← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 48

Sashe 41

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mama zata zauna a nan har sai gobe da safe, saboda ta sake samu sau™i sosai sai ku koma." Kai ta Waga kai ta yun™ura zata tashi yace, "ki koma ki zauna."

"Zan faWawa Mama sai gobe ne."

"0n kin koma tayi bacci." Ta kalle shi tace, "ya akayi ka sani?." Ya kalli agogon hannun sa yace, "Lokacin tayi baccin ne yayi." Ganin bata amince ba sai yace, "kije ki duba, in kin tabbatar tayi baccin ki dawo."

Fita tayi taga Maman tayi bacci kuwa sai bata koma ba saboda kiran sallar magriba da ake yi, sallah tayi tana zaune kusa da Maman Baba ya dawo ya shigo Wakin suka cigaba da zama kafin ya fita lokacin i'sha tayi sallah itama Bab ya dawo yace, "Manal baki ci abinci ba, gashi Dr Adnan ya faWa min zata kwana a nan saboda ta sake warwarewa gobe sai mu koma gida."

Manal tace, "Bana jin yunwa ma Baba."

"Zaki ki yunwa Manal, zan saka nemo miki abinda zaki ci."

"Allah bana jin yunwa."

"Ai kwana zaki ko kin manta ne?."

Ta girgiza kai tace, "Ban manta ba, basai naci komai ba." Baba yace, "To shikenan." Suna nan zaune har tara na dare sannan Baba ya tafi ya barta bayan ya tabbatar da Haroun ya tawo.

Ita kuma ta fito ta zauna a kofar Wakin tayi tagumi kamar wata marainiya. Huzaifa da yake niyar tafiya gida ya gano ta ya ™araso yace, "Manal ba dai jikin Maman bane?." Tayi murmushi tace, "A'a Dr, bacci ma take sosai."

"Haka ake so, zan wuce ni gida amma Bebi yana nan nasan zai kula da komai."

"Allah ya saka da alkhairi."

"Kar ki damu an zama Waya ai." So yake ya tambaye ta maganar Bebi amma sai ya kasa sai daga baya yace, "kin san waye Bebi Win?." Ta Waga kai alamun eh yace, "Yauwa, duk abinda yake damun ki ki sanar dashi."

Ta amsa da to yayj mata sallama ya tafi badan haka yaso ba yaso yaji meye ala™ar su da shi. Tana nan zaune sai ga message a wayar ta ya shigo ta buWe taga Adnan ne yace, _ki tashi daga nan ki shiga Wakin da kika zauna Wazu, sai zuwa sha Waya Mama zata farka._ kallon wajan tayi taga baya nan, abin bai bata mamaki ba ta san bazai wuce ta camera ya ganta ba, tashi Win tayi ta shiga dan ta gaji da zaman.

Tana shiga ta zauna akan kujera babba ta jingina, buWe ™ofar akayi aka shigo sai ga wata nurse da abinci tace, "Dr Adnan yace a kawo miki." Murmushi tayi ta karSa tayi godiya ita kuma ta koma. BuWe pack din abincin tayi shinkafa ce basmati fara tass ga miya a wani pack Win sannan ga salad mai yawan gaske yaji uban cucumber.

Fara ci tayi a hankali taci rabi ta tashi ta sha ruwa a water dispenser ta dawo ta zauna tana murmushi a zuciyar ta.

Knocking ™ofar aka yi ta amsa ya buWe ya shigo ta kalle shi ya kalli abincin yace, "baki ci ba?."

"Naci, ya ishe ni, na gode."

"Šazu kafin nazo waye ya kawo ku nan?."

"Dr Huzaifa ne, shi na kira na sanar dashi, na ruWe na manta ma ba faWa maka."

Ya girgiza kai yana kallon ta yace, "baki taSa bani labarin kina da number Huzaifa ba, bayan nace miki bana so kiyi min hiding komai." Manal da mamaki tace, "ban Wauka ya shiga ciki abinda kake nufi bane, beside na jima ina da number shi tun muna zuwa babban asibiti, ina kiran shi a waya in yana nan muje in baya nan sai mu fasa zuwa." Ya girgiza kai yace, "Baki bani labarin ala™ar ku tayi girma haka ba ai."

Manal tace, "yana da kirki sosai har yaso ya fika, yana Wauka na kamar ™anwar sa nima ina Waukar shi Yayana. Kai tsaye zan iya kiran shi kafin na kira ka." Ran Bebi ya sosu sosai bai magana ba ta kuma cewa, "Saboda wani lokacin kai sai aga kamar baka son ma ayi maka magana." Ya sauke numfashi yana kallon ta ta ™asan ido cikin ™unar rai yace, "shi kuma wanda ma gan ku da safe tare fa? Sau biyu ina ganin ki dashi akan titi kuna hira, shi kuma waye Win ki? Shi ma yafi ni Win ko?."

Nana Haleema>ØBÝd'þ

*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025

     ©þNana Haleema.

Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

_Kina neman inda zaki siyi abinci mai daWi? Kina ™iyar yin girki gashi zaki yi ba™i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daWi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daWi akwai a lallaSa. Kina son ki siyi abincin da zaki Wauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daWi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan Sangare, tazo muku da nau in abinci kala-kala na gargajiya da na ™asar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._

_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ™asan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr

Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.

*BOOK 1*

*Page 26.*

Manal ta kalle shi cikin mamakin abinda yace tace, "ka gan mu da safe? A ina to?." Ya jingina da kujera ya Wora ™afa kan Waya yace, "ki bani amsa." Manal ta yatsine fuska tace, "Yaya Haroun ne, Yayana ne, kuma ka san shi."

"Baki bani labarin kina da Yaya ba."  Kallon sa tayi tace, "komai sai na faWa maka?, kuma ranar da kazo gidan mu ya kira ni a waya ai na faWa maka ko?."

Da ido ya bata amsa ya kulle shi ya buWe alamun eh ta kawar da kai tace, "kai ba komai ka faWa min ba ai" ta faWa tana kallon agogo kafin tace, "Lokacin tashin Mama yayi kamar yadda kace, zan koma wajan ta." Baice mata komai ba ya ta fita yayi murmushi bayan ta fita, Allah kaWai yasan yadda yake matu™ar farin ciki in yana zaune gashi gata. Sau uku kawai suka zauna tare amma bazai manta da wannan ranakun ba gaskiya.

Kamar almara tana shiga taga Mama ta farka dan tana zaune ma ta ™arasa tace, "Mama kin tashi?."

"Eh Manal, ina kika je?."

"Ina zaune a wani Waki a can ma naci abinci."

"To zo ki taimaka min nayi sallah, dare yayi ko?."

"Eh Mama, har ta wuce tayi." Mama tace, "Subahanallahi." Taimaka mata tayi ta sauka tayi alwala ta tayar da sallah.

Sai bayan ta idar Manal na zaune Mama tace, "Manal ina ganin hasken Wakin nan da kaWan-kaWan." Manal tace, "da gaske Mama? Kina iya ganin Wakin nan?" Ta tambaya a ruWe da farin ciki.  Mama tayi murmushi tace, "ina iya ganin hasken Wakin amma ba sosai ba."

"Bara naje na faWawa Dr ko akwai abinda za'a yi." Mama tace, "yi zaman ki ki huta, Mubeena bata zo ba ko?."

Manal tace, "tare muka zo sai Baba yace ta koma gida." Mama bata ce komai ba tayi shiru Manal tace, "Mama abinci fa?."

"Bar shi Manal naci da safe."

"Safe kuma Mama? Bafa kici abinci ba kwata-kwata."

"Yanzu in nace zanci a ina zaki samo? Sai dai ki faWawa Adnan a kawo min kuma ni bana so. Yaron nan bai fa aure ki ba har yanzu, kin ce baki gama tunani akan zaki iya auren sa ba ko baza ki iya ba, tun yanzu muna Wora masa wahalar rashin lafiyata?, ko ya aure ki kula dani ba a kansa yake ba balle bai aure ki ba. Da na san ma shi zaki kira da ban faWa miki bani da lafiya ba. Matsayin sirikina yake a yanzu, bai aure ki ba baza'a dinga Wora masa wahala ba. Ko ya aure ki ha™™in kula dani ba a kansa yake ba."

"Assalamu alaikum." Aka faWa daga bakin ™ofa mai share-share na asibitin ya shigo da leda a hannun sa yace, "Barka da dare, ya mai jikin?." Manal ta amsa ya mi™a mata yace, "Gashi in ji Dr Adnan." Manal ta karSa tayi godiya ya fita ta kalli Mama tana buWe

abincin tace, "gashi ya aiko dashi."

Mama ta girgiza kai tace, "Bana jin daWin haka Manal, nauyin sa nake ji wallahi."

"To Mama bani nace masa ya kawo ba ai."

"To sai ki bani naci."

Manal tayi murmushi ta koma kusa da ita ta buWe mata tana ci. Sai bayan ta gama cin abincin Adnan ya shigo da sallama ya kalli Mama yace, "Mama ya jikin?."

"Da sau™i sosai Adnan, har ciwon ma na daina ji." Manal tace, "Mama tace tana ganin hasken Wakin nan." Mama ta taSa ta tace, "Manal!." Manal tace, "Mama bazan iya shiru ba, kiyi ha™uri."

"Daman ke ai bakya iya shiru." Manal tayi murmushi Bebi yace, "Ana samun cigaba sosai, zan aiko da magani yanzu ki saka mata a idon ta, sannan akwai glasses da zan baki tana amfani dashi."

Manal tayi murmushi tace, "To" sai ta kalli Mama tace, "Mama kin ji ko? Kar kice na takura miki da magani wani sabo za'a bayar." Mama tayi murmushi ita nauyin ma Adnan Win take ji, Bebi ya fita ba jimawa aka aiko da maganin ta sakawa Maman suna ta hira sama-sama.

Adnan ya gama komai amma bazai iya tafiya ba haka ya kwana a asibitin, har bakwai na safe yana asibitin a lokacin ake medication nurses suna bi Waki-Waki suna bawa a marasa lafiya magani.

A lokacin Huzaifa yazo da mamaki yake kallon motar Bebi ganin inda ya barta jiya, ya shiga ciki yaga dai yana nan kuma gashi da kayan jiya da alana kwana yayi, ya bishi da kallo yace, "Daman kwana kayi?."  Idanun sa lumshewa suke saboda bacci Adnan yace, "Uhum! Yanzu zan tafi."

"Wai saboda Manal Win ka kwana ka yini kana aiki?." Kallon sa yayi bai ce komai ba Huzaifa yace, "ai na gama fahimtar itace wacce ka ke so Win, daga yi maka wasa jiya ka canja."
Chapter 41 · 0% Book details