← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 48

Sashe 5

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mimi tace, "in baza ki je ba sai ki faWa mu kama gaban mu, Kausar muje in ya tambaya muce tce ya takura mata." Tare suka fita, Mimi haushin Mamy take ji ganin a gaban take wannan maganar ta amma bata ce komai ba. Basu san ya abin ya faru  ba sai gano Lubna Win sukayi  ta fito.

Suna shiga falon nasa suka same shi a zaune yana sanye da glasses a idanun sa fari wanda yake taimaka masa wajan kallon takarda da wani document a hannun sa yana dubawa. Sallama da suka yi ya saka ya kalle su ya amsa tare da ajjiye littafin yana kallon su suka ™araso suka zauna akan kan carpet Mimi tace, "Yaya gamu." Kai ya girgiza alamun na gan ku kafin ya ce, "tambayar ku nake so nayi, ina so ko wacce ta faWa min asalin abinda yake zuciyar ta. Bana son ™arya ku faWa kai tsaye kar a Soye min."

Basu ce komai ba ya kalli Mimi yace, "me kika shiryawa rayuwar ki a yanzu? Aure ki ke so?." Yadda yayi tambayar ya saka ta kalle shi suka haWa ido dan bata kawo abinda zai ce ba kenan ya Waga mata kai yace, "asalin abinda yake zuciyar ki nake son ki,aure kike so?." Mimi ta sauke kai ™asa tace, "ni Yaya abinda Allah ya tsara min shine daidai."

"Kowa ma haka Mimi, but there's something on your mind that you wish to happen in your life, maybe aure maybe kuma karatun kike so ki gama har ki fara aiki."

Mimi tace, "Yaya ina so, amma nafi so na kammala karatun tunda kaga ina final year."

"Are you sure?." Ta girgiza kai alamun eh. Kallon Kausar yayi yace, "sai ke what's your plan about yourself?." Kausar tce, "ni Yaya ina karatu, in auren yazo zan karSa. Amma kaga yanzu ko saurayi ma bani dashi, karatun shine a kan gaba."

Ya girgiza kai ya kalli Lubna yace, "ke dai daman nasan auren ki ke so ko?." Ta girgiza kai alamun a'a yace, "then what?." Tayi shiru bata amsa ba yace, "in ba haka bane a ranki meyasa kike tara samari? Yau in na ganki da wannan, gobe da wannan an ganki. Kuma dukkan su babu wanda zai aure ki a cikin su duk ´an Sata lokaci ne, wannan wanda na ganku Wazu nayi miki warning a kan sa amma baki ji ba. Ta™amar ki shima ai abokina ne, na fiki sanin abokina ne, shiyasa nace ki barshi sboda na san shi din amma baka jin magana Lubna."

Lubna tayi shiru bata amsa ba yace, "duk wacce take ji a zuciyar ta she's ready to get married please let me know zan tabbatar ta samu abinda yake so. Abu Waya ne bana so ku dinga hiding abinda ku ke yi ko ku ke so a gare ni, baku san duk wani motsin ku akan idona kuke yin shi ba shiyasa. Ke Kausar ai baki nasan na san kinje Sufi mart ba Jiya. Mimi Wazu kinje biki baki sanar dani ba." Shiru sukayi dukkan su ya kalle su yace, "zan muku duk abinda kike so amma ku tsayar da hankalin ku waje Waya, bana son kula samari barkai musamman ke Lubna" ya faWa yan nuna ta da yatsa.

"Kece Babba a cikin su amma kin fi kowa wannan rawar kan, ki dawo hankalin ki kafin ranki ya Saci,  na sake kama ki da makamancin wannan zan baki mamaki.  duk wanda yace yana son magana dake invite him to come over and talk to me, sai muyi magana akan ki na san waye shi da komai na shi, I'll only let him to talk to you if i trust him, otherwise l'll reject to him. Bama ke kaWai ba dukkan ku, in na samu wata da akasin haka gaskiya ranku zai Saci" ya faWa yana nuna su gabaWayan su.

Mimi tace, "To Yaya in sha Allah zamu yi abinda kace." Ya sauke numfashi yana kallon su yace, "good. Akwai abinda kuke so?." Mimi da Kausar aka kalli juna kafin Mimi tace, "daman Yaya gobe akwai get together na class mate Win mu tun na secondary ina so naje." Ya kalli Mimi yace, "which time?."

"Around 4pm."

"Where?."

"Green pack." Yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "okay zan saka a kai ki." Tayi murmushi tace, "na gode."

"Baku da abin cewa?" Ya faWa yana kallon su suka ce babu yace, "okay zamu iya tafi, zan tura muku kuWin kati."Suka yi murmushi dan sun san kyautar sa a gare su akai daWi suka fita ya bisu da kallo.

Allah ya sani baya so wani abun ya samu Waya daga cikin ™annen sa mata, yana tattalin su sosai musamman yanzu da duniyar ta gama lalacewa kowa ba abin yarda bane, baya son yaga wani abun da zai Sata musu rayuwa shiyasa bai basu fuskar sauraren ko wanne namiji ba, sannan bai basu fuskar karSar komai a hannun ko wanne namiji ba. duk da iyayen su suna da halin da zasu basu kuWi amma yana yawan basu kuWi da canja musu waya saboda kar rashin basu yasa su tambayi saurayi. GabaWaya aikin da mahaifin su ya kamata a ce yayi ya dawo kansa bashi, tunda yayyen sa maza guda biyu kowa yana gidan sa shine tamkar uba a wannan lokacin, shiyasa bashi da nutsuwa sai yaji sun kwana lafiya sun tashi lafiya wani abun bai sake su ba. Gashi Allah ya yi shi a mutum mai kishin ´an uwan sa, baya so yaga suna kula ko waye balle saurayi.

Ajiyar zuciya yayi a bayyane yace, "Abba!." Kai ya girgiza kawai yana jin haushin halin mahaifin su amma ya zaiyi ba'a canja uba dolen sa dai shine mahaifi a gare shi. Tashi yayi da niyar shiga Waki sai yaji ana buWe  gate ya ™arasa wajan window yana kallo sai yaga motar mahaifin su ta shigo kawai ya saki labulen dan bai ga amfanin dawowar tasa ba dan da safe zai ce zai koma.

Yana zaune yana cigaba da duba takardun hannun sa yaga wayar sa na haske ganin sunan Abba ya saka shi kulle ido ya buWe ya Wauka da sallama yayi shiru alamun ana amsawa kafin ya tashi ya fita waje. Kai tsaye Sangaren Abba ya nufa ya same shi a zaune a kan kujera ya shiga da sallama ya amsa ya ™arasa ya zauna a kasa yace, "barka da dawowa Abba, ina fatan an dawo Lafiya."

"Lafiya lau Adna, ya aikin naka?."

"Alhamdulillah" ya amsa a ta™aice daga nan bai sake cewa komai ba.

Abba yace, "sai ha™uri aiki ne suke min yawa ga shirye-shiryen zaSe mai xuwa shiyasa abubuwan sai a hankali." Adnan yace, "amma Abba duk mahimmacin abinda ka saka a gaba bai kai mahimmacin iyalan ka ba."

"To iyalai na me suka rasa Adnan? Babu abinda babu a gidan nan koda babu ni na tabbata baza ka bar wani yayi kukan babu ba. Yadda kake kula da iyayen ka da ´an uwan ka ko ni bana kula dasu, indai kana da rai ragamar g1dana tana hannun ka dan na yi shekara bana gida bazan damu ba."

Adnan ya kalle shi Wan daman shi ne kawai mai iya faWa masa gaskiya yace, "Amma Abba ko mu yaran ka  ace babu ha™™in mu a kan ka akwai iyayen mu mata, dukkanin suna bu™atar kulawar ka wacce a wajan ka kawai zasu samu, ni da ka bar min komai a hannuna bazan iya samar musu da kulawar da zasu samu a wajan ka ba. Idan zan iya kula da ´an uwana su kuma fa Abba?." Alhaji Mu'azzam Alhassan ya kulle ido ya buWe yace, "Haba Adnan! Iyayen naka bafa yara bane da kake wannan zancen a kansu, dukkan su babu wacce bata aurar da yara a cikin su ba har da jikoki, to me suke nema a wajena kuma?."

"Kulawar ka suke so Abba domin matan ka ne, na tabbatar ka san suna bu™atar hakan." Yayi murmushi yace, "gashi ai na dawo, zan kuma yi sati a nan duk kulawar da suke so zasu iya samu a cikin kwanakin da zanyi." Kallon sa Adnan yake yi zuciyar sa gabaWaya babu daWi yaja bakin sa yayi shiru bai ce komai ba kafin Abba yayi magana Mamy da Mama suka shigo da sallama ya amsa sai Adnan ya mi™e yace, "Abba sai da safe."

"Allah ya tashe my Lafiya, da safe kafin ka fita kazo nan Ina son ganin ka, koda ina bacci ka jira ni. Maganar da na kira ka muyi bamu samu ba zamu yi daga baya."  Ya amsa da to ya fita. Kallon Mamy da Mama yayi da suke zaune ko wacce fuskar sa babu yabo babu fallasa yace, "ko wacce ta shigo tana shan kunu kamar wanda aka yiwa dole."

Mama tayi murmushi kawai bata ce komai ba ta mi™e tace, "barka da zuwa muka zo muyi maka daman, da fatan an dawo Lafiya." Yabi Mama da kallo ita kuma ba shi take  kallo ba yace, "Sannu da zuwan ce sai an tashi tsaye?."

Mama tace, "Ina sauri ne zan je na kwanta, sai da safe" ta faWa tana hanyar fita Mamy ma ta mi™e tace, "jira ni mu koma yadda kuka shigo tare" ta faWa tana tashi tsaye itama.

Mama ta kalle ta tace, "baza ki zauna a nan ba?."

"Lissafina ya kwace min bazan iya banbance wacece ma ya kamata ace ta kwana a nan Win ba, ga dai abinci nan Maryam zata kawo yanzu" ta faWa tana fita ta bar Mama a tsaye dan har ta riga taficewa. Mama na shirin fita tace, "kar ki fita Hauwa, dawo ki zauna muyi magana." Ta juyo ta kalle shi tace, "ko meye ma tattauna da safe in Allah ya nuna mana, ka kwana lafiya" ta faWa tana fita ya bita da kallo yana murmushi.
Chapter 5 · 0% Book details