← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 48

Sashe 13

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace, "ba haka bane Mummy, Yawon su kaWai ne bana so" ya kalli Kausar yace, "muje." Ya mi™e tsaye ya kalli inda Mimi take ya kalli Mama yace, "mun gama magana da wanda yace yana son Mimi, ban bashi damar zuwa ba banyi binciken da nake so nayi ba, zuwa nan da jibi dai haka." Mama tayi murmushi tace, "To Baban Yaya, Allah ya taimaka." Ya amsa da amin ya wuce ya fita Kausar tabi bayan sa.

Sai da yaje wajan mota ya lura da ita a bayan sa ya bita da kallo up and down yace, "wannan wanne irin mayafi ne? Koma malama ki canja." Da sauri ta juya shi kuma ya shiga motar ba jima ta dawo ta saka abaya akan kayan ta shiga gaba ya fita daga gidan. 

A hanya ya kalle ta yace, "bakwa yiwa yayar ku Lubna faWa ko?." Tace, "Wallahi Yaya muna yi bata jin magana ne, sai tace wai takura mata ake ita da Yaya Maryam." Ya girgiza kai yace, "bata jin magana." Bata ce komai ba ya cigaba da tafiya kafin yace, "tun yaushe kike ciwon?."

"Kusan sati kenan."

"Kuma kin tabbatar ba period bane?." Ta Waga kai ta amsa da eh baice komai ba ya cigaba da tafiya har suka je asibitin ya faka motar ya fito itama ta fito suka shiga ciki.  Office Win sa suka shiga da ita akwai patient guda biyar da suke jiran sa tana zaune duk suka shigo ba jimawa suke fita har ya gama dasu sai ga Hamza da Huzaifa Win sun shigo.

Huzaifa ya kalli Kausar yace, "Kausar yau ke kika yiwa Yayan naki rakiya?." Tayi dariya ta gaishe su suka amsa ya kalli Hamza yace, "wajan ka tazo." Hamza yace, "to Allah yasa Lafiya." Huzaifa yace, "Kuje office ai kowa yana son sirri." Ba musu ya fita ita kuma bata tashi ba tana jira Bebi ya bata umarnin tafiya.

Lura da hakan sai Huzaifa yayi dariya yace, "Kausar tashi kije na baki umarni a madadin sa." Sai a sannan ya Wago dan shi ya Wauka ma ta fita a lokacin ta fita ya cigaba da abinda yake yi.

Ba jimawa ta dawo da sallama suka amsa tace, "Yaya an gama." Ya Wago ya kalle ta yace, "to yanzu ya za'ayi? Tafiya zaiyi ko zaki jira na gama?."

"A'a zan tafi dai."

"Allah ya kiyaye" ya faWa yana cigaba da rubutun sa. Sai tace, "babu kuWi a hannuna ai."

Huzaifa ne ya bata dubu biyu ta karSa tace, An gode, Yaya na tafi.

Allah ya kiyaye, ki kula. Ta amsa da to ta fita, Huzaifa yace, "wani lokacin kana burge ni akan yaran nan, wani lokacin kana bani haushi." Baice komai ba ya cigaba da abinda yake yi. Huzaifa yace, "Yauwa, wanne magani kake ganin za'a bawa matar nan ta jiya?."

"Wacce mata?."

"Mahaifiyar yarinyar nan mana da suka kwana a nan."

"Ohh! Sai naje naji yanayin bugawar zuciyar sannan nasan abinda za'ayi." Bai jima ba ya tashi zuwa Wakin ya samu Maman a zaune Manal Win na gefen ta tana bata apple da ta yanka mata ™ananu.

˜arasawayayi yace, "Sannu Mama." Mama duk da ba gani take ba sosai tace, "Yauwa sannu likita."

"Ya jiki?."

"Da sau™i" ta faWa a wahala kana ganin ta kasan tana jin ciwo har lokacin. Hannun ta ya ri™e yana sauraren bugun zuciyar ta kafin ya saki yace, "Mama saka damuwa a zuciya ba komai yake kawowa ba sai ciwo, ki kawar da abinda yake damun ki kodan Lafiyar ki."

Mama tayi murmushi kawai tana girgiza kai bata ce komai ba ya kalli Manal kamar zai magana sai ya fasa ya fita. Ba jimawa ya dawo ya bawa Manal takarda yace, "babu wannan allurar a nan sai gobe za'a kawo, zuwa dare ki bawa yayan ki a siyo ta. KarSa tayi ya fita ita kuma ta ajjiye takardar a kusa da ita.

Mama tace, "Manal wanne Yaya yake nufi?." Manal tace, "Mma ki yi shiru kina wahala in kina magana."

"Mubeena bata zo ba ko?." Manal tace, "eh bata zo ba." Mama ta girgiza kai kawai bata sake cewa komai ba.

Sai da Mama tayi bacci Manal ta fito neman wannan mutumi bata ganshi ba haka ta koma a lokacin Surayya da Maman ta sun sauke zuwa suka Wauke mata kewa har magariba sannan suka tafi. Suna tafiya yazo bai shiga inda Mama take ba ya tsaya a inda ya ganta Manal tace, "sannu da zuwa."

"Yauwa Sannun ki. Ya jikin Maman?."

"Da sau™i sosai. Tun Wazu nake neman ka an bani wata takardar magani ance a siyo allurar, da kuWi a a hannuna amma ban saninda za'a siyo ba ko zaka taimaka min."

Yayi murmushi yace, "siyan allura da magani duk aikin wanda ya Wauki nauyin Mama ne, abinda zai faru yanzu tunda tana bacci Mama kizo muje ki masa godiya daga nan sai a baki allurar. Kin San godiya tana daWi, sai yafi jin daWin sake miki wani alkhairi musamman in akace kin taka kin je har inda yake.

Manal cikin faWuwar gaba tace, "amma bi kaWai ce a wajan Mama, in na tafi waye zai zauna?."

"Ai ba jimawa zaki ba, amma in kina ganin basai kin gode masa ba shikenan." Manal murya a sanyaye tace, "ina ne inda zamu je?."

"Nan ne gidan sa babu nisa, da mu je zaki ga mata ma wanda ya taimakawa kamar ki."

"Da zamu bari sai da safe maje ko?."

"To ya za'ayi da allurar?." Manal tace, "zan siya da kuWina." Yayi murmushi yace, "kuWim ki baza su iya ba, wannan allurar da kike gani a ™alla zatayi dubu hamsin, kizo muje a siyo a yi mata dare yana yi."

Manal tayi shiru tana tunani yace, ko kina da dubu hamsin Win?. Ta girgiza kai alamun a a yace, muje.

Gaban Manal dai faWuwa yake sosai ta Waga kai alamun to ta biyo bayan sa. Mota ya shiga itama ta shiga suka fita daga asibitin, sai salati take a zuciyar ta dan ta san ba daidai take aikatawa ba. Babu nisa da asibitin sosai ya tsaya aka buWe masa gate suka shiga ya faka motar yace, "kinga masu neman taimakon ko?." Ya faWa yana nuna mata wasu mata da suke tsaye da hijjabai su biyu.

Kai ta Waga tana kallon su jikin sanyi jiki, murmushi yayi yana aiyana ai kin zo hannu yarinya ya buWe motar ya fito yace, muje ko?.

Manal jikin ta har yayi Wumi saboda tashin hankali ta fito tana kallon gidan, yana da girma sosai ga haske ko ina kamar rana, gaba yayi ganin hakan sai ta sauke numfashi suka nufi ciki kai tsaye.

*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025

©þNana Haleema.

Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

*BOOK 1*

*Page 010*

Suna daga cikin falon a tsaye a bakin window suna hango masu shigowa da masu fita, ganin Manal ta fito daga mota sun doso ciki sai Alhaji Magaji yace, "to kaga yarinyar nan an kawo maka ita, Wanya sharaf ga shegen kyau, yadda kaga fuskar ta na tabbatar ka san daga ciki ma zata yi kyau ai ka gane, ni na tabbatar ko ita wacce kake zance bata kai wannan ba. Kalle ta fa, komai yaji da gani zata yi sau™in kai, kayi abinda ka ke so kai kaWai babu mai takura maka.

Alhaji Mu'azzam yayi murmushi yace, "akwai haske kam kamar yar india, kasan ko a can ba a samun masu wannan hasken kamar madara. Hasken ta akwai Waukar hankali tun daga nesa na tabbatar. Amma ni wallahi hankalina yana ga Mubeena. Ina son yarinyar, ina kuma ™aunar ganin ta ko yaushe, saboda Mubeena ta haWu daidai gwargwado. Ganin zasu shigo sai suka koma suka zauna a lokacin suka shigo da sallama.

Suka amsa yana binta da kallo duk da kanta yana ™asa, ta tsuguna kamar yadda wanda ya rako ta ya tsuguna yace, "Alhaji gata itace mai mara lafiyar, tazo tayi maka godiya ne." Jin haka sai tace, "ina wuni." Alhaji Mu'azzam ya amsa fuska a sake yana so yaga fuskar ta sosai amma ta™i bada damar hakan, taee, "Na gode Alhaji, Allah ya saka da alkhairi ya biya bu™ata."

"Haba ai yiwa kai ne ´an mata. Kamar ku bai kamata ace kuna neman abu ku rasa ba, mu kuma in muka ga haka dole sai mun taimaka.

Wanda ya rako ta yace, "gashi takardar allura ce za'a siya, na tambayi kuWin allurar ance duba Wari ce shine nace tazo in tayi maka godiya sai ka bada kuWin."

Murmushi yayi masa alamun ya tashi ya tafi, ya kalli Alhaji Magaji sai ya mi™e yace, "Nidai zan wuce sai gobe." Ya Waga masa kai kawai, falon ya rage daga ita sai shi sai ihun a.c. Ya fito da kuWi daga aljihu sa ya ajjiye yace, "zo ki karSa aje a siyo. ya faWa yana mika mata kuWin, ta taso ta ™arasa zata karSa sai ya haWa da hannun ta ya ri™e, da ssuri ta kalle shi gaban ta ya faWi suka haWa ido sai yayi murmushi yace, "kar ki damu ba komai bane wannan."

Hannun ta ta zame ba ta karSi kuWin ba ta matsa baya yana kallon ta yace, "bakya son kuWin?."

"Bana so indai sai ka ri™e hannuna." Yayi murmushi yace, "kin amince kar a yiwa Maman ki allurar kenan?." Tayi shiru bata amsa amma tsoro ya gama mamaye ta, dana sanin zuwa kuwa kamar ta cakawa kanta wu™a saboda takaici yace, "kar ki manta ba'a biya kuWin asibitin ba sai za'a sallama ku, kinga kenan ke zaki biya duka abinda aka kashe in ba haka ba su kama ki. Wannan ai ba komai bane ki amince na baki kuWin ki tafi. Kamar baki waye ba ´an mata? Wannan ai ya zama normal ba wani abin damuwa bane.
Chapter 13 · 0% Book details