← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 48

Sashe 23

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zama tayi sannan yace, "Yauwa. Wannan saurayin naki" sai yayi shiru yana shan ruwa kafin yace, "mun gama magana dashi zai zo gobe, da yau ne ma zai zo sai da ya kira ni nake sanar dashi na manta ban sanar dake ba amma gobe yana nan zuwa" ya faWa yana kallon ta.

Da to ta amsa Mama ta kalle shi tace, "ka gama yi masa interview Win kenan ko?." Yayi murmushi baice komai Mama tace, "wata™ila a haWa auren naku kai da ita ai, in Allah yayi shine mijin ta shikenan faWuwa tazo daidai da zama sai ayi auren naku a wuce wajan."

Shi dai baice komai ba yana cin abinci Mama tace, "ko ba haka ba Rumana?." Rumana tayi ´ar dariya tace, "Haka ne Mama." Sai da yaci abincin sosai sannan ya tashi yace, "yau ban shiga wajan Mamy ba, zanje mu gaisa daga nan bazan fito ba sai gobe."

Mama tace, "Allah ya tashe mu Lafiya" ya amsa da amin ya juya zai fita Rumana tace, "Gud night Beb." Bai amsa ba bai kuma juyo ba ya fice daga falon haushin ta yake ji sosai a zuciyar sa, ita ko kunyar Mummy bata ji ta dinga abu kamar mara hankali.

Wajan Mamy y shiga da sallama ta amsa a ciki bai ma lura da yanayin ta ba ya zauna yace, "Mamy barka da dare, yau ban shigo mun gaisa ba gabaWaya."

"Barka, ya aikin?." Sai da ya kalle ta jin a yadda ta amsa kamar bata so, amma sai bai nuna ba yace, "Alhamdulillah."

Maryam da take gefe tace, "wai Bebi meye damuwar ka da Kamal ne? Dan rashin kunya da rashin mutunci har cikin gidan sa kije ka ci masa mutunci? Meya tare mata wai? In ma bibiyar tawa yake ina ruwan ka ba rayuwa ta bace ba?." Kafin yayi magana ta sake cewa, "dan tsabar wula™anci da raini shine Wazu kace wai kar a barni na fita da yake ga wacce ka haifa ko?, ko kuma ga gidan da ka gina ubana?."

Bebi yace, "Duk abinda nake yi ina yi ne saboda rayuwar ki, badan son raina ba ko kuma dan ra'ayina ba....." a fusace ta katse shi tace, "Ina ruwan ka da rayuwar tawa? Ka cire hannun ka daga cikin rayuwar tawa mana sai me?."

Ya kalli Mamy tace, "Mamy nasan ke kin fahimci abinda nake nufi, ya kamata ki mata faWa abinda take yi ba daidai bane nan gaba zai jawo mata dana sanin da har ta mutu baza ta daina ba. Meye amfanin kula mijin da ya rabu da kai har da zama dashi a mota ko ina a kulle da sunan gaisawa?. Ko Wazu shine ya ajjiye ta a ™ofar gidan nan, meye amfanin aikata hakan a wajan ta don Allah?."

Mamy tace, "A'a Bebi, Wazu nice na aike ta kasuwa, kuma dan sun gaisa da tsohon mijin ta kamar ba laifi bane ba ai ko?." Jin abinda Mamy tace sai ya kalle ta da mamaki sosai yace, "Mamy kina goyan bayan hakan kenan?."

"Ai babu wanda zai ™i hakan sai kai, ka hana Lubna sauraren Mujahid kawai dan bai maka ba, ko kuma dan ta samu miji su Mimi basu samu ba shine damuwar ka?."

Maryam tace, "ba dole ba, kishin ´an ubancin ne ya tashi shiyasa yake so ya korar mata shi, yadda nasa basu samu ba itama ta zauna haka."

A fusace ya kalle ta yace, "Kul kar ki sake faWar haka in ba haka ba zaki nadama. Mimi, Lubna, Kausar, Maryam da Farida duka Waya ne a wajena basu da wani banbanci sai na halitta. Kuma bara kiji, ko me zai faru sai na tabbatar na raba ala™ar ki da Kamal wallahi, haka itama Lubna indai ina da rai bata isa ta auri Mujahid ba, duk abinda zaku ce kuce wannan kamar umarnina ne babu wanda ya isa ya canja shi koda Abba ne, dan ni kaWai nasan hatsarin da yake cikin abinda kuke son yi. Sam baki San abinda kike yi ba, miji ya sake ki saki uku amma kice kike biye masa har ake zama a mota ana tuna rayuwar da ta wuce ana dariya, hakan a wajan ki daidai ne ko kuma wayewa. Rashin sanin darajar kai ne, da kuma rashin sanin ciwon kan ki da bakya yi, ki gyara rayuwar ki ko dan yaran ki" ya faWa cikin faWa dan tasan daman dole zaiyi haka baya jurewa tension, kuma in ransa ya Sac1 kome yazo bakin sa faWa yake kuma a gaban kowa.

Maryam ta kalli Mamy tace, "Mamy kina jin abinda yake cewa ko?" Ta sake kallon shi tace, "ni kuma wallahi sai Lubna ta auri Mujahid sai dai duk abinda akayi kayi" ta faWa shi lokacin ma yayi  nisa da barin falon. ta sake kalli Mamy tace, "Daman Mamy ke kike goya masa baya, gashi yanzu a gaban ki yake zazzaga min rashin kunya kamar ba gaba nake dashi ba, ko da yake har ke ya yiwa bama ni kaWai ba." Mamy na zaune dai kawai bata ce komai ba amma ya bata mamaki kam sosai.

Rai a Sace Bebi ya shiga Wakin sa ya rasa abinda yake damun Maryam gabaWaya bata da girma sai na jikin ta, in badan haka ba da hankalin ka da tunanin ka ka dinga sauraren tsohon mijin da ya sake ka har ka dinga yi masa dar1ya kuna zama waje daya?. Yayi tsaki ya zauna, dole ya yiwa tufkar hanci kar abinda yake gudu yazo ya faru.

Nana Haleemad'þ>ØBÝ

*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025

©þNana Haleema.

Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

_Kina neman inda zaki siyi abinci mai daWi? Kina ™iyar yin girki gashi zaki yi ba™i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daWi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daWi akwai a lallaSa. Kina son ki siyi abincin da zaki Wauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daWi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan Sangare, tazo muku da nau in abinci kala-kala na gargajiya da na ™asar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._

_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ™asan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr

Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.

*BOOK 1*

*Page 015.*

Washe gari bai fita da wuri ba tunda yaje ya gaida su Mama da asuba, sai da ya tashi ya shiga wajan Mamy  ya gaishe ta ta amsa da™yar bai yi wata magana ba ya wuce wajan Mama ya same ta a zaune ita kaWai babu kowa ya zauna yace, "Mummy basa nan ne?." Mama ta kalle shi tace, "Basa nan, sai ka tashi kaje ka haWa tea Win da kanka tunda kai komai sai an maka, Rumana ta shiga uku da yawan saka aikin ka wallahi."

Baice komai ba shi dai, ya tashi ya haWa tea ya dawo yana cewa, "Wai Mummy baki wannan kunun ba?, ni tea ba damuna yayi ba, shan sa sai dole."

"Ai tunda nayi kace babu daWi bazan sake maka kunu ba Bebi, na hana idona bacci na dama maka amma sai kace wai kamar ba'a dama ba."

Yayi ´ar dariya yace, "Allah Mummy ranar tuntuSen hannu kika yi, ni na Wauka ma fa Mimi ce ta haWa ashe wai kece da kan ki."

Ta harare shi tace, "Yanzu ai sai ka samu mai yi maka."

"Tuba nake Mummy." Kausar ce ta shigo falon da sallama suka amsa ya kalle ta yace, "me ya dawo dake?."

"Test muka yi, kuma daman yau bani da class."

"To Wauko min sugar" ya faWa yana ajjiye tea Win.

Shiga kitchen tayi ta kawo har zata tafi yace, "baki Wauko tea spoon ba." Ta juya ta sake kawo masa sai ya kalle ta  bayan ya karSa yace, "haka zan sha babu madara?."

Kausar kamar ta zubar da hawaye ta sake kawo masa tan ajjiyewa tayi ciki gab da zata shiga Waki yace, "Kausar bani ruwa, ki buWe flaks in akwai wani abun ki kawo min." Ta juyo ta Wauko ta kawo masa tare da doya da kwai a plate ta wuce ciki a guje dan kar ya sake aiken ta.

Mama ta kalle shi tace, "kai dai saka aikin ka yayi maka yawa wallahi, indai kana waje shikenan baza su huta ba? Šauko min wannan Wauko min wancan?. Yamzu ba sai kace mata Wauko min sugar da madara, ki haWo min tea spoon da ruwa, in akwai wani abun a flaks ki kawo min, shikenan zuwa Waya taje ta dawo amma sai da ka mayar da ita sau huWu."

Baice komai ba ya shanye tea Win da yake sha Mama ta kalle shi tace, "Adnan ka cire hannun ka daga batun Maryam da Lubna don girman Allah."

Jin magiyar da Mummy tayi masa sai ya kalle ta yace, "me ya faru?."

"Jiya Maryam tazo har nan bayan ka fita tace nace maka babu ruwan ka da lamarin su, in ma tana kula Kamal Win rayuwar tace ba taka ko ta Farida ba. Sannan ko ™anin far'auna ne Mujahid saboda ba™in halin babu ruwan ka, ka cire lissafin Lubna baza ta aure shi ba a ran ka don Allah. Komai kayi ba gani ake ba, a kullum a Wan kishiya ake kallon ka."

"Ke tazo ta faWawa haka?" Ya faWa  alamun bai ji daWi ba tace, "kaga kwantar da hankalin ka, bada rashin kunya ta faWa ba cikin lallami ta faWa,  domin kasan ita ko yaushe ´an Wakin su sune ´an uwan ta, ku kuma ´an Wakin nan daban ku ke a wajan ta."
Chapter 23 · 0% Book details