← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 48

Sashe 34

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma da sai ki saka Gmail Win ki a wata wayar ki Wauki number ta ki kira ki sanar dani, na damu sosai baby." Ta share idanun ta tace, "ban yi wannan tunanin ba." Yayi murmushi yace, "to shikenan, indai waya ce za'a sake siya miki wata dan ma dare yayi ne da yanzu za'a kawo miki amma gobe da safe ki shirya karSar waya. Sim card Win fa?." Mubeena tace, "zan canja wani kawai, daman bana son wancan damuna ake da waya." Yayi murmushi yace, "an gama ranki ya daWe, zan aiko ayi miki register har gida ba sai kinje kin bi layi ba."

Tayi murmushi tana turo baki ya bita da kallo kurilla yace, "Ina kewar ko baby." Ta kalle shi itama tace, "Nima haka" ta faWa tana kallon sa tana tuna abinda yayi mata sai tsigar jikin ta ta tashi. Hannun ta ya ri™e yace, "yaushe zaki raka ni Abuja? Ina so naje na gana da president kinga sai muje ko?." Mubeena Jin ance president sai ta kalle shi tace, "Mummy baza ta barni ba, faWa zata yi min." Yayi murmushi yace, "to yanzu ya za'ayi? Ina so kiyi min rakiya muje mu dawo a ranar."

Mubeena tayi shiru tace, "a ranar muje Abuja mu dawo?." Yayi dariya yace, "sosai, jirgi zamu hau kuma private get ne sai lokacin da naso muje mu dawo." Jin haka sai ta sake jin daWi tayi dariya tace, "to zan duba na gani in zanje."

"Zaki je ma kawai Baby." Tayi murmushi shima yayi tare da yiwa hannun ta kiss yace, "hankalina ya tashi akan rashin magana dake, yanzu dana ganki sai na samu nutsuwa."

Tayi dariya bata ce komai ba yace, "in badan ke ba bana driving da kaina, amma bazan iya zuwa da wani wajan ki ba Baby" ya faWa yana Wauko leda a bayan motar ya ajjiye akan cinyar ta.

BuWe ledar tayi taga kayan ciye-ciye ne kawai a ciki, tayi murmushi tana kallon ledar sai ji tayi ya mata kiss a kumatu ta kalle shi ya Waga mata gira sai suka yi dariya a tare.  A haka suka rabu ta koma ciki shi kuma ya ja motar domin baya so Maubeena ta guje masa bai samu abinda yake so ba, in hakan ta faru yayi babbar asara.

Mubeena bata dawo ba sai goma na dare Baba yana zaune a ™ofar gida yana jiran yaga ta inda zata Sullo dan lamarin ta ya lura sai ana mata yi jan ido,  ai kuwa ya hango ta shigo layin, baiyi magana ba har ta shiga cikin gidan sannan yabi bayan ta ya kulle gidan dan a wajan Mama yake ya shiga ciki.

"Daga gidan uban wa kike?." Jin abinda Baba yace sai da gaban ta ya faWi ta juyo tana kame-kame,  ya Wauke ta da mari mai zafi kafin ta dawo hankalin ta ya sake marin ta sai ta zube a wajan tana gani biyu-biyu dan rabon da a mare ta har ta manta yace, "ni zaki mayar Wan iska? Dan kinga ina bin ki a hankali sai ki mayar sa'an wasan ki? Daga ina kike a cikin daren nan?." Baya yayi ya Wauki  igiyar shanya yace, "Wallahi ko ki faWa min ko yau na zane miki jikin ki, daga gidan uwan ban wa ki ke a daren nan?."

Mubeena ta tsorata sosai karo na farko da Baba yayi mata haka,jiki na rawa ta rasa abinda zata ce kawai taji ya fara dukan ta dan ta gama Sata masa rai.

A guje Manal ta fito jin maganar Baba da ™arfi ganin ana dukan ta sai jikin ta yayi sanyi ta fara kuka tana daga tsaye Baba yace, "baza ki faWa min ina kike zuwa ba?."

"Makaranta naje, sune suka tura mu wani aiki sai yanzu na dawo."

"˜arya kike, har makarantar taku na saka an duba bakya nan, ko faWa min inda kikaje ko yau sai na lahira ya fiki jin daWi, ko ki faWa min uban da yake goya miki baya yake zuga ki ko yau na karya ki." Ganin Baba dukan nata zai sake yi da sauri tace, "Wallahi Ina can, ina can babu inda naje" ta faWa tan kuka sosai dan ta daku.

Baba yace, "duk abinda kike ganin daidai ne a wajan ki Mubeena ki yi, ki cigaba da Wurawa babar ki ba™in ciki, ki cigaba da bari tana zubar da hawaye a kan ki. Daga lokacin da kika yi sake tayi miki baki daga wannan lokacin zaki gane kuskauren da kika tafka a rayuwar ki wanda baza ki gyara ba. Ina so ki sani, daga yau babu ke babu zuwa makarantar na soke, sannan daga yau kar na sake gani kin fita ko da gidan su Surayya ne. wallahil azim kika sa ke aikata wani abun sai nayi miki illa, sai na karya ki gida biyu" ya faWa yana cillar da igiyar ya shiga Wakin sa cikin Sacin rai sosai.

Manal da take kallon ta tana kuka tace, "Ko yaushe burin ki ran Mama ya Saci, bakya damuwa da wanne hali zata shiga saboda son zuciya da son kuWi ya riga ya rufe miki ido. Ki yi abinda kike ganin ya dace, abinda baki sani ba nasan ba makaranta kike zuwa ba Yaya akwai inda kike zuwa in kika fita, bana zargin ki a baya, amma yanzu ina zargin kin fara wata Wabi'ar da baki da ita. Kije ki yi ke zaki dana sani, ke zaki nadama a lokacin da bata da amfani, ke abin zai bibiya har mutuwar ki" tana faWa ta shige ciki ta barta a wajan tan kuka sosai. Mama duk tana jin abinda yake faruwa tayi kamar tayi bacci nan kuwa idon ta biyu babu wanda ya kai ta jin ba™in ciki a zuciyar ta.

Tana jin wucewar Mubeena Win tana kuka bata ma Waga kai ta kalle ta ba balle tayi mata magana. A haka suka kwana kowa rai a Sace. Da ciwon ™irji Mama ta tashi sai da Manal ta bata magani sannan ta Wan ji daWi. Mubeena na Waki ta™i fitowa ko cin abinci balle wanka babu wanda ya neme ta duk suka share ta.

Gab da sallar azahar Bily tazo gidan Baba yana nan dan bai fita ba saboda case Win Mubeena, Bily ta gaishe da Mama suka gaisa da Manal kafin tace, "Manal Baba yana nan?." Manal tace, "eh yana nan, amma yana wancan gidan." Bily tace, "muje ki raka ni wajan sa na zo" Ta amsa da to ta tashi ta saka mayafi suka fita.

A lokacin zai fito daga gidan suka  haWu a soron gidan, Bily ta gaishe shi ya amsa kafin Manal tace, "™awar Yaya ce Baba, tace tana son ganin ka." Baba yace, "Allah yasa Lafiya."

"Ba Lafiya ba Baba, magana ce akan Mubeena."

Baba ya nutsu yana kallon ta yace, "Ina jin ki."

"Baba tun shekarar mu ta farko aka kori Mubeena daga makaranta saboda bata maida hankali akn karatun, duk wata ™arya da take yi akan makaranta ™arya take wallahi bata da register babu sunan ta a jerin ´an makaranta, tana dai taya ni zama mu dawo. To yanzu ta daina zuwan ma saboda akwai wani Alhaji da yake wure mata kunne da sunan zai aure ta, baban mai kuWi ne sosai a garin nan, har waya ya siya mata mai tsadar gaske. Nayi shiru da ban faWa ba, amma yanzu rawar kan nata yafi na baya, shiyasa naga in nayi shiru naci amanar ku dalilin da ya saka nazo na faWa a saka mata ido domin a kansa babu abinda baza tayi ba."

Baba ya girgiza kai cikin mamakin Mubeena yace, "Ya sunan ki?."

"Bilkisu."

Baba yace, "Na gode Bilkisu, Allah yayi miki albarka, Allah ya saka miki albarka a rayuwar ki."

Bily tace, "Amin Baba. Nayi anyi da ita akan ta bari ta™i shiyasa na yanke hukunci nazo na same ka, kuma daman gidan mu shine mafakar ta, a nan take wuni har dare sannan ta tawo." Baba yace, "kin kyauta da kika faWa Sin, na gode sosai Allah yayi miki albarka" ta amsa da amin tayi musu sallama ta wuce. Manal ta koma ciki jikin ta duk babu daWi jin abinda akace Mubeena Win nayi.

Manal da ta shiga gida kai tsaye inda Mubeena take ta wuce ta shiga ta zauna kusa da ita tace, "ni kaWai ce ´ar uwar kuma wacce zan faWa miki gaskiya Yaya, ni kaWai kike da ita ko kina so ko bakya so. Rayuwar da kika Wauka ba komai bace face watsewa da kuma lalacewa, in kina ganin hakan da kike yi shine daidai kuma shine wayewa wallahi rashin hankali ne da kuma rashin wayo da lalacewa. Zai jawo miki dana sanin da har ki mutu baza ki daina ba a lokacin da bazai miki amfanin komai ba, ita wannan duniyar kayi daidai ma ya ka cika balle baki yi daidai ba?. Kabi iyayen ka ya ka zauna balle ka raina iyayen ka?."

"A ko yaushe burin ki Satawa Mama rai, bakya ganin girman ta bakya darajata dan ta kasance a wannan gidan da kika raina kuma bata gani, ke a ganin ki Allah bai miki daidai ba da ya yo ki a gidan nan. Ba ™arya kowa yasan kina da kyau amma meye amfanin kyau babu kyaun zuciya? Meye amfanin kyaun da zai kai ki wuta da ™afar ki?. Ke a tunani ki wannan Sacin rai da kike saka Mama bazai iya kai wuta ba? Ko hawayen da kike saka ta a kulluS ruwa ne yake zubewa daga idanun ta Yaya?."

Mubeena tayi shiru bata ce komai ba Manal tace, "duk abinda kike aikatawa in ya kamata kin sani wallahi, kome kike yi ki na sane domin kuwa da hankalin da kuma ilimin ki, ki sauke tunanin da ya shiga kan ki, ki yi rayuwa mai kyau in ba haka ba dana sani zata riske ki a lokacin da hakan bazai miki amfani ba. Na faWa miki haka ne a matsayin ki na ´ar uwata ta jini, bani da kamar ki shiyasa na faWa miki gaskiya, in kin ga zaki gyara kanki, in baza ki gyara ba kan ki" tana gama faWa mata haka ta tashi ta fita dan in tana zaune kusa da ita ji take kamar ta mare ta.
Chapter 34 · 0% Book details