← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 48

Sashe 2

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama tace, "to haka zaki zauna kina tauye kan ki saboda ni Manal?, kin ™i cigaba da karatun boko tunda idanuna suka rufe, islamiyyar ma gashi kin ajjiye. Ita waccan da bata da amfani a gidan sai ita take zuwa kuma ta raina mai biya mata ™udin makarantar, ko yaushe a banza take kallon sa saboda bashi da kuWi kuma ba shine ya haife ta ba."

Manal tace, "Wallahi Mama babu inda zan iya zuwa na barki, ko naje bazan yi karatun ba tunanin ki zan dinga yi. Kuma ni culinary school nake so, na zama fitacciya a fannin girki." Mama tace, "to ai ko ita Win kin ™i Manal."

Tayi murmushi tace, "Zan yi Mama amma ba yanzu ba, zan tafi Mama akwai sabon girkin da na gano mana nake so naje mu gwada da Surayya."

Mama tayi dariya tace, "shiyasa kika iya saboda in dai kin gani zaki ce zaki gwada. Jeki babu abinda nake so Manal sai kin dawo, Allah yayi miki albarka ya baki abokin zama na gari, ya haWa ki da masu taimaka miki kamar yadda kike taimakona."

Murmushi tayi tace, "Amin Mamana, sai na dawo" ta faWa tana tashi ta fita zuciyar ta gabaWaya babu daWi akan lamarin Yaya Mubeena.

Da sallama Mubeena ta shiga falon gidan babba mai kyau kai da kaga falon kasan mazaunan falon ma ™ananun masu kuWi bane ba saboda yadda ta tsaru sosai, babar macen da take zaune sanye da glasses a idanun ta tana duba waya ta Wago ta kalle ta tayi murmushi tace, "Mubeena kece." Murmushi tayi ta ™arasa ta zauna kusa da ita tana murmushi tace, "Mummy ina wuni?."

Wacce ta kira da Mummy tace, "how was your day?, Ya Maman ki?."

"She's fine Mummy. Tace tana gaishe ki."

"Ina amsawa" ta faWa tana kallon mai aikin ta tace, "ina so ki dafa min couscous amma baki iya ba." Tayi shiru bata amsa ba Mubeena tace, "mummy ki kawo na dafa miki." Mummy tayi murmushi tace, "noo! Bilkisu tana ciki jeki" da sauri Mubeena ta tashi ta shiga cikin Wakin ta samu Bily a zaune tana waya ta bita da kallo kafin ta tsaya jikin mudubi tana kallon kanta cikin burgewa. Ita kanta tasan tana da kyau ko ba'a faWa ba, tana da kyaun da lokaci Waya zai Wauki hankalin ka in ka kalle ta sai ka sake.

Sake kallon kanta take yi kafin tace, "Allah bai yi za'a haife ni a irin wannan gidan ba, da a wannan gidan nake ai sai nafi haka kyaun gani, da wannan gidan na dace ba waccan ba."

Bily ta katse kiran tace, "ke kullum kika zo gidan nan sai kin maimaita maganar nan, dallah ki shiga kiyi wanka mu wuce bana son Sata lokaci." Bata ce komai ba ta shiga banWakim tayi wanka ta fito ta zauna tana shafa mai Bily ta kalle ta tace, "Gaskiya Mubeena dole ki dinga ba™in cikin haihuwar ki da aka yi a gidan ku, ke kin ganki kuwa?, kina da kyau sosai, kawai farin Manal da yake mai haske ne yafi burge ni, dan kin ga ita babu masu wannan hasken da yawa a cikin nigeria. Ke kuwa haske dai wanda kowa ya sani ki ke dashi, amma kina da kyau."

Mubeena tace, "bari kawai, bayan talauci ma ga uwa makauniya, ga mai ri™on namu ma talaka, ga ™anwa soloSiyo babu abinda ta iya kullum cikin kiyi ha™uri da duniya take faWa min. Shiyasa ko a school ban taSa bari na nuna ta matsayin ™anwa balle kuma na nuna babar ta mu balle kuma gidan namu gabWaya." Dariya Bily tayi tace, "Shege talauci. Amma bai kamata ki cewa Mama haka ba, kuma a ko ina zaki iya nuna Mama saboda ta fi ki kyau. Kawai dai da ace ke ´ar Alhaji ce da an gama magana." Itama dariyar tayi tace, "Ina jin daWin haWuwar mu dake, ke kan ki farkon haWuwar mu kin Wauka irin wata shegiyar nan ce ni baki san ganye na baro su suna ci ba."

A tare suka sake yin dariya Bily tace, "Wallahi baki da kirki, ke baki bar kowa ba har Mama." Mubeena ta tashi ta buWe kayan Bily ta Wauki kayan da take so ta saka ta tsaya tana kallon kanta a mudubi dan ita kanta tasan tayi kyau ba kaWan ba. Bily ta bita da kallo tace, "Gab nake da daina baki kayana domin in kika saka sai naga sun fi miki kyau a kaina."

Dariya Mubeena tayi ta shirya tsaf tayi kyau sosai suka dau™i jaka suka fita ko mummy basu yiwa sallama ba dan su ´an boko ne babu ruwan su basa tauyewa Bily ha™™in ta, Bily taja mota suka fita daga gidan.

***** A yadda ya shigo falon zai tabbatar maka da ransa a Sace yake, cikin fuskar sa da bata da alamun walwala a ko yaushe dan kana kallon sa  zaka fassara shi a mutum mara fara'a, kuma baza'a rasa faWa a wajan sa ba.

Kyakykyawa ne mai duhun fata da madaidaicin jikin, yana da ido da dogon hanci siriri, fuskar sa Wauke da zagayayyen gashin da ya kewaya ko ina. Cikin glasess Win da yake idanun sa ya kalle ta tana zaune kafin yayi magana cikin fusata tace, "wai kai waye gaba tsakani na dakai ne? Yayar ka ma Farida gaba nake da ita balle kai da zaka dinga min shishshigi a cikin lamarin rayuwata, ina ruwan ka da abinda na zaSarwa kaina?, har nawa aka ke da zaka dinga nuna min daidai da ba daidai ba?."

Wanda take yiwa maganar yana tsaye yana jin ta ya kalle ta yace, "ba yaya ta ba, ko kece kika haife ni baki isa kina yi abu ba daidai ba na zuba miki idanu ina kallon ki. Yasan yana son ki meyasa ya rabu da ke? Ya san zai dinga bibiyar ki har ki dinga shiga motar sa meyasa ya miki sakin da bazai iya mayar dake na?."

"Ina ruwan ka dani?, haka na zaSa baka isa ka hana ni ba wallahi."

"Ai kuwa zaki ja masa, na rantse da Allah na sake ganin sa ™ofar gidan nan sai na saka n kulle shi ya kwana biyu a cell, in kina musu ki sake gayyato shi kiga nida ke waye zaiyi nasara."

Anty Maryam ta harzu™a matu™a kamar zata kifa masa mari tace, "baka isa ba walalhi, ™arya ka ke Bebi baka isa ka hana ni abinda nayi niya a cikin gidan nan ba. gidan ubana ne kamar yadda yake gida uban ka, ina da iko kana da iko, baka iya ka hana ni abinda nake so ba. In kana hana ™anen ka ni Yayar kace." Ganin Mamy tazo wajan sai baice komai ba ya juya ya fita ransa a Sace sosai.

Yana fita ta kalli Mamy tace, "yaron nan yana neman raina min hankali, Mamy kiyi mana tsakani dashi, ni yayar sace babu ruwan sa da abinda zanyi."

Mamy ta kalle ta tace, "Gaskiya yake faWa miki ai, kishin ki yake matsayin ki na yayar sa shiyasa yake tsaye akan lamarin ki. Ke kuma banza shashasha mara kamun kai miji ya sake ki amma ya dinga bibiyar ki kina masa dariya saboda baki san abinda yake miki ciwo ba. Ya san yana son ki ya miki saki har uku?."

"Mamy su Nabila da Nabil na duba fa."

"Zaki min shiru ko sai na tsinke ki da mari?, babu mota a gidan nan da baza ki hau kije wajan yaran naki ba? Ki aika a Wauko miki su ko lallai sai kinje inda suke?."

Anty maryam ta sauke numfashi tace, "kenan yanzu Mamy shine mai gaskiya ni mara gaskiya?." Mamy ta Harare ta tace, "ki cigaba da abinda kike yi nan gaba zaki dana sani, sai a lokacin zaki fahimci Bebi gaskiya yake faWa miki. Bebi gata yake miki wanda uban ki bai miki shi ba." Tana gama faWa mata haka ta shige ta barta a wajan.

Kai tsaye Bebi Sangaren mahaifiyar sa Mama ya shiga wacce shi kaWai yake kiran ta da Mummy kowa Mama yake cewa, amma shi tun yana yaro yake cewa Mummy har girman sa. Yana shiga  ya same ta a zaune ita ™anwar sa Mimi ya ce, "yanzu Mummy abinda yarinyar nan Maryam take yi daidai ne? Miji ya rabu da ita ya sake ta amma ya dinga bibiyar ta har yana Waukafr ta a mota? Akan wanne dalili?."

Mama tace, "to Bebi ni me zance? Ina ruwana tasan daidai ai sannan tasan ba daidai ba." Ya kulle idanun sa bala'i kishi yake ji yana addabar zuciyar sa ya kalli Mama yace, "shikenan sai a zuba mata ido kenan?."

"To maganar taka me ta canja? Su mazan yayyen ta akwai wanda ya damu da yayi maganar ne?, kai kaWai ka ke tayar da jijiyar wuya akan lamarin Maryam da Lubna."

Bebi ya girgiza kai kawai yace, "bazan bari ba kin san da hakan Mummy." Mama tayi dariya tace, "shikenan Bebi, zaka dinga asarar maganar ka kuwa dan ba ji zatayi ba ita da kanwar ta." Kallon Mimi yayi kamar zai yi magana sai ya fasa ya fita ya shiga mota kai tsaye ya bar gidan.

Nana Haleema.

*BAYA DA ˜URA*

FitattuBiyar2025

    ©þ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp

*BOOK 1*

*Page 002.*

Getting better specialist hospital ya nufa, babban private hospital da ya samu lambar yabo a fannin abubuwa da yawa, asibitin shine private hospital na farko da aka fara dashen zuciya a cikin sa arewancin nigeria, asibitin ya haWa manyan likitoci masu ™warewa a kan aikin su. Asibitin gabaWaya sa an gina shi ne zuciya, da abinda ya shafi cututtukan jini, da abinda ya shafi Sangaren mata, sauran abinda bai shafi wannan ba ana yi ne kawai amma ba dan saboda haka aka gina shi ba sa. Asibitin mutane huWu ne suka cure waje guda suka samar dashi, kuma suna matu™ar kula dashi sosai, shiyasa ya zama asibiti mafi ™olowar masu zuwa da kuma tsada, a duk shekara suna yin aikin kyauta ga masu bu™ata ta musamman, wannan dalilin ya saka sunan asibitin Getting Better ya zaga ko ina.
Chapter 2 · 0% Book details