, "Yaya ko sallama baki yi ba fa." Hararar ta tayi tace, "bazan yi sallamar ba, bana son iyayi."

Ta kalli Mama da take zaune daga gefe tace, "Mama ki shiga tsakanin a da yarinyar nan ta daina shiga harkata." Mama bata ce komai ba Mubeena ta wuce Waki sai gata ta fito tace, "ke Manal wai babu abinda aka dafa a gidannan ne?."

"Inda kika je basu baki abincin ba?" Mama ta faWa tana daga inda take zaune. Mubeena tace, "in baza'a bani ba ai sai a faWa min kawai, daman nima karanbani na ne ya saka na tambaya, ina za'a samu irin abincin da nake so a cikin gidan nan?."

"Wallahi Yaya baki da hankali." Wara ido tayi tana kallon Manal tace, "ni ki ke cewa bani da hankali Manal?." Manal tace, "na faWa akwai abinda zaki min ne?." Kafin Mubeena tayi magann Manal tace, "Mai hankali bazai aikata irin abinda kike aikatawa ba, ke a ganin ki wayewa ce raina iyaye, baki san hauka ne da rashin sanin ciwon kai ba. Sai girmama iyayen wasu saboda neman suna bakya girmama naki, tirrr! Kin ji kunya wallahi."

"Salamu alaikum wai Nusaiba tazo!." Wani yaro ya faWa yana shigowa, abinda ya dakatar da Mubeena ga yiwa Manal masifa ta juya kan yaron tace, "sai naci kaza kazan wanda ya sake kira na da Nusaiba, sai na zage shi duk girman sa na rantse da Allah. Kar a kuma kira na da Nusaiba ba sunana bane, in baza'a ce Mubeena na ba a kira ni da baiwar Allah. Meye wani Nusaiba ana zaune Lafiya? Ni an cuce ni ma da aka samin Nusaiba wallahi."

Yaron da take yiwa masifa tace, "Baba ne yace kizo in baza ki zo ba sai naje na faWa masa" ya faWa yana fita daman dan ya tunzura ta yace Nusaiba. Mubeena tace, "ko ne zan masa da zai aiko nazo oho, ni bana son takura da saka ido wallahi. Tunda ba shi ya haife ni ba meye nasa na takura min?" ta faWa tan figaat mayafi ta fita daga gidan.

Manal ta kalli Mama dan tasan bata so taji Mubeena tana ambatar sunan mahaifiyar ta tana cewa bata so, ranta yana Saci sosai har hakan sai ya nuna a fuskar ta. Manal tace, "Kiyi ha™uri Mama, ki cigaba da yiwa Yaya addu'a wata ran zata daina duk abinda yake yi." Mama bata ce komai ba tayi shiru kawai Manal sai ta tashi ta Wauke kwanon da suka gama cin abinci ta fita dashi ta dawo ta Wauko kayan shimfiWa Mama ta shimfiWa musu tace, "Mama nayi shimfiWa in zaki kwanta."

Kafin Mama tayi magana Mubeena ta shigo tana cewa, "ni wallahi babu wanda zai takura min, sai nayi abinda nake so bazan kuma auri talaka ba wallahi. Ni Mubeena nafi ™arfin Wan mai kuWi,  sai dai mai kuWin kan sa ba Wan sa ba. Bazai yu ace sai uban miji ya bawa mijina sannan shima ya bani ba, na fi so daga hannun mijina sai wajena. Babu wanda zan aure gwara ma Baban ya sani, dan yana ™anin mahaifin mu kuma yana auren Mama ai mahaifin mu bane. Bana son takura a bar ni na sake" ta faWa tana shigewa Waki Manal zata bita Mama tace, "kar ki bita Manali, zo ki bani ruwa na sha." Manal ta canja hanya ta kawowa Mama ruwa ta sha tace, "kashe min hasken falon ki kwanta, in kuma kin kashe shikenan."

Kamar yadda tace haka tayi ta kashe hasken Mama ta kwanta ita kuma ta Wauki alqur'ani ta koma tsakar gida ta zauna tana karantawa zuciyar ta babu daWi.  Bata son halin da Mubeena take nunawa Maman su ko kusa ko alama, tana jin haushin hakan domin yana daga cikin dalilin da ya saka ciwon zuciyar Mama ya™i sau™i saboda damuwar Mubeena.

Da sassafe Manal ta tashi tayi abubuwan da ta saba dan zasu je asibiti da Mama kuma bata so su makara, dan sau biyu suna son ganin likitan makara take hana su ganin sa. Šorawa Mama ruwan wanka bayan ta fito ta juye mata a bokiti ta kai mata banWaki sannan taje ta tarar da maman a zaune ta dafe kanta tace, "Sannu Mama, har yanzu ciwon kan ne?." Mama tace, "kece da sannu Manal, har yanzu bai sake ni ba ciwon nan kaina yayi nauyi sosai."

Manal tace, "har na juye miki ruwa saboda zuwa asibitin, Anya zaki iya zuwa ma kuwa?." Mana tace, "gaskiya bana tunanin zan iya fita, kaina ciwo yake min sosai ba kaWan ba Manal." Manal tayi shiru ta kalli ™aramin agogo falon su tace, "gashi har bakwai ta kusa, ance likitan tun shida yake zuwa. Bara na shirya naje kawai na kai result Win zuciyar sai ya bani maganin na ki." Mana tace, "Anya zai saurare ki?."

"Zan gwada Mama, tun yaushe ake saka mana ran zamu ganshi bamu ganshi ba, ga dama mun samu baza mu yi wasa da ita ba. Bara na saka kayana nayi sauri naje na dawo" ta faWa tana shiga Waki a lokacin Mubeena bacci take sosai ko alamun tashi bata yi ba, ta shirya ta saka hijjabi ta Wauki katin Mama da kuWin mota ta fito ta samu Maman ta koma ta kwanta tace, "Mama zan tafi babu abinda kike so?."

Mana tace, "babu komai Manal, sai kin dawo Allah ya kiyaye yayi miki albarka." Ta amsa da amin ta fita daga cikin gidan. Napep ta hau zuwa asibitin murtala ta sauka ta shiga ciki inda aka yi mata kwancen likitan yana zuwa nan ta hango dandazon mutane mata da maza a zaune a cikin wata rumfa da alama duk likitan zasu gani.

˜arasowa tayi wajen wanda yake tsaye da katina a hannun sa tace, "sannu da aiki." Ya kalle ta yace, "Yauwa."

"Dan Allah nan ne wajan likitan zuciya?."

"Eh nan ne, kawo katin naki." Mi™a masa katin tayi ta koma ta zauna akan abinda ake zama tana jiran azo kanta.

Ta jima sosai sama da awa Waya tana zaune kafin a kira sunan Mama jin hakan ya saka ta tashi da sauri ta karSi katin ta shiga office Win. Bebi yana zaune a kan kujera cikin manyan kaya ya sunkuyar da kai yana rubutu ta zauna ya mi™a mata hannu yace, "bani katin." Ba musu ta bashi katin ya karSa tace, "ga sakamakon gwajin zuciyar da akayi." KarSa shima yayi ya buWe takardar yana kallon ta sai ya Wago suka haWa ido da Manal ya sake kallon age din jikin katin ya sake kallon ta yace, "Zahra'u Muhammad, are you?."
Chapter 6 · 0% Book details