← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 48

Sashe 44

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mama har hoton su tare na gani, shiyasa ma na amince da hakan a zuciya ta." Mama tace, "wani lokacin ai baki da wayo Manal, meye abin amincewa da wannan maganar?. Ke kin san inda halin sane baban ku bazai barki har yanzu tare dashi ba?, yayi bincike a kan sa sosai an tabbatar masa da nagartar sa da kuma girmama mace da yake yi a duniya, a cikin labarin da aka bawa mahaifin ki babu zancen yaudara, ance ya taSa yin wata budurwa amma tayi aure bayan ita babu wata da aka san su tare. Wajan aikin sa da ko ina an tambaya an tabbatar ba'a ganin sa da mace in dai ba mara lafiya ba. Ke kina ganin da yana da wannan halin zai Suya ne? In wani bai sani ba wani tabbas zai sani."

Manal ta girgiza kai tace, "Haka ne Mama."

"Kar wani ya sake kawo miki irin wannan tunanin ki amince Manal, akwai mutanen da suke faWar gaskiya akwai saboda kar ka faWa halaka, akwai wanda suke faWar ™arya dan su cutar dake ko su cutar dashi. Barin wannan yayi tasiri a zuciyar ki ba abu bane mai amfani, kamar ma baki yarda da Adnan Win ba duk tarin girmama ki Win da yake yi tun kafin yace zai aure ki." Manal ta sauke numfashi tace, "Haka ma Surayya tace ban yarda, amma yanzu na amince da batun ki Mama bazan sake ba."

"Yafi miki dai. Ashe da kin fasa auren nasa ban sani ba ko?." Manal tace, "ina tunani dai." Mama tace, "baki da wayo ne Manal, bazan amince a aurar dake babu bincike ba domin naga illar hakan, ko ni da kaina zan fita na bincika Adnan balle da baban ku a raye. Abinda baki sani ba akan Adnan yanzu ya sani shiyasa ya amince dashi Wari bisa Wari dan ya tabbatar zai kula dake kula mai kyau. Shiyasa kika ga na amince nima, bai wa dan yana da kuSi ba sai dan kawai ya cancanci a zaSe shi. Ni kuWi ba ba™ona bane Manal, babu wani mai kuWi da zai zo ban amince dashi na bashi ke."

Sai a sannan tayi murmushi tace, "haka ne Mama." Mama tace, "ko kefa, da kina ta yin tunanin banza da wofi. Ina Mubeena?."

"Tana kwance." Mama bata sake magana ba tayi shiru Manal ta tashi tace, "Mama bara na siyo mana kayan cefane, yau dambu zan mana."

Mama tayi murmushi tace, "sai kin dawo" ta faWa tan fita. Tana fita gidan ta Wauki waya ta kira Dr Huzaifa akayi sa'a ya Wauka ta saka a kunne tace, "Dr ina kwana?."

"Lafiya lau Manal, ya jikin Mama?."

"Taji sau™i sosai."

"To haka ake so, Allah ya ™ara Lafiya."

"Amin. Daman tambayar ka nake so nayi don Allah in babu damuwa."

Yayi dariya yace, "Ina jin ki amaryar Adnan." Sai tayi murmushi tace, "Don Allah a cikin abokan ku akwai Mujahid?." Da sauri yace, "a ina kika san shi?."

"Dama jiya ne yazo ya same ni yana min magana akan wai in na amince da auren Dr yaudara ta zaiyi ba aure na zaiyi ba, ya saba yiwa mata haka ba nice ta farko ba Magana dai kala-kala, hankalina ya kasa kwanciya shiyasa na kira ka."

Huzaifa yace, "Innalillahi! Wai kina nufin har gidan ku yazo?." Manal ta amsa Huzaifa yace, "kar ki damu da abinda yace, yana yi ne dan ya raba Adnan da abinda yake so, duk wani farin cikin Bebi baya so, so yake yaga ya jefa zuciyar sa cikin ™unci baya ™aunar yaga Bebi yana murmushi a duniya. Wallahi ba ina faWa miki dan na kare Bebi bane, ina faWa miki gaskiya ne domin ke kanwata ce bazan miki ™arya akan abinda yake gaskiya ba, in na cutar da rayuwar ki kaina na cuta. Mujahid da abokin mu ne kafin mu rabu dashi saboda wata Wabi'a tasa ta banza, Bebi shine yayi silar da aka kwace lasisin sa na zama likita, shikenan ya tsani Bebi yake so ya raba shi duk wani abun da yaga yana so. Bebi yana sonki Manal, babu macen da yake so in ba ke ba na tabbatar da hakan, Mujahid yaga haka ne shine yazo dan ya raba ku Allah bai bashi nasara ba."

Manal ta girgiza kai cikin gamsuwa da abinda yace tace, "na gode sosai, na kuma fahimta."

"Yauwa ko kefa, ko da zai sake dawowa kar ma ki saurare shi."

"In sha Allah, Amma don Allah kar ka faWa masa, kar kayi masa zancen gabaWaya don Allah." Huzaifa yace, "kar ki damu, bazan faWa masa ba."

"To na gode." Daga nan suka yi sallama ta kashe sai a sannan hankalin ta ya kwanta dan tana son Bebi itama.

Nana Haleemad'þýÿ

*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025

                 ©þNana Haleema.

Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

*BOOK 1*

*Page 028*

Bebi kuwa yana kwance a gida baya son fita a ranar kwata-kwata, ya jawo wayar sa ya kira Huzaifa bayan ya Wauka yace, "Yau bazan shigo ba, in akwai wani abun ku yi kar ku jira ni." Huzaifa yace, "Lafiya?."

"Baba jin daWi ne."

"Sannu, Allah ya ™ara Lafiya." Ya amsa da amin kafin yace, "Mama ta amince da maganar aurena da Manal, amma tace da sharaWin in na auri Manal da shekara Waya zan auri Rumana."

Huzaifa yace, "kuma dai!." Bebi bai iya magana ba jin haka Huzaifa yace, "to Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, kar ka sake mata musu a wannan lokacin kawai ka amince  tunda tana so."

"Na amince ma ai Huzaifa, na amince har zuciyata ta saboda ita."

"Hakan yayi, Allah ya kai mu lokacin" ya amsa da amin ya yanke wayar ya koma ya jingina da kujera.

Manal ya kira bata Wauka ba ya sake kira a lokacin ta Wauka tayi sallama yayi shiru na wani lokacin idanun sa a kulle kafin ya amsa tace, "an tashi lafiya?."

"Lafiya lau, ya jikin Mama? Ina fatan ta samu Lafiya?."

"Da sau™i sosai, yau ma tace min tana ganin hasken rana."

"Ma sha Allah, a hankali komai zai dawo in sha Allah. Ki gaishe ta."

Manal tace, "zata ji in sha Allah." Yayi shiru baice komai ba itama bata ce ba na wani lokaci, sai da ya sauke ajiyar zuciya ya katse shirun yace, "kin cemin kina da Yaya, ban taSa ji kin min maganar ta ba ban kuma taSa ganin ta ba. Bakya so na santa?."

Tayi murmushi tace, "Yaya Mubeena wai? Tana school, cikin kwanakin nan ne ta dawo gida kuma bata jin daWi shiyasa baka ganin ta."

"Ohhh" Abinda ya furta kenan kafin yace, "ita tana zuwa makaranta amma ke bakya zuwa, meyasa bakya so?."

"Ina so sosai, kawai dalili ne ya hana ni zuwa."

"Meye shi?."

"Mama, bazan iya tafiya school na dinga barin Mama  ita kaWai ba gaskiya. Shiyasa na ajjiye duk wani burina a gefe, tana da lalurar ido in muka tafi duka waye zai kula da ita?."

Lumshe ido yayi yana jin wani irin bugun zuciya a lokaci Waya, Allah ya sani yadda take son mahaifiyar ta yana daga cikin abinda yake jan hankalin sa zuwa gare ta, soyayyar ta yake ji sosai a zuciyar sa fiye da yadda yake tunani, bai taSa tunanin zai so wata mace kamar haka ba, shi ko a yaushe burin sa kar soyayya tayi masa mugun kamu, sai gashi a lokacin da bai yi tunani ba ya faWa tarkon ™aunar ta, ™auna mai tsanani ma kuwa. Har bugun zuciyar sa yake ji a kunnen sa saboda soyayya,  bai san lokacin da yace, "ina sonki Manal" ya faWa cikin shau™in so da kuma ™auna.

Murmushi yaji tayi jin abinda yace, yadda yake furta kalmar ma abin jin daWi ne balle yadda kalmar take ratsa ta sosai, tace, "Nima haka Dr."

"Kema me?."

Tayi murmushi ta kulle fuska kamar tana ganin sa bata ce komai ba yacw, "ina jin ki, kema me?." Tayi dariya tace, "nima i love you." ˜aramin tsaki yayi yace, "Da hausa zaki faWa min." Manal cikin shagwaSa tace, "kunya nake ji."

Ya gyara zama sosai shagwaSar ta na ratsa shi sosai yace, "shiyasa nace ki faWa." Manal tace, "to ba na faWa ba?."

"Ban amince da wanda kika ce ba, da hausa nake so ki faWa."

"Ina son ka." ³ar dariya yayi cikin farin ciki  ya wara idanu yace, "wow! Finally yau dai kin ce."

Tayi murmushi shima shi yake yi yace, "sake faWa naji pls." ˜i tayi sai ta canja maganar tace, "meyasa ake ce maka Bebi?."

"Sunan gida ne" Ya faWa a ta™aice kafin yace, "bakya zuwa makaranta saboda Mama, amma yanzu zaki aure ki bar Mama."

Tayi shiru na wani lokacin muryar ta ta raunana kafin tace, "tuna hakan yana saka ni ciki damuwa" ta faWa murnar ta na rawa sosai alamun kuka zata yi. Da sauri yace "wasa nake miki, meye na kuka Manal?."

"Da gaske ne ko baka ce ba itama tana faWa min, don Allah babu ta yadda za'ayi na zauna a wajan Mama? Wallahi bazan iya zama a  ko ina in bata nan ba, ko Ina zanje bazan ji daWi sa kamar wajan ta ba."

Kuka take sosai nan take yayi dana sanin faWa mata haka yace, "Manal relax please, ki daina kuka ki tsaya kiji abinda zance miki." Bata yi magana ba hakan ya saka yace, "Manal kina tare da Mama a ko yaushe in sha Allah kar ki damu, aure ai ba mutuwa bace." Manal bata ce komai ba jin tayi shiru yace, "ki nutsu ni da wasa nake faWa miki ba da wani abun ba, naga alama kina son kuka baya miki wahala ke kam."

Manal tace, "duk yadda zan faWa baza ka gane ba, Mama na kira na" Tana faWa ta yanke wayar shi kuma yabi wayar da kallo yana jin wani iri a zuciyar sa da ya saka ta kuka. Ba jimawa ya kuma kira amma bata Wauka ba, ya sake kira ba'a Wauka ba, babu daWi zuciyar sa haka ya ™yale ta ya cigaba da harkokin sa.
Chapter 44 · 0% Book details