← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 48

Sashe 20

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama tace, "ya isa ki daina min kuka. Duk duniya in akwai wanda Adnan yake jin maganar sa to nice, meyasa kika kasa amincewa da nace miki shine mijin ki?. Ko kina kokwanto akan umarnina ne?."

"Mama ba na™i amincewa bane ba, Ina jin tsoron yadda ya dage kan maganar ne."

"Kar ki damu, ki kwantar da hankalin ki sai Adnan ya aure ki in sha Allah."

Ta goge idanun ta tana jan numfashi tace, "Kuma

Mama har wata na gani a motar sa Wazu, dana tambaye shi sai yace wai wacce zai aura akwai abinda zanyi ne."

Mama da mamaki tace, "mace a motar Bebi?."

"Eh wallahi Mama na gansu."

Mama ta girgiza kai tace, "wannan ba komai bane kar ki damu, ya faWa miki haka ne dan ya Sata miki rai amma bashi da wata budurwa. Saboda son da yake miki tunda kuka rabu bai sake yin wata budurwar ba."

Mimi da take kallon Rumana tace, "to wai Yaya Rumana tun da kin san kina son sa kika rabu dashi kika auri wani?. Tun tashin mu tare muka san ku, ko da baya nan yana karatu kowa ya san Yaya Bebi ke yake so, amma lokaci Waya kika juya baya kika ce ke sam baza ki aure shi ba kuma aka ™yale ki, dan yanzu yace baya son ki sai a takura shi?."

Mama ta harare ta tace, "ya ishe ki malama, tashi ku bani waje." Duk tashi sukayi suka fita dukkan su basa fatan ya aure ta dan lokacin da ya nuna son auren nata wula™anta shi tayi ta nuna bai kai wannan matsayin ba saboda ta samu wanda yake da mahaukacin kuWin ya Wauke ta suka koma Dubai da zama, sai gashi auren bai je ko ina ba ya mutu.

Rarrashin ta Mama ta dinga yi har taga ta daina fushi ta daina kukan sannan tace taje ta kwanta ta fita ita kuma ya kira Bebi a waya. Yana zaune a lokacin ya rasa wanne irin tunani ma zaiyi komai ya tsaya masa ya tsani zancen auren Rumana da ake masa wallahi, baya qaunar hakan in badan Mama bace babu wanda zai dinga yi masa zancen nan ya zauna lafiya. Wayar yaga tana haske ganin sunan Mama sai ya Wauka sai kuma ya sauke waye ya tashi daga inda yake ya fito zuwa wajan Mama.

Falon mata babu kowa y shigo Wakin ya same ta a zaune ya zauna shima yace, "Gani Mama." Ta kalle shi rai a Sace tace, "Yanzu tsakani da Allah ka kyauta abinda akayi?." Da mamaki ya kalle ta yace, "Me nayi Mummy?."

"Kai yanzu na Wauka in wani zai cewa Rumana ragowar wani kaini zaka kare ta sai inda ™arfin ka ya ™are saboda sha™uwar ku da kasancewar ta ´ar uwar ka, sai gashi kaine kake faWa da kanka Bebi, hakan daidai ne?." Numfashi ya sauke haushin ta ya ninku a zuciyar aa yace, "Mummy ™arata ta kawo kenan?."

Mama ta fusata cikin faWa tace, "ita ta kawo, ko kana ganin bata kawo kuka gidan magani ba?." Ya girgiza kai alamun jin abinda ta faWa cikin faWa yace, "A'a, ki yi ha™uri."

tace, "meye laifin yarinyar nan ne wai? Laifin ta abinda tayi kuma ta gane kuskuren ta tace ka yafe mata,  kar ka manta daman Allah yayi ba kaini mijin ta na farko ba, babu wanda zai canja ™addarar meyasa ka ke wannan fushin bayan har yanzu kana sonta?."

"Wallahi Mama bana sonta, Soyayyar da nake mata kamar ta sauran ´an uwa ne amma waccan soyayyar ta jima da gushewa."

Mama tayi mamakin abinda yace amma bata nuna masa ba tace, "™arya ne Adnan, ita ka fara so a rayuwar ka, soyayyar farko da wahalar mantawa take, domin tana da tasiri a zuciyar wanda yayi ta. tana nan a cikin zuciyar ka inda zaka bincika sosai zaka gani har yanzu kana son Bebi."

Shiru yayi baice komai ba yasan Mama baza ta taSa fahimta ba  gashi baya son mata musu tace, "ka adana kalaman ka akan ta domin matar kace wacce zaka aura, ku fara daidaita kan ku kafin maganar nan taje gaba." Nan ma baice komai ba amma mamaki abinda yake bashi, ita lokacin da ta guje shi babu wanda ya mata dole amma shi yanzu ana so ayi masa dole a kai dan babu yadda zaiyi.

"Tace min taga wata a motar ka da gaske ka Wauki wata yau?." Lumshe ido yayi ya buWe gabaWaya haushin ta ya sake cika masa zuciya tunda gashi har ta fara haWa shi da mahaifiyar sa tun kafin auren yace, "eh Mummy haka."

"Wacece ita?."

"Wacce nake so!" Ya faWa ba tare da ya shirya ba yana kallon Mummy Win dan so yake yaga yanyin ta,  itama tana kallon sa da mamakin abinda yace Mama tace, "har ka samu wacce kake so babu labari?." Adnan yace, "ina son sanar miki sai yanzu na samu dama."

Mama ta kalle shi kallon baka isa ba tace, "amma kasan kayi  gangancin fara son wata bayan Rumana tana da rai ko?." Ya kalli Mama yace, "Mummy yanzu saboda Ruman sai a hana ni abinda nake so?." Mama ya Waga  kai tace, "™warai kuwa, ai bama za'a hana ka ba, an ma hana ka Win Adnan. Sannan kayi gaggawar bawa zuciyar ka ha™uri akan wacece ka gayyato soyayyar ta Rumana ta maye gurbin ta  domin gida bai ™oshi ba baza a kai wa dawa ba Adnan."

Shiru kawai yayi baice komai ba dan bai san abinda zai ce ba  Mama tace, "kaje kayi abinda nace, sannan cikin satin nan ku shirya kan ku kai da ita wata mai zuwa ayi auren ku a huta. Ita kuma waccan ka faWa mata an yi maka mata a gida." Kamar ana zuba masa ruwan zafi haka yake ji a zuciyar sa in ana zancen auren Rumana,  baya so ko kusa ko alama, har mamakin Mama yake wai yace an masa mata kamar wani mace. Mama ta kalle shi tace, "zaka iya tafiya ka kwanta, ka kashe min hasken Wakin." Da to ya amsa ya tashi ya fita itama ta kwanta.

A haka ya koma Waki yana mamakin wannan abu da ake son yi masa mai kama da auren dole, zama yayi yana tunani gaskiya baya son auren Rumana badan baya son yiwa Mama abinda take so bane sai dai in ya auro Rumana kamar ma maganar ta tayitasiri a kansa kenan, dolen da take cewa ta tabbata a kan sa kenan, ya bWe ido yace, "Allah kada ka ™addara min auren ta, Allah ka kawo min abinda zanyi da gaggawa na gujewa auren ta" ya faWa yana sake kulle idanun sa domin samo mafita ya zamar masa dole kafin ayi masa auren dole.

iPhone Win Bily take kallo tana  kallon Mubeena tace, "iPhone 16 pro max, kuWin ta ya kuwa five millions a yanzu, Sannan ga kuWi  har naira dubu Wari bakwai just for ice cream. Wow! Mubeena you have to me very careful akan wannan tsohon. Kamar ba da aure yake son ki ba akwai wani abun a zuciyar sa."

Mubeena tace, "Bily ke kike cemin ya kamata na samu wayar da zan ri™e saboda a dinga ganina big girl, i've finallay fulfilled my dreams. Meyasa bakya murna?." Bily tace, "ban amince dashi bane Mubeena, dan nace ki samu waya ai bance kiyi komai ki samu waya ba, beside bance ki biyewa kowa ba."

"0n ba ta haka ba da wanne kuWin zan siyi waya? Nifa na faWa miki babu wani zance na banza da ya taSa min, In dai ba ina kewar ki ba dama kina kusa dani, shikenan fa."

"Kissing naki da yayi fa, shima hugging Win ba komai bane?." Mubeena tabi Bily da kallo tace, "Bill wallahi mamaki kike bani, Meye a cikin kiss da hug dan Allah? It's normal abu da yake faruwa tun a secondary school. Maza nawa kika yi hugging da Muna school?."

Bily tace, "wannan ya wuce ak Mubeena, lokacin ba wani hankali ne damu ba ai. Muna maganar yanzu ne ba wani abun ba." Mubeena tace, "abinda kayi da dan ka yi shi yanzu ai ba komai bane Bily."

Bily tace, "okay naji, in Mama ya warke taga wayar nan a hannun ki me zaki ce mata?."

"Da wanne idon zata gani?."

"Shine ™arfin guiwar ki? To Baba fa?.

"Shine ya haifan? Ubana ™asa ta jima da rufe idon sa babu wani mijin mahaifiyata da yana auren uwata da zai latsa ni." Bilkisu ta girgiza kai tana kallon ta tace, "kin yi nisa bakya jin kira" ta faWa  tana shiga toilet ta barta a wajan ita kuma tan sake kallon sabuwar wayar ta.

           Washe gari ma da wuri Bebi ya fita koda yaje asibiti theater sukayi bai samu yaje inda su Manal suke bama sai kusan sha Waya na safe sannan ya shiga inda Maman take ya samu zuciyar ta t dawo bugawa normal sai jiran tashin ta. Yana fitowa daga Wakin suka haWa ido da Manal ta saka black Win hijjab yayi mata wani mahaukacin kyau, ganin sa sai tayi murmushi ta ™araso tana jan ™afa tace, "ina kwana, tun Wazu nake jira kazo ka faWa min ya jikin Mamana, Yaya Dr Huzaifa bai zo ba balle ya faWa min a madadin ka."

Kallon ta kawai yake yi, na farko tayi amsa kyau sosai bazai ™aryata zuciyar sa ba, na biyu ya fuskanci yarinyar akwai surutun kafin ya amsa gaisuwa ta faWi ma abinda yake ranta.

Šauke kai yayi daga kallon ta yace, "tana lafiya kar ki damu."

"Ko yaushe haka ka ke cemin, dan Allah ina son na ganta." Hanyar ya bata alamun ta shiga tayi hanzari zata wuce sai ta taya tace, "Wayyo." sai kuka ta cigaba da jan ™aafar ta shiga Wakin.

Bata jima sosai ba ta fito tan dar1ya da kuka tace, "naji daWin ganin Mama da aka cire mata oxygen, na gode da kulawar da kake bawa Mama. Duk da baka dar1ya amma kana da mutunci." Dariya yayi a zuciyar sa ya kalli ™afar ta yace, "Jiya kika ce ™afar ki bata ciwo."

"Yau ta fara."
Chapter 20 · 0% Book details